Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a University of Kurdistan

Karatu a University of Kurdistan

Loading

Jihar kurdistan tana yammacin ƙasar Iran ne sannan kuma tanada iyaka da ƙasar Iraq. Babban birnin wannan jihar shi ne Sanandaj. Mun shawartar ku da ku karanta wannan rubutun idan kuna sha’awar yin karatu a wannan jami’a.

Gabatarwa

University of Kurdistan ta fara aiki a shekarar 1974 a ƙarƙashin Tarbiat Moallem University Tehran (kafin ta fara aiki a ƙashin kanta a shekarar 1991). Dr. Freydon Motamad Waziri (ɗan siyasa kuma malamin jami’a) shi ne ya kafa wannan jami’a ta Kurdistan da Jami’ar Razi Kermanshah. A halin yanzu wannan jami’a tana ɗaya daga cikin jami’o’i masu ɗagowa a Iran da kuma duniya baki ɗaya.
Jami’ar nada ɗalibai 9000, malamai 350, da mambobin kwamitin ilimi 400. Binciken da akayi ya nuna cewa, jami’ar ta wallafa maƙalar ilimi 6315 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida, mujalla 12 na musamman, da maƙala 3951 a matakin ƙasa da ƙasa. Har ila yau, jami’ar ta karɓi baƙuncin taruka 27.

Martabar Jami’a

A sabon tsarin ranking na Shanghai na shekarar 2022, an bayyana Kurdistan University a matsayi na 301-400 a fannin Natural Science da Earth Science, matsayi na 401-500 kuma a fannin Biology da Agricultural Science. Har ila yau, Jami’ar Kurdistan ta samu matsayi na 301-400 a karon farko da ta samu shiga wannan tsarin ranking na Shanghai a shekarar 2021, a fannonin Biology da Agricultural Science.

Karatu a Kurdistan UniversityMakarantu

_Faculty of Humanities and Social Sciences
_Faculty of Language and Literature
_School of Basic Sciences
_School of Agriculture
_Department of Natural Resources
_School of Engineering
_School of Arts and Architecture
_Bijar Faculty of Engineering and Basic Sciences

Jadawalin Kuɗin Makarantar Kurdistan University

A wannan jami’a, dole ne ɗalibin ƙasar waje ya biya kuɗi dala 75 lokacin yin rajista, hakan ne zai bashi damar fara ayyukansa na registration.

Haka kuma ɗaliban wannan jami’ar zasu iya biyan kuɗi dala 350 a kowane zangon karatu domin suyi amfani da hostel zin wannan makaranta.

Kuɗin Makarantar Kurdistan University

Kwasa-Kwasai

_Business Management
_Economical Science
_Accounting
_Sociology
_Psychology
_Law
_Educational Science
_Physical Education
_Consultation
_Islamic Teachings
_Shafi’i Jurisprudence and Law
_Kurdish Language and Literature
_English Language and Literature and Linguistics
_Arabic Literature
_Persian Language and Literature
_Animal Science
_Horticultural Science and Engineering
_Food Industry Engineering
_Civil Engineering
_Mechanical Engineering
_Chemical Engineering
_Meteorology
_Geomorphology
_Fisheries
_Architecture
_Da sauransu…

Ku sauke wannan fayil na ƙasa domin samun cikakken bayani game da kwasa-kwasai da matakan karatun wannan jami’a.

Kwasa-Kwasan University of Kurdistan

Cibiyoyin Bincike

_Nanotechnology Research Institute
_Medicinal Plants Research Unit
_Strawberry Research Center
_Research Institute of Kurdistan Studies
_Water Science and Engineering Research Center
_ Microgrid and Smart Networks Research Center
_Forestry Research and Development Center
_Technology Units Growth Center

Mujalloli da wallafe-wallafen ilimi da al’adu

_A Research Paper on Kurdish Literature
_Research Paper on Marketing Management
_Reading Research Quarterly
_Teaching Research Quarterly
_Two Quarterly Journals of School Management
_Family Counseling and Psychotherapy Quarterly
_Urban Studies Quarterly
_Runahi Journal (specialized legal and jurisprudential scientific journal)
_Geh Shatyar

Kwasa-Kwasan University of KurdistanAbubuwan Alfahari

_Ayyana University of Kurdistan a matsayin fitattar jami’a da cibiyar International Cooperation Studies tayi.
_Samun tallafin bincike daga Gidauniyar Kimiyya ta ƙasar Swiss wanda ɗaya daga cikin mambobin kwamitin ilimi na wannan jami’a ya yi.
_Taron ƙaddamarda yarjejeniyar fahimtar juna kan kimiyya, bincike, da bincike mai zartarwa tsakanin tafiyarda harkokin bunƙasa kasuwanci, cibiyoyin haɓaka ƙirƙire-ƙirƙire tare da kamfanin masana’antun sinadarin Biston.
_Ayyana sunayen mambobin kwamitin ilimi na wannan jami’a ta Kurdistan su huɗu a list ɗin manazarta da aka fi ambata (citing) daga Iran.
_Gogewa da nasarar Jami’ar Kurdistan wurin haɓaka haɗin gwiwar al’umma da masana’antu.
_Kasancewar Jami’ar Kurdistan cikin jerin manyan jami’o’in duniya da suka cika sharuɗa a shekarar 2022.
_Kasancewar jami’ar Kurdistan a cikin manyan jami’o’i a Asia.
_Dr. Hasan Bivarani ya zama fitaccen mamba na tsangayar ilimi na Iran.
_Samun nasarar shiga tsarin martaba jami’o’i na duniya.
_Girmama ɗaliban Jami’ar Kurdistan a matakin farko na gasar Olympics ɗalibai na ƙasar karo na 27, a shekarar 2022.
_Kammala yarjejeniyar fahimtar juna kan haɗin gwiwar kimiyya da bincike tsakanin Jami’ar Kurdistan da Jami’ar Ljubljana, Slovenia.
_Da sauransu…

