Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Mazandaran University

Karatu a Mazandaran University

Loading

Jami’ar Mazandaran na ɗaya daga cikin jami’o’i mafi daraja na Iran a fannin Basic Sciences, Engineering Sciences da Economics, hakazalika ita ce cibiyar koyarwa ta gaba da sakandare mafi girma a lardin Mazandaran wacce ta fara gudanar da ayyukanta a shekarar 1979. A wannan rubutun zamu mayar da hankali wurin bayani akan yadda ake karatu a Mazandaran University.

Gabatarwa

Jami’ar Mazandaran mai tarihin fiye da shekaru 47, ta samu nasarar ɗaukaka mastayinta na ilimi ta hanyar bunƙasa yawa da ingancin karatunta, kuma a kowace shekara tana karɓar adadi mai yawa na ɗalibai. Haka kuma tun daga shekarar 2001 wannan jami’ar take karɓar ɗaliban waje. Girman filin makarantar hekta 4000, girman gine-ginen da ke ciki murabba’in mita 150,000, girman gine-ginen sashen karatu kuma murabba’in mita 58,000, filin azuzuwan karatu kuma murabba’in mita 12.

Karatu a Mazandaran University
A wannan jami’a akwai ɗalibai 13580, ɗaliban waje 783, mambobin fakwalti 350 (farfesoshi 37, ƙananan farfesoshi 88, mataimakan farfesa 200, malamai 24), wasu adadi na malamai masu lasisi da suke a bakin aiki. Bincike ya nuna cewa Jami’ar Mazandaran ta wallafa maƙalolin ilimi guda 11563 a wallafe-wallafen cikin gida da taruka (mujalloli guda 3714 da mujallar taro guda 7849), maƙaloli 6078 a matakin ƙasa da ƙasa. Jami’ar Mazandaran ta shirya taruka 19. Har ila yau, jami’ar ita ce mamallakiya kuma mawallafiyar mujalloli 13 na musamman.

Martabar Jami’a 

Sabon bayanin da  matattarar bayanai ta Times ta wallafa a shekarar 2023 ya nuna cewa a cikin ƙwararrun jami’o’i 1662 na duniya a tsarin tantance jami’o’i na Times ɗin, Jami’ar Mazandaran tana tsakanin matsayi na 1001 zuwa 1200.

Makarantu 

_Makarantar Theology and Islamic Studies
_Makarantar Law and Political Science
_Makarantar Chemistry
_Makarantar Economic and Administrative Sciences
_Makaranatar Humanities and Social Sciences
_Makaranatar Sports Sciences
_Makaranatar Mathematical Sciences
_Makaranatar Basic Sciences
_Makaranatar Marine and Environmental Sciences
_Makaranatar Engineering and Technology
_Makaranatar Persian Literature and Foreign Languages
_Makaranatar Cultural Heritage, Handicrafts and Tourism
_Makaranatar Arts and Architecture

Kwasa-Kwasan Mazandaran UniversityCibiyoyi

_APA Specialized Center 
_Nano and Biotechnology Research Group 
_Women’s Education and Employment Gesearch Group 
_Center for the Growth of Technology Units
_Algebraic Superstructures and Fuzzy Mathematics Research Group
_Persian Education Center for Non-Persian Speakers 

Kwasa-kwasan karatu

_Quran and Hadith Sciences
_Islamic Jurisprudence and Foundations
_Islamic knowledge
_Islamic philosophy and theology
_Physiology
_Sports Biomechanics
_Political Science
_Law 
_Accounting
_Economic Sciences
_Management 
_Social Sciences
_Geography
_Educational Sciences
_Tourism Management
_Biology
_Cellular and Molecular Biology
_Physics
_Mathematics
_Statistics
_Computer Engineering – Software
_Electrical Engineering
_Mechanical Engineering
_Civil Engineering
_Information Technology
_Urban Engineering
_Handicrafts
_Physics of the Sea
_Sea Chemistry
_Sea Biology
_Archaeology
_Tourism
_Anthropology
_Artificial Arts
_English Language and Literature
_English Language Teaching
_Da sauransu
Ku sauke wannan fayil domin samun cikakken list na kwas da matakin karatu da kuke buƙata.

