Garin Sari da ke arewacin ƙasar Iran, shi ne cibiyar lardin Mazandaran kuma yana da daɗewar shekaru 5000. Hadafinmu a wannan rubutu shi ne yi muku bayani game da yanayin iska, yanayin al’adu, karatu, da sauransu na wannan gari na Sari. A cigaban rubutun za mu tattauna batutuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum ga masu karatu a wannan gari.
Sari
Ana kallon garin Sari a matsayin ɗaya daga cikin daɗaɗɗun garuruwan ƙasar Iran. Garin yana tsakiyar yankin duwatsun Alborz kuma yana ɗaya daga cikin garuruwan ƙasar masu yawan mutane. Ta gabas, garin Sari na maƙotaka da garin Surak, ta arewa maso gabas garin Neka, ta arewa da tekun Mazandaran da garin Juybar, ta yamma garin Qa’emshahr da garin Savadkoh, ta kudu kuma garin Sari na maƙotaka da Saman. An kasa garin gida uku, sannan a cikin garin akwai muhimman cibiyoyin gwamnati da na shari’a na lardin Mazandaran.
Garin Sari na cikin yankin duwatsun Alborz sannan yana da sassa shida. A lokacin zafi iskar garin na da danshi sannan sannan babu zafi sosai, a lokacin sanyi kuma iskar busassa ce kuma bai kai sauran garuruwan arewacin ƙasar sanyi ba. Bayanan ƙididdiga a kan yanayi sun nuna cewa yawan ruwan sama da ake samu a yankin ya ragu saboda fari.
Hasumiyar agogo ita ce babban tambarin wannan gari. Ana kiran harshen mutanen garin da Sarawiy. Kamar yadda bayanan ƙirge na shekarar 2016 suka nuna, akwai mutum 509820 zaune a garin Sari kuma ƙalilan ne baƙi a cikinsu. Akasarin al’ummar garin Sari mazauna garin ne ƴan ƙabilar Tabari, sannan mafi yawan mutanen garin musulmi ne ƴan Shi’a Imamiyya.
Karatu a Sari
Akwai jimillar cibiyoyin ilimi da jami’o’i 77 a lardin Mazandaran. Cibiyoyin sun keɓantu da wallafa mujallun ilimi na musamman guda 59 da maƙalolin ilimi guda 99787. A cikin maƙalolin akwai maƙalolin mujalla guda 13682 da maƙalolin taro 57399 da suka wallafa a tarukan cikin gida, haka kuma sun wallafa wasu maƙaloli a matakin ƙasa da ƙasa. Daga cikin fitattun jami’o’in lardin akwai Mazandaran University of Medical Sciences. Za ku iya samun ƙarin bayani a rubutunmu mai suna Karatu a Mazandaran University of Medical Sciences.
Zirga-Zirga
Akwai filin jirgin ƙasa da ƙasa na Dasht Naz a garin Sari wanda yana cikin filayen jiragen ƙasar Iran da ake yawan kai-komo a cikinsu. Matafiya za su iya amfani da hanyoyin mota, hanyoyin jirgin sama, hanyoyin jirgin ƙasa, da hanyoyin ruwa domin zirga-zirga tsakanin Sari da sauran garuruwa. (garin Sari shi ne garin Iran na farko wanda layin jirgin dogo na ƙasa da ƙasa ya ratsa ta cikinsa). A garin babu tsarin motocin zirga-zirga na gama-gari (autobus) saboda ƙaramin gari ne kuma yana cike da abubuwan kallo. An fi amfani da motocin taksi na haya wajen zirga-zirga a garin Sari.
Nishaɗi da wuraren yawon buɗe ido
Garin Sari na ɗauke da abubuwan buɗe ido masu yawa, wannan ya sanya ya zama gari na biyar a yawon buɗe ido a ƙasar Iran kuma ɗaya daga cikin wuraren yawo masu muhimmanci a Iran. Saboda kasancewarsa a bakin teku, ana samun nau’o’in dabbobi kala daban-daban a cikinsa. Wani abun jan hankali game da wannan gari shi ne; irin yanayin rayuwa na musamman da yake da.
_ Gidan Fazeli
_ Tafkin Miyansheh
_ Avin waterfall
_ Taflin Alandan
_ idanuwan ruwa na Badab Soort
_ Yankin Dasht Naz
_ Tafkin Chort
_ Madatsar ruwa ta Shahid Rajaei
_ Park ɗin jeji na Shahid Zare
_ Tafkin Hamid Abad
_ Dasht Naz
_ Khezr Abad
_ Melal Park
_ Gidan Ramadani
_ Gidan wanka na Waziri
_ Babban masallacin Shah Abbas
_ Bula waterfall
_ Kogin Tajan
_ Imamzadeh Abbas
_ Babban masallaci
_ Hasumiyar Raskat Dogane
_ Gidan Kolbadi
_ Gidan Fazeli
_ Gidan Sardar Jalil
_ Lambun Nilofer Abi
_ Da sauransu…
Cibiyoyin Magani
_ Asibitin Hekmat
_ Asibitin Velayat
_ Asibitin Bu-Ali Sina
_ Asibitin Imam Khomeini
_ Asibitin Fatema Zahra (AS)
_ Da sauransu…
Hotel da Masaukai
_ Slar Dareh Hotel
_ Badeleh Hotel
_ Asram Hotel
_ Narenj Hotel
_ Navid Hotel
_ Aseman Shahr Hotel
_ Masaukin baƙi na Asheri Galesh
_ Masaukin baƙi na Cheshem Soort
_ Masaukin baƙi na Mah Joon
_ Gidan baƙi na Ghorbani
_ Da sauransu…
Ɗakunan Karatu
_ Laburaren Arshad
_ Laburaren Gari na Alulbait (AS)
_ Laburaren Azadegan
_ Laburaren Ibn Shahr Ashoub Saravi
_ Laburaren Shahid Mojtaba Alamdar
_ Laburaren ƙasa na lardin Mazandaran
_ Babban laburaren Danesh Amouzi
_ Ɗakin karatu na Rojman
_ Da sauransu…