Abubuwan More Rayuwa

_Samar da Inshorar lafiya ga membobin kwamitin ilimi da ma’aikata da tattara takardu da kudade tare da miƙa su ga ma’aikata
_Shirya sansanonin yawon bude ido da na ziyarori
_Aiwatar da duk wata inshora da keda alaƙa da jami’a, kamar inshorar gobara, ambaliya, inshorar girgizar ƙasa da duka nau’o’in inshorar lamuni kamar ɗakunan gwaje-gwaje, wuraren wasanni, haɗurran da suka shafi ɗalibai da sauran su
_Gudanar da gasar wasanni daban-daban a mabambantan lokuta
_Aiwatarda abubuwan da suka shafi inshorar haɗuran wasanni
_Sauƙaƙa yuwuwar amfani da wuraren kwana kamar gidajen baƙi na jami’o’in ƙasar da sauran su
_Ƙoƙarin samarda sababbin abubuwan more rayuwa ga abokan aiki
_Yuwuwar bayar da inshorar mota a matsayin bashi
_Bayarda wasiƙu ga abokan aiki don amfani da wuraren jin daɗi na wasu cibiyoyi
_Aiwatarda abubuwan da suka shafi inshorar rayuwa da haɗurran rukunin na ma’aikata da membobin kwamitin ilimi

Wurin Kwanan Ɗalibai: University of Kurdistan nada hostel guda 10 na ɗalibai maza, hostel 12 na ɗalibai mata a halin yanzu. A jimlace, waɗannan hostel zasu iya ɗaukar ɗalibai 6000. Duka ɗaliban ƙasar waje suna zaune ne a hostel ɗin ɗalibai (Sashen kula da wuraren kwanan ɗalibai na daya daga cikin sassan harkokin ɗalibai wanda  alhakin tafiyarda duk al’amuran da suka shafi wuraren kwanan ɗalibai (hostel), zartar da ƙa’idojin hostel, ƙoƙari wurin haɓaka inganci da yawan hostel, samar da masauki ga baƙin ɗalibai, da sauransu, yana wuyansu. Wannan sashen ya kasu kashi biyu; sashen kula da al’amuran hostel na maza da sashen da ke kula da na mata)

Babban Laburare: Wannan laburaren ya fara aiki ne a shekarar 1975 da littafai ƙasa da kwafi 1000, tare da ma’aikaci ɗaya, a wani wuri mai girman murabba’in mita 12. Bayan wani lokaci, tare da faɗaɗa girman wannan laburaren a makarantar Human Sciences, ya cigaba da gudanar da ayyukansa da kwafin littafai 60,000 na farisanci, latin, larabci, da sauransu. Bayan kammala aikin samar da babban laburaren jami’ar Kurdistan a watan Janairun shekarar 2009, aka shiga jigilar kayan laburaren zuwa wannan sabon da aka gina. A sabon ginin laburaren akwai littafai na farisanci, kurdanci, larabci, da latin sama da kwafi 126,000. Hakazalika akwai Digital References a sassa daban-daban kimanin guda 8000.

Kayan aikin Jami'ar Kurdistan Yanayin Wuri

Jami’ar Kurdistan tana cikin garin Sanandaj, a titin ƙofar yamma. Ta fuskar yanayin wuri,  tana kusa da  Asibitin Social Security,  hakazalika  Central Library,  Faculty of Natural Resources,  da kuma  Agricultural Predecessor.

Adireshin University of Kurdistan

Adireshi: University of Kurdistan, titin Pasdaran, Sanandaj, Kurdistan.


Tambayoyin da ake yawan yi

  1. Yaushe ake fara azuzuwan koyon farisanci?
    Kuna iya ziyartar ɓangaren kalandar karatu a sashen cibiyar koyarda yaren farsi ga waɗanda ba yarensu bane, a shafin yanar gizo na University of Kurdistan.
  2. Shin ko online ake gabatarda azuzuwan koyon farsi a wannan jami’a?
    Eh
  3. Kwana nawa zamu iya yi idan mun je ƙasarmu?
    Idan har zaku wuce wata 3 a ƙasashenku, to dole ne ku sake neman izinin shigowa Iran (biza).

Loading

Related Posts
Leave a Reply

Your email address will not be published.Required fields are marked *