Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Golestan University of Medical Sciences

Karatu a Golestan University of Medical Sciences

Loading

Lardin Golestan na ɗaya daga cikin lardunan arewacin ƙasar Iran wanda har zuwa shekarar 1997 ya kasance wani yanki na lardin Mazandaran, amma a 1997 an raba shi daga lardin Mazandaran inda ya koma lardi mai zaman kansa. Ɗaya daga cikin garuruwan wannan lardin shi ne garin Gorgan, wanda a ciki Golestan University of Medical Sciences take. A wannan rubutu, zamu yi ƙoƙarin kawo muku bayanai a kan batun karatu a Golestan University of Medical Sciences.

Gabatarwa

Golestan University of Medical Sciences wata jami’a ce a garin Golestan Jami’ar ta fara aiki ne a shekarar 1991 kafin a ɓamɓare ta daga jami’ar Mazandaran bayan samar da lardin Golestan a shekarar 1997. Jami’ar ke da alhakin gabatar da ayyukan kiwon lafiya da magani na baki ɗayan lardin Golestan. Har ila yau, ita ke da alhakin tafiyarda ayyukan koyarwa ga ɗaliban fannoni daban-daban na likitanci, a matakai daban-daban. A halin yanzu Saeidgol Firouzi ne shugaban wannan jami’a.

Akwai kimanin ɗalibai 3949 da membobin tsangayar ilimi 333 a wannan jami’ar yanzu haka. Bayanai sun nuna cewa jami’ar ta wallafa maƙalolin ilimi guda 1072 zuwa yanzu, a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida. Golestan University of Medical Sciences ta mallaki lambar yabo, kuma ta wallafa mujalla 5 na musamman, sannan ta shirya taruka 5 zuwa yanzu. Baya ga haka, jami’ar ta wallafa maƙala 2838 a matakin ƙasa da ƙasa.

Karatu a Golestan University of Medical Sciences

Martabar Jami’a

Tsarin ranking na Times a shekarar 2023, ya bayyana Golestan University of Medical Sciences a matsayin jami’a ta ɗaya a Iran. Tare da ƙoƙari da faɗi-tashin membobin kwamitin bunƙasa ayyukan waje na wannan jami’a, da kuma goyon bayan da jami’ar ta samu daga shuwagabanninta; An bayyana Golestan University of Medical Sciences a matsayin ta farko a jami’o’in Iran inda ta samu shiga jerin jami’o’i masu matsayi na 351 zuwa 400 a duniya. Wannan Matsayin ya dogara ne da abubuwa 13 waɗanda ke auna nagartar jami’a a wurare huɗu: Karatu, Bincike, Watsa ilimi, da kuma kimarta a duniya.

Makarantu

_ School of Medicine
_ School of Paramedicine
_ School of Health
_School of Dentistry
_Faculty of New Technologies
_ School of Nursing and Midwifery
_Gonbad Kavos Health Higher Education Complex

Cibiyoyin Bincike

_Gastroenterology and Liver Research Center
_Health and Social Development Research Center
_Nursing Research Center
_Dental Research Center
_Congenital Abnormalities Research Center
_Clinical Research Development Unit of Shahid Sayadi Hospital
_ 5 Azar Unit for Supporting the Development of Clinical Research
_Stem Cell Research Center
_Environmental Health Research Center
_Rheumatology Research Center
_ Cancer Research Center
_Ischemic Disorders Research Center
_Metabolic Disorders Research Center
_Psychiatric Research Center
_Children’s Research Center
_Health Research Center for Food, Medicinal and Natural Products
_Cell and Molecular Research Center
_ Neuroscience Research Center
_ Laboratory Science Research Center
_Center for Reproductive Health Research and Consultation in Midwifery
_ Student Research Committee
_Laboratory Animal Care Center

Jadawalin Kuɗin Makarantar Golestan University of Medical Sciences

Degrees TitlesAnnual TuitionDuration ( in Years )
Master's Programs (M.Sc.)2,500$2-3
Ph.D. Programs5,000$3-5
Specialty (Medicine)5,000$4-5
Subspecialty5,000$2-3
Fellowship5,000$1-2
Doctor of Medicine(M.D.)5,000$7
MBBS.5,000$5.5
Doctor of Dental Medicine(DDM)4,000$6
BDS.3,500$4
Bachelor's Program1,800$4
Registration(graduate)150$once
Registration(undergraduate)150$once
First Airport PickupIf neededonce
Furnished Accommodation(dormitory)1,200$yearly
Visa50$yearly
Insurance10$yearly
Persian Language Courses (if required)800$for 240 hours
English Language Courses (if required)1,000$for 240 hours
Persian Test20$once
English Test20$once
Tuition Fee5,000$yearly

Kwasa-Kwasai

_ Medicine
_Dentistry
_ Pharmacy
_Molecular Medicine
_ Clinical Biochemistry
_Medical Virology
_ Traditional Medicine
_ Nursing
_Biotech
_ General Hygiene
_ Midwifery
_ Anesthesia
_ General Surgery
_ Psychiatry
_ Radiology
_ Surgery Room
_Da sauransu

