Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Qom University of Medical Sciences

Karatu a Qom University of Medical Sciences

Loading

Qom University of Medical Sciences ɗaya ce daga cikin jami’o’in likitanci na lardin Qom. A wannan rubutu, za mu kawo muku bayanan da suka shafi yanayin karatu a wannan jami’a ta Qom University of Medical Sciences, ku kasance tare da mu.

Gabatarwa

Qom University of Medical Sciences ɗaya ce daga cikin jami’o’in lardin Qom wadda ta fara gudanar da ayyukanta a matsayin jami’a, a shekarar 2005. Bayan samar da lardin Qom a shekarar 1999 da kuma haɓaka sansanonin kiwon lafiya da magani na Qom na wancan lokacin, ta kasance tana aiki a matsayin ɗaya daga cikin cibiyoyin da ke ƙarƙashin Tehran University of Medical Sciences kuma ita ke kula da al’amuran da suka shafi kiwon lafiya da jinya na Qom, an kafa ta a matsayin makarantar likitanci da ayyukan kiwon lafiya. A lokaci guda kuma ta samu lamuncewar hukumar lafiya da karatun likitanci don samar da makarantun nursing, kafin a shekarar 1997 ta fara ayyukanta ta hanyar ɗauka da horar da ɗaliban kwas ɗin Nursing a matakin digiri.

Qom University of Medical Sciences a farkon shekarun assasata, tana karɓar ɗalibai maza ne kawai, amma bayan rufe Fatemieh University of Medical Sciences ta Qom wadda ita kuma ta mata ce, ta fara karɓar duka jinsin ɗalibai (maza da mata). Qom University of Medical Sciences ta shiga horar da ƙwararrun mataimaka na musamman kwasa-kwasan likitanci, surgery, emergency medicine, neurology, gynecology, da cardiology.

A halin yanzu akwai ɗalibai 2294 da malamai 206 a wannan jami’a. Bincike ya nuna cewa jami’ar ta wallafa maƙalolin ilimi 743 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida zuwa yanzu (228 na mujalla, 515 na taruka). Qom University of Medical Sciences ta wallafa mujalla 4 na musamman kuma ta shirya taro ɗaya zuwa yanzu. Har ila yau, jami’ar ta wallafa maƙaloli 1889 a matakin ƙasa da ƙasa.

Qom University of Medical Sciences

Martabar Jami’a

Sakamakon da tsarin ranking na Times ya fitar a shekarar 2023 ya nuna cewa wannan jami’a ta samu matsayi na 401-500.

Makarantu

_ School of Medicine
_ School of Paramedicine
_ School of Dentistry
_ School of Health
_ College of Health and Religion
_ School of Nursing and Midwifery
_ School of Traditional Medicine

Cibiyoyin Bincike

_ Center for Basic Research and Cognitive Medicine
_ Gastrointestinal and Liver Diseases Research Center
_ Neuroscience Research Center
_ Spiritual Health Research Center
_ Spiritual Health Research Center
_ Cell and Molecular Research Center
_ Environmental Pollutants Research Center
_ Children’s Clinical Research Development Unit
_ Shahid Beheshti Clinical Research Development Unit
_ Khairin Salamat Clinical Research Development Unit

Kuɗin Makarantar Qom University of Medical Sciences

Cibiyoyin koyarwa da jinya

_ Shohada Educational and Therapeutic Center
_ Kamkar Educational and Therapeutic Center – Arabnia
_ Khairin Salamat Medical Research Educational Complex
_ Hazrat Masoumeh (AS) Educational and Therapeutic Center
_ Shahid Beheshti Educational and Therapeutic Center – Amiral-Momenin (AS)
_ Masumieh School of Iranian Medicine
_ Specialized Dental Center

Sassan koyarwa (Departments)

School of Medicine:
_ Biochemistry and Genetics
_ Physiology and Pharmacology
_ Microbiology and Immunology
_ Anatomical Sciences
_ Tissue Engineering and Applied Cell Science
_ Islamic Teachings
_ Medical Education
_ Elderly Science
_ Midwifery
_ Cardiovascular
_ Internal
_ Surgery
_ Neurology
_ Children
_ Psychiatry
_ Infectious
_ Obstetrics and Gynecology
_ Social and Family Medicine
_ Emergency Medicine
_ Anesthesia

School of Paramedicine:
_ Department of Anesthesiology
_ Operation Room Technology
_ Medical Emergency
_ Laboratory Sciences

