Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Kashan University of Medical Sciences

Karatu a Kashan University of Medical Sciences

Loading

Kashan University of Medical Sciences jami’a ce da ke ƙarƙashin kulawar hukumar lafiya, a cikin garin Kashan. An gina makarantar likitanci ta Kashan University of Medical Sciences and Healthcare Services a fili mai girman murabba’in mita 22610. Karatu a Kashan University of Medical Sciences da bayanan da suka danganci hakan, zai iya zama batu mai muhimmancin gaske ga mutane, abunda zamu maida hankali akai kenan a wannan rubutu namu.

Gabatarwa

An assasa Kashan University of Medical Sciences a shekarar 1986. Wannan jami’a,  tana aiwatarda ayyukan kiwon lafiya ga sama da mutum dubu 450 a garin Kashan da Aran Bidgol.
A halin yanzu akwai ɗalibai 1988 da malamai 212 a wannan makaranta. Adadin waɗanda suka kammala karatu a wannan cibiya kuma 1698. Hakazalika bincike ya nuna cewa wannan jami’a tayi nasarar wallafa karɓaɓɓun maƙaloli guda 3480 na ƙasa da ƙasa, maƙalar ilimi guda 1441 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida. Sannan ta mallaki mujalla 3 na musamman. Har ila yau, jami’ar ce ta shirya manyan taruka guda 2.

Martabar Jami’a

Tsarin ranking na Times ya ayyana Kashan University of Medical Sciences a matsayi na 601 – 800. An fara wallafa wannan tsari ne a shekarar 2004. Abubuwanda tsarin Times yake la’akari dasu su ne; koyarwa (yanayin wurin koyarwa) _ Bincike (yawa, kuɗin shiga, fice) _ Ambato (tasirin koyarwa) _ Kuɗin shiga daga masana’antu (ƙirƙire-ƙirƙire) _ Kuɗin ƙasa da ƙasa (yawan ma’aikata, ɗalibai, da bincike).

Karatu a Kashan University of Medical SciencesMakarantu

_School of Medicine
_School of Dentistry
_School of Paramedicine
_Faculty of Health
_School of Nursing and Midwifery

Cibiyoyin Bincike

_Biochemistry and Nutrition Research Center in Metabolic Diseases
_Anatomical Sciences Research Center
_Trauma Research Center
_Physiology Research Center
_Trauma Nursing Research Center
_Gametogenesis Research Center
_Health Information Management Research Center
_Autoimmune Diseases Research Center
_ Research Center for Social Factors Affecting Health
_Infectious Diseases Research Center

Jadawalin Kuɗin Makarantar Kashan University of Medical Sciences

Sauran kuɗaɗe

Kwasa-Kwasan Kashan University of Medical Sciences

_Nutritional Sciences
_Laboratory Sciences
_Anesthesia
_General Hygiene
_Anatomical Sciences
_Nursing
_Geriatric Nursing
_Medical psychiatry
_Radiology
_Neurology Specialty
_Addiction Studies
_Bacteriology
_Neuroscience
_General Surgery
_Parasitology
_Da sauransu…
Domin samun cikakken bayani dangane da kwasa-kwasan Kashan University of Medical Sciences da matakan karatunsu, ku sauke wannan fayil.

Kwasa-Kwasan Kashan University of Medical Sciences

Kwasa-Kwasan Kashan University of Medical SciencesAsibitocin da ke ƙasanta

_Shahid Beheshti Hospital Complex, Kashan (gadaje 700)
_Ayatollah Yathrabi Hospital, Kashan
_Naqvi Kashan Hospital
_Kashan Brotherhood Hospital
_Metini Hospital Kashan
_Kashan Karganjad Hospital
_Kashan Emulation Hospital
_Saman Al-Hajj (AS) Hospital, Aran and Bidgol
_Shahid Rajaei Hospital, Aran and Bidgol
_Imam Hassan Mojtaba (AS) Hospital, Aran and Bidgol

Ababen More Rayuwa

Imam Ali (as) Hostel: An buɗa shi a watan farko na shekarar 1997 kuma yanzu haka akwai mutum 440 a cikin wannan hostel ɗin (yana da ɗakuna 100 masu ɗauke da wuraren karatu, kayan kallo, hita, ac, ban ɗaki, da sauran abubuwan buƙata).
Azzahra (as) Hostel: An buɗa wannan hostel ne a shekarar 1987 kuma yanzu haka akwai mutum 600 dake zaune a ciki (yana da na’urar ɗumama da sanyaya wuri. Haka kuma yanada ɗakin kallo mai girman murabba’in mita 35, masallaci, ɗakin taro, da sauran abubuwan buƙata).

Laburare:  An buɗa laburaren farko na wannan jami’ar ne a shekarar 1987 a wurinda aka maida School of Nursing and Midwifery yanzu  Wannan laburaren a halin yanzu yana da kwafin littafan farsi da na latin guda 47131, CD na farsi 673, da CD na latin guda 1001. Kowane daga makarantu da asibitocin wannan jami’ar yana da laburarensa daban, wanda dukansu suna ƙarƙashin dokoki da kulawar babban laburaren jami’ar. Ana gudanarda ayyuka daban-daban cikin babban laburare. Wasu daga cikin waɗannan ayyuka basu ta’allaƙa kai tsaye da maziyarta laburaren ba, haka kuma laburaren ne keda ikon tattarawa da shirya abubuwan karatu da suke cikin laburaren (kamar: Sashen zaɓe, sayen littafai, sashen rubuta catalogue, da sauransu…) Wasu daga cikin ayyukan kuma sun ta’allaƙa kai tsaye da maziyarta laburaren (kamar sashen bada aron littafai, sashen bada bayanai, da sauransu…)

Kayan aikin Kashan University of Medical SciencesAbubuwan Alfahari

_Samun matsayi na yabawa akan tsari mai taken “Design, Implementation, Evaluation of the Educational Decision Support System for Prescribing Antibiotics for Acute Respiratory Infections”
_Samun matsayi na farko da na biyu a bukin ɗalibai mai taken ‘Innovative Ideas of Education’ karo na huɗu.
_Samun daraja ta farko a fosta mai taken “Designing, Implementing, Evaluating the Training Course and Empowering Educational Ideation” bisa la’akari da projects da ayyukan group na ɗaliban likitanci na Kashan University of Medical Sciences na shekarar 2021.

Yanayin Wuri

Kashan University of Medical Sciences ta fuskar  yanayin muhalli, tana kusa da muhimman wurare kamar;  Asibitin Shahid Beheshti,   Kashan University of Medical Sciences and Healthcare Services,  Emergency na asibitin Shahid Beheshti,  Sarbok Bookstore,  Masallacin jami’ar,  da kuma  Supermarket na asibitin. 

Adireshin Kashan University of Medical Sciences

Adireshi: Titin Shahrdari, randabawul na 15 Khordad, Kashan.


Tambayoyin da ake yawan yi game da Kashan University of Medical Sciences

  1. Wasu irin documents ake buƙata don yin rajista a Kashan University of Medical Sciences?
    Passport, hoto, transcripts, certificates na karatu, CV, motivational letter, da recommendation letter.
  2. Shin Kashan University of Medical Sciences tana karɓar ɗalibai a dukan matakan karatru?
    A’a, zuwa yanzu (semester da ta gabata) tana karɓar ɗalibai a matakin specialization ne kawai.

[neshan-map id=”9″]

Related Posts
Leave a Reply