Asibitocin da ke ƙarƙashinta

_Gorgan 5 Azar Educational and Therapeutic Center
_Deziani Specialized and Super specialized Clinic
_Payambare Aazam Hospital (PBUH), Gonbad
_Shohadaye Gonbad Hospital
_Taleghani Hospital
_Shahid Sayadi Hospital
_Martyrs’ Hospital Bandargaz
_Imam Khomeini Hospital, Bandar Turkmen
_Kurdkoy Hospital
_Imam Reza Hospital Khanbebin
_Alavi Marawa Tepe Hospital
_Al-Jalil Aqqla Hospital
_Shahid Motahari Hospital Gonbad
_Baqiyat Allah Al-Azam Hospital
_Taleghani Hospital Gonbad
_Hazrat Masoumeh Azadshahr Hospital
_Fatemeh Zahra Hospital, Minovdasht
_Hazrat Rasool Akram (PBUH) Hospital, Kalala
_Health School of Iranian Medicine and Supplement

Cibiyoyin Lafiya

_Ramyan Health Center
_Gamishan Health Center
_Bandargaz Health Center
_Gorgan Health Center
_Gonbadkavus Health Center
_Galiksh Health Center
_Minodasht Health Center
_Kalala Health Center
_Bandar Turkmen Health Center
_Kurdkoy Health Center
_Azadshahr Health Center
_Aliabad Health Center
_Marawa Tepe Health Center
_Aq Qala Health Center

Golestan University of Medical Sciences

Ababen More Rayuwa

Babban Laburare: Saboda muhimmancin laburare a kowace makaranta, an buɗa babban laburaren wannan jami’a a watan Jamunary na sheharar 2010 lokaci ɗaya da kwanakin tunawa da juyin musulunci na Iran. Yanzu haka babban laburaren jami’ar (sashen ajiya da bayar da aro) na cikin harabar jami’ar wadda ke titin Shahid Beheshti, a nan yake gudanar da ayyukansa ga maziyartansa, ɗalibai masu ayyukan bincike, manazarta, kuma yana laburaren na fatan bunƙasa ayyukansa nan gaba kaɗan bayan ya koma cikin babban ginin jami’ar, inda zai samu sarari fiye da wanda yake da shi yanzu. Babban hadafin wannan laburare shi ne, samarwa da tsara kayan aikin da masu bincike suke buƙata, da kuma sauƙaƙe musu hanyoyin kaiwa ga bayanan.

Abinci: Ofishin kula da abinci, wanda aka kafa da manufar samarwa, da raba abinci mai lafiya da inganci, abinci mai gina garkuwar jiki, mai inganta lafiyar jiki da ruhin ɗalibai. Ofishin yana iya bakin ƙoƙarinsa wurin gamsar da ɗalibai ta hanyar samar musu da abinci mai inganci, a farashin da ya dace. Ofishin yana ba wa ɗalibai damar ziyarar gani da ido, domin ganin yadda suke gudanar da ayyukansu na harhaɗa kayan abinci, adanawa, dafawa, da rabawa. A kowace rana kafin ƙarfe biyu na rana, ɗalibi na da damar yayi rizab na abincin gobe. Amma shi abincin ranar asabar, ana iya yin rizab ɗinsa zuwa ƙarfe 10 na safiyar ranar juma’a ne kawai.

Abubuwan Alfahari

_Samun matsayin jami’a ta ɗaya a Iran, a tsarin ranking na Times.
_Tawagar Golestan University of Medical Sciences ta yi nasarar samun matsayi na 3 a yawon buɗe ido na ƙarshen mako wanda Jahrom University of Medical Sciences ta shirya.

Yanayin Wuri

Golestan University of Medical Sciences na nan cikin garin Gorgan, lardin Golestan. Ta fuskar yanayin wuri kuma, Golestan University of Medical Sciences na kusa da iyakar Shohadaye Gomnam, tare da masallacinta.

Adireshin Jami’a

Ginin Faculty of Medicine, Philosophical Higher Education Collection, farkon titin Shast Kala, Gorgan.

Tambayoyin da ake yi game da Golestan University of Medical Sciences

Ko Golestan University of Medical Sciences tana ba ɗaliban da ba ‘yan gari ba hostel?

A’a, Golestan University of Medical Sciences ba tada wani tsari na masauki ga ɗaliban cikin gari ko na waje.

Ya ake biyan kuɗin makaranta a Golestan University of Medical Sciences?

Ana biyan kuɗin makarantar Golestan University of Medical Sciences ne da dala.

Minene amintaccen shafin yanar gizo na wannan jami’a?

https://goums.ac.ir shi ne shafin wannan jami’a kuma ɗalibai za su iya bibiyar wannan shafin domin samun ƙarin bayani game da wannan jami’a.

Related Posts
Leave a Reply