Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Urmia University of Medical Sciences

Karatu a Urmia University of Medical Sciences

Loading

A wannan rubutun, zamuyi ƙoƙarin kawo muku bayani game da karatu a Urmia University of Medical Sciences da sauran bayanai da suka shafi wannan makaranta. Urmia shi ne babban birnin Azerbaijan ta yamma, Urmia University of Medical Sciences ɗaya ce daga jami’o’i da cibiyoyin koyarwa dake cikin wannan garin.

Gabatarwa

Urmia University of Medical Sciences (wadda ke ƙarƙashin hukumar lafiya) ita ce jami’ar likitanci ta zamani mafi daɗewa a Iran wadda ke cikin garin Urmia. Wannan cibiya ta fara gudanar da ayyukanta a matsayin ɗaya daga cikin sassan koyarwa na jami’ar Urmia (Urmia University) a shekarar 1977. A halin yanzu akwai ɗalibai 4376, da malamai 313 a wannan jami’a.
Bincike ya nuna cewa wannan jami’ar ta samu nasarar wallafa maƙala ta ilimi guda 611 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida (wanda suka haɗa da maƙalar mujalla 195 da maƙalar taro guda 416) da maƙala 3786 a matakin ƙasa da ƙasa. Jami’ar ta mallaki mujalla ta musamman guda 2.

Martabar Jami’a

Tsarin ranking na Times ɗaya ne daga fitattun tsarukan ranking ɗin jami’o’i da cibiyoyin koyarwa na gaba da sakandare wanda aka fitar saboda kwatanta matsayin jami’o’i da juna a ilmance. A shekarar 2023, jami’a 99 ne suka samu halartar wannan taron daga ƙasar Iran, inda Urmia University of Medical Sciences ta samu matsayi na 401 – 500.

Karatu a Urmia University of Medical SciencesMakarantu

_School of Medicine
_School of Dentistry
_School of Pharmacy
_School of Paramedicine
_Faculty of Health
_School of Nursing and Midwifery
_Khoi Faculty of Medical Sciences
_Mahabad School of Nursing
_Selmas School of Nursing
_Miandoab School of Nursing
_Buchan School of Nursing
_Nakdeh Higher Health Education Complex

Cibiyoyin Bincike

_Urmia Lake Cohort Study Center
_Cellular and Molecular
_Nephrology and Kidney Transplantation
_Health of food and Beverages
_Pregnancy Health
_Social Factors Affecting Health
_Neurophysiology
_Solid Tumor
_Maternal and Child Obesity
_The Growth of Health Technology
_Hospital Patient Safety
_Comprehensive Research Laboratory
_Experimental and Applied Pharmaceutical Sciences
_Solid Tumor
_Clinical Research Development Unit
_Hematology, Tuberculosis Immunotherapy and Stem Cells

Ciiyoyin koyarwa da jinya

_Imam Khomeini Educational and Medical Center
_Shahid Motahari Educational and Therapeutic Center
_Taleghani Educational and Therapeutic Center
_Seyyed Al-Shohda Educational and Treatment Center
_Razi Educational and Therapeutic Center
_Kausar Women’s Comprehensive Educational and Treatment Center

Kuɗin Makarantar Urmia University of Medical Sciences

Kwasa-Kwasai

_Medicine
_Biochemistry
__Health Policy and Management
_
_Epidemiology
_Parasitology
_Anatomical Sciences
_Physiology
_Nutritional Sciences
_Medical Physics
_Microbiology
_
_Food Hygiene and Safety (Based on Research)
_Cellular and Molecular (based on research)
_
_Surgery Room
_Health Information Technology
_Laboratory Sciences
_Radiology
_Anesthesia
_
_Medical Informatics
_General Health
_Professional Health Engineering
_Environmental Health Engineering
_
_Ergonomics
_Medical Entomology
_Health Economy
_Medical Emergency
_Nursing
_Midwifery
_Consultation in the Field of Midwifery
_Internal Surgery Nursing
_Psychiatric Nursing
_Special Care Nursing
_
_Dental
_Pharmacy
da sauransu.
Domin samun cikakken list na kwasa-kwasan da akeyi a wannan jami’a da matakan karatu, ku sauke wannan fayil ɗin.