Dental College:
_ Oral and Facial Diseases
_ Oral, Jaw and Facial Surgery
_ Endodontics (root canal treatment)
_ Pediatric Dentistry
_ Restorative Dentistry
_ Dental Prostheses
_ Periodontics
_ Orthodontics
_ Radiology

School of Health:
_ Environmental Health Engineering
_ Occupational Health and Safety Engineering
_ General Hygiene
_ Health Education and Promotion
_ Epidemiology and Biostatistics

College of Health and Religion:
_ Quran and Hadith Sciences in Health
_ Health Philosophy and Ethics
_ History of Medical Sciences

School of Nursing and Midwifery
_ Internal Surgery
_ Children’s Nursing
_ Psychiatric Nursing
_ Community Health

School of Iranian Traditional Medicine:
_ Traditional Medicine

Qom University of Medical Sciences

Abubuwan more rayuwa:

Wurin Kwana: Abubuwan more rayuwa na hostel sun haɗa da fridge, carpet, wadrobe, gas cooker, computer, kujeri, teburin karatu, da sauransu da kuma samarwa da bunƙasa kayan aikin gine-ginen gidajen ɗalibai. Ɗakunan kwanan ɗalibai mata suna ɗaukar mutum 4.
Ɗakunan maza kuma suna ɗaukar mutum 4 zuwa 10, ya danganci girman ɗakin. Wuraren kwanan ɗalibai na wannan jami’a sun haɗa da:

_ Wurin kwanan ɗalibai mata na Kowsar: Hostel ɗin Kowsar (na mata) na nan a titin Gadir, daura da filin wasa na Yadegare Imam, cikin Harabar Qom University of Medical Sciences.
_ Wurin kwanan ɗalibai maza na Imam Khomeini: Yana titin Shahid Beheshti, daura da cibiyar kiwon lafiya ta garin Qom.

Abinci: Kiyaye lafiya da tsaftar abincin ɗalibai na ɗaya daga cikin muhimman wazifofin sashen gudanarda al’amuran ɗalibai, saboda haka sashen abinci ne keda alhakin lura da tattara kayan abinci masu kyau da inganci, dafawa, da kuma raba abincin safe, na rana, da na dare tsakanin ɗalibai, a babban wurin cin abinci na jami’ar ko hostel, ta hanyar amfani da tsarin abinci na kai-tsaye (automatic).

Abubuwan more rayuwa: Daga cikin abubuwan more rayuwa na wannan jami’ar akwai: Wasanni (harbi, jifan dart, ƙwallon kafa na tebur, gym, kokawa, table tennis, badmiton, basketball, volleyball da ƙwallon ƙafa), ayyukan bada shawara da psychology, yawon ziyara da buɗe ido.

Yanayin Wuri

Qom University of Medical Sciences na nan a unguwar Bajak 1 ta garin Qom, a titin Za’er, titin Lavasani. Tana kusa da wurare kamar asibitin Ayatullah Golpaygani, Esteghlal Hotel, wurin ɗaukar hoto na Parto-tib Azma, rukunin sayarda wayoyi na Al-Zahra, da kuma asibitin Kamkar Arabniya.

Adireshin Qom University of Medical Sciences

Qom – Titin Shahid Lavasani (Saheli) – Qom University of Medical Sciences

Shafin jami’ar: muq.ac.ir

Tambayoyin da aka yi game da Qom University of Medical Sciences

Yaya ake neman hostel a wannan jami’ar?

1- Nema da cike form ɗin hostel daga shafin jami’ar tare da miƙa shi ga ofishin kula da hostel da ke cikin harabar jami’ar.
2- Samun takardar yarjejeniyar zama a hostel kamar yadda aka nuna a shafin makarantar, da miƙa ta ga ofishin kula da jindaɗin ɗalibai da ke harabar jami’ar.
Biyan kuɗin hostel tare da taimakon ofishin kula da hostel.

Shin ayyukan bada shawara da ake gabatarwa ga ɗalibai kyauta ne
ko ana biyan wasu kuɗi?

Duka ayyukan bada shawara ga ɗalibai
kyauta ne kuma ana yi ma duka ɗalibai a kowane matakin karatu.

Yaya sabis ɗin zirga-zirgar ɗalibai yake?

akwai motocin jigilar ɗalibai daga hostel zuwa makarantunsu kuma akwai jadawalin lokutan tashinsu manne
a ƙofofin hostel ɗin ɗalibai da na makarantunsu.

Related Posts
Leave a Reply