Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Jami'ar Tabriz (University of Tabriz)

Karatu a Jami’ar Tabriz (University of Tabriz)

Loading

Garin Tabriz (gari na uku mafi girma a Iran) yana yankin arewa maso yammacin ƙasar Iran kuma a tsakiyar lardin Azerbaijan. A wannan gari akwai jami’ar da ake kira Jami’ar Tabriz (University of Tabriz) wadda ɗaya ce daga cikin ingattattun jami’o’in ƙasar Iran. A wannan maƙala zamu tsunduma cikin bayani game da karatu a wannan jami’a ta University of Tabriz:

Gabatarwa

University of Tabriz (Jami’ar Tabriz) ɗaya ce daga cikin jami’o’in gwamnati wadda girmanta ya kai kimanin hekta 275 sannan kuma tana ƙarƙashin kulawar Hukumar Lafiya. University of Tabriz tana da makarantu 21, cibiyoyin koyarwa 29, da kuma cibiyoyin bincike guda 10. Hakazalika a halin yanzu akwai ɗalibai 50,000, ɗaliban ƙasashen waje 1000, malamai 819, mambobin kwamitin ilimi 780, da sauran ma’aikata su 800 a wannan jami’ar.

Zuwa yanzu, wannan jami’ar ta samu nasarar wallafa kimanin maƙala 23778 da mujallar ilimi 27 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida.
University of Tabriz na ɗaya daga cikin tsofaffin jami’o’in Iran wadda an assasata ne a shekarar 1947 da wannan sunan nata na yanzu kuma a lokacin ne ta fara gudanar da ayyukanta, amma bayan wucewar ‘yan shekaru an canza mata suna zuwa ‘University of Azarabadegan’. Daga ƙarshe bayan anyi juyin musulunci a shekarar 1978 aka sake canza mata suna zuwa sunanta na farko wato ‘University of Tabriz’. Wannan jami’a ta ƙunshi campus guda biyu. Ares International Campus da kuma Tabriz Self-Governing Campus [sauran rassanta, jami’o’in gwamnati ne da ke karɓar kuɗin makaranta daga wurin ɗalibai, an assasa su ne domin hana ɗalibai zuwa ƙasashen waje karatu].
A halin yanzu wannan jami’a ita ce cibiyar koyarwa mafi girma a yammaci da arewa maso yammacin ƙasar Iran. Ana karɓar ɗalibai a dukkan matakan karatu:

Kwasa-Kwasan Associate Degree 4
Kwasa-Kwasan Degree 164
322 رشته کارشناسی ارشدKwasa-Kwasan Masters 322
Kwasa-Kwasan PhD 209

Martabar Jami’a

University of Tabriz, sakamakon ƙoƙari da ayyukanta, da kuma matsayinta a ilmance idan an kwatanta da sauran jami’o’in duniya, Ta samu matsayi na 9 a jami’o’in Iran. Hakazalika a tsarin ranking na Times, ta samu matsayi na 801-900 a jami’o’in duniya.

Makarantu

Wannan jami’a tana da makarantu 21 waɗanda suka haɗa da:
_Faculty of Persian Literature and Foreign Languages
_ Faculty of Economics, Management and Commerce
_Faculty of Theology and Islamic Sciences
_Faculty of Physical Education and Sports Sciences
_Faculty of Geography and Planning
_Faculty of Veterinary Medicine
_Faculty of Mathematics
_Faculty of Chemistry
_Faculty of Education and Psychology
_Faculty of Natural Sciences
_Faculty of Electrical and Computer Engineering
_Faculty of Chemical and Petroleum Engineering
_Faculty of Civil Engineering and Technology
_Technical and Engineering College of New Technologies
_Faculty of Technical and Mechanical Engineering
_Faculty of Physics
_School of Agriculture
_Ahar Faculty of Agriculture and Natural Resources
_Marand Technical and Engineering University
_Middle Technical and Engineering Faculty

شهریه

رشته‌ها

A University of Tabriz, akwai kwasa-kwasai mabambanta a matakan PhD, Masters, HND da Degree.

Professional Doctor:
_Veterinary Medicine

PhD:
_Veterinary Reproduction Technologies

PhD:
_Language and Lyrical Literature
_Mystical Language and Literature
_Persian Language and Literature
_Philosophy
_English Language Teaching
_French Literature

Masters:
_Western Philosophy
_Persian Language and Literature
_Resistance Literature
_Comparative Philosophy
_Philosophy of Art
_The Ancient Languages of Iran
_Veterinary Parasitology
_Veterinary Histology
_Clinical Biochemistry
_Food Quality Control
_English Language Teaching
_English Language and Literature
_French Language Training
French Language and Literature

Continous Bachelor’s Degree;
French Language and Literature
_Azeri Turkish Language and Literature
_English Language and Literature
_Meat Hygiene and Inspection
_Meat Hygiene and Inspection
_Persian Language and Literature

Degree:
_Veterinary Laboratory Science

Sauran kwasa-kwasai:
_Mechanical Engineering
_Civil Engineering
_Architectural Engineering
_Da sauransu…

_Environmental Research Institute
_Social Research Institute
_Tabriz Basic Science Research Center
_Geotourism center
_Institute of History and Culture of Iran
_Da sauransu…

Ababen More Rayuwa

Ɗaya daga cikin muhimman siffofin wannan jami’ar shi ne kayan aikinta da ababen morewar ɗalibai. Jami’ar Tabriz tana da hostel guda 4, kayan wasanni tare da ingantattun kayan aiki don gudanar da gasa a fannoni da dama, cibiyar binciken kimiyya, sassan fasaha, ofishin hulɗa da masana’antu, Planetarium, Cibiyar binciken Applied Physics da Astronomy, Lambun nazari akan tsirrai, gidan tarihin zoology, gidan tarihi da al’adu na Iran, cibiyar nazari akan zamantakewa, ƙungiyar bincike akan Geography, ƙungiyar kimiyyar ɗan Adam, cibiyar nazari akan asalin kimiyya, da sauransu.


Abubuwan Alfaharin Jami’a

_University of Tabriz ita ce jami’ar Iran ta farko da ta fara shiga hukumar zartarwa ta tarayyar jami’o’in duniya
_Samun matsayi na farko a taron tattara nasarorin shekaru 30 na nizamin Iran (shekarar 2008)
_Karɓar lambar yabo daga mataimakin shugaban ƙasa dalilin bunƙasa sararin shuke-shuke da kuma sunnanta wannan al’adar
_Da sauransu…

Yanayin Wuri

Ƙofar asali ta University of Tabriz tana nan a titin Golgasht, tana kallon asibitin Imam Reza, babban kantin injuna, makarantar dentistry, ɗakin taron malaman jami’ar Tabriz University of Medical Sciences. Samuwar tashar jirgin ƙasa ta metro a wannan shiyyar ya sauƙaƙe zirga-zirga cikin gari.

Adireshin Jami’a

Adireshi: University of Tabriz, titin 29 Bahman, Tabriz, East Azerbaijan, Iran.


سوالات متداول

  1. دانشگاه تبریز در کدام مقاطع دانشجو می‌‎پذیرد؟
    این دانشگاه در تمامی مقاطع دانشجو می‌پذیرد.
  2. امکان برگزاری دوره به زبان انگلیسی وجود دارد؟
    بله، اگر تعداد دانشجویان از ده نفر بیشتر باشد.

Loading

Related Posts
Leave a Reply

Your email address will not be published.Required fields are marked *