Kwasa-Kwasan Masters a Mazandaran University

Kwasa-Kwasan PhD a Mazandaran University

Kuɗin makarantar Mazandaran University

Kwas ɗin KaratuMatakin Karatutsawon lokacin karatuKuɗin makaranta (na shekara)
Kwasa-kwasan Literature da HumanityDigirin Farko (BSc)Shekara 4$375
Masters (MSc)Shekara 2$850
PhDShekara 3 zuwa 4$1250
Sauran kwasa-kwasaiDigirin Farko (BSc)Shekara 4$450
Masters (MSc)Shekara 2$1000
PhDShekara 3 zuwa 4$1500

Abubuwan Alfahari

Bayan shuɗewar shekaru 40 da assasa Jami’ar Mazandaran, ɗaya daga cikin nasarorin wannan makaranta shi ne martabar da malamanta biyu suka samu, Farfesa Jahanbakhsh Rauf da Farfesa Reza Orjani, waɗanda aka sanya a list ɗin masana kimiyya na duniya. Har ila yau, jami’ar ta lashe matsayin jami’a ta 6 mafi kyau a shekarar 2013.

Abubuwan more rayuwa 

Jami’o’i da cibiyoyin koyarwa suna wadata ɗalibai da abubuwa da dama don ganin cewa sun samu walwala daidai gwargwado a lokacin karatunsu. Daga cikin waɗannan abubuwan akwai wuraren cin abinci na Jami’ar Mazandaran, ɗakin wasanni, wuraren jinya, wurin koyarda yaren farsi ga waɗanda basu jin yaren, da zangunan shaƙatawa na ɗalibai.
Jerin wuraren kwanan jami’ar:
_Wurin kwana mai sunan Shahid Nawab Safavi: Wurin kwana domin mambobin kwamitin ilimi, da ɗalibai maza masu karatun Masters da PhD
_Wurin kwana mai sunan Hazrat Zainab(as): Wurin kwanan ɗalibai mata a dukan matakan karatu
Wurin kwana mai sunan Imam Hussain (as): Wurin kwanan ɗalibai maza da suke matakin digiri na farko
_Haɗakar Masaukai na Aftab: Wannan wuri ne da yake da alaƙa da Jami’ar Mazandaran kuma yana da dukan abubuwa.
_Masaukan ɗalibai masu zaman kansu

Kayan aikin Mazandaran UniversityMuhalli:

Mazandaran University tana nan a Babolsar da Pasdaran, tsakanin Pasdaran 3 da randabawul na Khalije Fars. Dangane da yanayin wuri kuma, wannan jami’ar tana kusa da muhimman wurare irinsu Gadar Babolsar, kogin Babolrood, Babolsar Plaza, Shaqa’iq Cinema, Babolsar Cable Bridge, Gidan cin abinci na Keshti, Bankin Gol Babolsar, da kuma Post Office.

Adireshin Jami’ar 

Adireshi: Titin Pasdaran, Sazman Markazi, Babolsar – Mazandaran 


Tambayoyin da ake yawan yi game da Jami’ar Mazandaran

  1. Shin akwai wurin kwana da aka tanada saboda ɗaliban wannan jami’a masu iyali? 
    Eh, akwai.
  2. A Jami’ar Mazandaran da turanci ake karatu ko da farsi?
    Akwai yiwuwar ayi karatu da turanci a wasu ɗaiɗaikun kwasa-kwasai, kuna iya tuntuɓarmu domin samun ƙarin bayani.

[neshan-map id=”24″]

Related Posts
Leave a Reply