Kwasa-Kwasan Urmia University of Medical Sciences

Kuɗin Makarantar Urmia University of Medical SciencesAbubuwan Alfahari

_Ɗaya daga cikin abubuwan alfaharin Urmia University of Medical Sciences shi ne dashen ƙoda da akeyi a wannan jami’a. Idan aka duba daɗewa, daga Shahid Beheshti University of Medical Sciences, sashen dashen ƙoda na Urmia University of Medical Sciences shi ne na farko a Iran wanda ya fara gudanarda ayyukansa ne a shekarar 1988.
_Samar da samfurin kayan aikin gano cutar Acute Leukemia tun tana matakan farko, wanda Khanom Dr. Sahar Mehranfer tayi.
_Da sauransu…

Ababen More Rayuwa

Hostel ɗin Kausar: Wannan hostel ɗaya ne daga cikin wuraren kwanan ɗalibai mata wanda aka fara ginawa a shekarar 2008 aka kuma fara aiki da shi a shekarar 2011. Girman filin wannan hostel ya kai murabba’in mita 4800 tare da gine-ginen murabba’in mita 4400. Kayayyakin da suke cikin wannan hostel sun haɗa da: Masallaci, ɗakin karatu, zauren wasanni, zauren kallo, koren fili, ɗakin kwamfuta, ɗakin shawara, ɗakin baƙi, da ɗakin guga.
Hostel ɗin Golestan: Wannan ma ɗaya ne daga cikin wuraren kwanan ɗalibai mata da ke cikin Hazrat Fatima (as) Dormitory Complex wanda aka fara ginawa a shekarar 1989, aka kuma fara amfani da shi a shekarar 2008. Wannan hostel nada girman murabba’in mita 9000, da gine-ginen murabba’in mita 500. Wannan hostel yana da abubuwa kamar shagon kayan abinci, masallaci, ɗakin karatu, cibiyar al’adu, zauren wasanni, ɗakin kallo, koren fili, da ɗakin kwamfuta.

Hostel ɗin Bostan: Wannan ma ɗaya ne daga cikin wuraren kwanan ɗalibai mata dake Hazrat Fatima (as) Dormitory Complex. An fara gina shi ne a shekarar 1993, inda aka fara  amfani da shi a shekarar 1994. Girman filin wannan hostel murabba’in mita 11000, girman gine-gine kuma murabba’in mita 6300. Abubuwan wannan hostel sun haɗa da: Shagon kayan abinci, masallaci, ɗakin karatu, laburare, cibiyar al’adu, zauren wasanni, ɗakin kallo, koren fili, ofishin basij, cibiyar Al-Qur’ani, ɗakin tattaunawa, da ɗakin kwamfuta.
Hostel ɗin Shahid Qoli Poor: Wannan kuma ɗaya ne daga cikin wuraren kwanan ɗalibai maza dake hanyar Salmas, Titin Shahid Qoli Poor, kusa da Mu’awanat na abinci da magani. An fara amfani da wannan hostel ne a shekarar 2008. Girman filin wannan hostel murabba’in mita 3500, girman gine-ginensa ma haka. Yana da abubuwa kamar masallaci, ɗakin karatu, laburare, cibiyar al’adu, zauren wasanni, ɗakin kallo, koren fili, da ɗakin kwamfuta.
Hostel na Shahid Gom Nam: Ɗaya ne daga cikin wuraren kwanan ɗalibai maza na Urmia University of Medical Sciences, wanda aka fara ginawa a shekarar 2008, aka kua fara amfani da shi a shekarar 2012. Girman wannan Hostel murabba’in mita 6400. Hostel ɗin yana da abubuwa kamar; fridge, TV, Hita, masallaci, zauren wasanni, da suaransu.

Kayan Aikin Urmia University of Medical SciencesYanayin Wuri

Jami’ar tana Azerbaijan ta yamma, cikin garin Urmia, titin Keshavarz. Tana kusa da wurare kamar Urmia School of Agriculture, Faculty of Basic Sciences ta jami’ar Urmia (Pardise Nazloo), da kuma West Azerbaijan Science and Technology Park.

Adireshin Urmia University of Medical Sciences

Adireshi Urmia University of Medical Sciences, Koe Urjans, titin Risalat.


Tambayoyin da ake yawan yi dangane da Urmia University of Medical Sciences

  1. Wasu irin takardu ake buƙata domin rajista a Urmia University of Medical Sciences?
    Passport, hoto, scripts, certificate, CV, motivational letter, recommendation letter.
  2. Shin biyan kuɗin hostel lazim ne ?
    Eh.
  3. Shi ɗaliban Iraq zasu iya yin transfa a Urmia University of Medical Sciences?
    Eh, zasu iya yin transfa zuwa ƙasarsu bayan sun kammala semester ta biyu.

[neshan-map id=”2″]

Related Posts
Leave a Reply