Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Iran University of Medical Sciences

Karatu a Iran University of Medical Sciences

Loading

Iran University of Medical Sciences jami’ar likitanci ce mai daraja. Ku kasance tare da mu a wannan rubutun domin sanin yanayin karatu a wannan jami’a wadda ta samu nasarori masu yawa, wato Iran University of Medical Sciences.

Gabatarwa

An assasa [Iran University of Medical Sciences]Iran University of Medical Sciences a watan July na shekarar 1973 a cikin garin Tehran (babban birnin tarayya na Iran) kuma ta kasance a sahun manyan cibiyoyin kiwon lafiya na lokacin.
A halin yanzu wannan jami’a na da ɗalibai 7206, ɗaliban ƙasashen waje 521, makarantu 12, malamai 980, da membobin tsangayar ilimi 1015. Iran University of Medical Sciences ta wallafa maƙalolin ilimi guda 4686 zuwa yanzu a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida, ta kuma wallafa mujalla 9 na musamman. Har ila yau, jami’ar ta shirya taruka 31.

Manyan ƙawayen wannan jami’a a harkokin ilimi sun haɗa da: Tehran University of Medical Sciences, Shahid Beheshti University of Medical Sciences, Islamic Azad University of Science and Research Tehran, Tarbiat Modares University, da kuma Mashhad University of Medical Sciences.

Abdol Hosein Sami’i shi ne wanda ya kafa wannan jami’a. Da fari laburaren jami’ar aka fara samarwa, aka kuma mayarda ita laburare mafi girma na likitanci ta hanyar samarda dubban litattafan likitanci a cikinta. Bayan samun alaƙa da muhimmiyar cibiyar bayanan likitanci ta Amurka ta hanyar satellite, ta zama ɗaya daga cikin muhimman cibiyoyin bincike da bayanai na likitanci, a matakin ƙasa da ƙasa. Wannan jami’a tana ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin ilimi, al’adu da kiwon lafiya a Iran.

Matsayinta a harkokin ilimi da bincike

Iran University of Medical Sciences ta zo a matsayi na 800-601 a tsarin ranking na Times. Hakazalika ta samu matsayi na 901-1000 a tsarin Shanghai.

Karatu a Iran University of Medical SciencesAsibitocin koyarwa

_ Hazrat Rasool (PBUH) Medical Research Educational Complex
_ Hazrat Fatemeh Plastic and Reconstructive Surgery Training Center
_ Rajaei Heart Training, Research and Treatment Center
_ Hazrat Ali Asghar Children’s Educational and Therapeutic Center
_ Shafa Yahyaian Orthopedic Training Center
_ Mustafa Khomeini educational and therapeutic center
_ Firouzabadi Educational and Therapeutic Center
_ Shahid Akbarabadi Obstetrics and Gynecology Training Center
_ Firouzgar Medical Education Center
_ Iran Psychiatry Training Center
_ Shahid Hashminejad Kidney and Urinary Tract Training Center
_ Martyr Motahari Accident and Burn Treatment Training Center

Asibitocin jinya

_ Asibitin Shohadae Haftome Tir
_ Asibitin Lolagar
_ Asibitin Shohadae Yaft Abad
_ Asibitin yara na Shahid Fahmideh
_ Asibitin Imam Sajjad na Shahryar
_ Asibtin Hazrat Fateme Rabet Karim
_ Asibitin Imam Hosein na Baharestan

Makarantu

_ School of Medicine
_ School of Traditional Medicine
_ School of Pharmacy
_ School of Health
_ School of Paramedicine
_ Faculty of Rehabilitation Sciences
_ School of Nursing and Midwifery
_ Faculty of Management and Medical Information
_ Faculty of Behavioral Sciences and Mental Health
_ Tehran Institute of Psychiatry
_ Faculty of Modern Medical Technologies

Harabar jami’a

Jami’ar na da kamfus ɗaya na ɗaliban waje wanda ya ƙunshi makarantu uku (makarantar medicine, dental, da pharmacy).

Cibiyoyi

_ Endocrine and Metabolism Research Institute
_ Five Senses Research Institute

Cibiyoyin Nazari

_ Cell and Molecular Research Center
_ Hospital Management Research Center
_ Research Institute for History of  Medicine, Islamic and Complementary Medicine
_ Razi Pharmaceutical Sciences Research Center
_ Otolaryngology and Head and Neck Research Center
_ Immunology Research Center
_ Ophthalmology Research Center
_ Nursing Care Research Center
_ Mental Health Research Center
_ Research Center for Rehabilitation
_  Neuroscience Research Center
_ Cardiac Intervention Research Center
_ Heart Electrophysiological Research Center
_ Heart Echocardiography Research Center
_ Shahid Rajaei Heart and Vascular Research Center
_ Medical Science Research Center
_ Research Center for Management Sciences and Health Economics
_ Endocrine and Metabolism Research Center
_ Minimally Invasive Surgery Research Center
_ Microbial Resistance Research Center
_ Occupational Health Research Center
_ Children’s Disease Research Center
_ Laboratory Science Research Center
_ Physiology Research Center
_ Skull Base Research Center
_ Burn Research Center
_ Iran Gastrointestinal and Liver Diseases Research Center
_ Occupational Medicine Research Center
_ Pathology and Cancer Research Center

Jadawalin kuɗin makarantar Iran University of Medical Sciences

  • kuɗin hostel na wannan jami’a su na farawa daga dala 100 zuwa dala 200 a kowane wata.

Kwasa-Kwasai

Jami’ar na karɓar ɗalibai a matakin associate degree, degree, masters, PhD, da kuma specialized doctorate, a sashen karatun rana da na dare a kwasa-kwasai kamar haka.
_ Medicine
_ Pharmacology
_ Nursing
_ Midwifery
_ Physiotherapy
_ Artificial Organs
_ Occupational Therapy
_ Speech Therapy
_ Audiology
_ Optometry
_ Management of Healthcare Services
_ Librarianship and Medical Branch
_ Health Information Technology
_ Laboratory Sciences
_ Radiology
_ Surgery Room
_ Anesthesia
_ General Hygiene
_ Health Professional
_ Environmental Health

Kwasa-Kwasan Iran University of Medical Sciences a matakin degree

Kwasa-Kwasan Iran University of Medical Sciences a matakin masters

Kwasa-Kwasan Iran University of Medical Sciences a matakin PhD

Kwasa-Kwasan Iran University of Medical SciencesAbubuwan More Rayuwa

Iran University of Medical Sciences ta yi tanadin wasu kayan aiki domin sauƙaƙe wa ɗalibai yanayin karatu, abubuwa kamar laburare, filin shan iska mai haki, zauren taruka, ginin hedikwata, banki, cibiyar kula da ƙirƙire-ƙirƙire da cibiyar nazari ta gani da ido, ayyukan kiwon lafiya, likitan haƙori, magunguna, bada shawarwari ga ɗalibai kyauta.

Kayan aikin Iran University of Medical SciencesAbubuwan Alfahari

_Samar da ayyukan kiwon lafiya da magani
_ Yaye ɗalibai da dama a fannoni daban-daban na likitanci
_ Shirya tarukan ƙarawa juna sani da taruka daban-daban a fagen ilimin likitanci
_ Fassara da wallafa litattafai da sauran wallafe-wallafe a fannonin likitanci daban-daban
_ Gabatar da ayyukan karatu da magani a fannoni daban-daban na likitanci
_ Ƙarfafa alaƙa da jami’o’in cikin gida da na waje ta hanyar kwangilolin al’adu da na ilimi
_ Rekod ɗin wallafa maƙala daga dukan membobin tsangayar ilimi a hukumar kiwon lafiya

Yanayin muhallin da Iran University of Medical Sciences take

Jami’ar na nan a titin Yasmi na garin Tehran, kuma tana kusa da muhimman wurare kamar asibitin Khatamal Anbiya (s), Bahin Bazar, Fata Police, asibitin Shahid Motahhari, ginin ƙungiyar matasa ta Red Crescent, school of nursing ta jami’ar, da kuma hedikwatar bayanai ta Naja.

Adireshin jami’a

Adireshi: Tehran, babbar hanyar Hemmat, kusa da Burj Milad, Iran University of Medical Sciences


  1. Wasu irin takardu ake buƙata don neman admission a Iran University of Medical Sciences?
    Passport, hoto, transcripts, certificate, resume, motivation letter, recommendation letter.
  2. Ko ana yin kwas ɗin MD da MBBS a wannan jami’a?
    Eh, ana yin duka biyu, sannan ana karɓar ɗaliban waje a waɗannan kwasa-kwasan.
  3. Minene shafin Ma’aikatar Ilimi?
    https://www.msrt.ir/en

Loading

Related Posts
Leave a Reply

Your email address will not be published.Required fields are marked *