Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu Shahid Madani University

Karatu Shahid Madani University

Loading

Azerbaijan Shahid Madani University tana ɗaya daga cikin jami’o’in da ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimi. A wannan rubutun mun yi nufin kawo muku sharhi dangane da karatu a Shahid Madani University, tarihinta, ranking, kwasa-kwasan da ake yi a cikinta, makarantunta, kuɗin makaranta, da sauransu. Yanke hukunci akan inda zamu yi karatu abu ne mai matuƙar muhimmanci saboda hakan zai taka muhimmiyar rawa wurin gina gobenmu.

Gabatarwa

Da farko Azerbaijan Shahid Madani University ta fara gudanar da ayyukanta ne da sunan Tarbiat Moallem University Tabriz a shekarar 1988. A shekarar 2001 yanayin wannan jami’ar ya canja sakamakon canjawar hadafinta, daga ƙarshe a shekarar 2012 aka bata sabon suna; Azerbaijan Shahid Madani University kuma ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na koyarwa da bincike-bincike a matsayin jami’a ta biyu a gabacin Azerbaijan
Akwai ɗalibai 6707, malamai 399, da mambobin kwamitin ilimi 270 a Shahid Madani University. Bincike ya nuna cewa, zuwa yanzu wannan jami’ar ta samu nasarar wallafa maƙala 3707 na ilimi a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida [wanda suka haɗa da mujalla 1179 da maƙalar taro guda 2528], da kuma maƙaloli 3153 karɓaɓɓu a matakin ƙasa da ƙasa. Shahid Madani University ta shirya taruka 23 zuwa yanzu, kuma ita ce mamallakiya kuma mawallafiyar mujalla 4 na musamman.

Martabar Shahid Madani University

Tsarin ranking na Times ɗaya ne daga cikin fitattun tsarukan ranking ɗin jami’o’i da cibiyoyin koyarwa na duniya da nufin kwatantawa da daraja makarantu, da aka wallafa karon farko a shekarar 2004 tare da haɗin gwiwar tsarin QS. Wannan haɗin gwiwar ya ci gaba har zuwa shekarar 2010. Daga ƙarshe bayan yankewar wannan haɗin gwiwar, Times sun ci gaba da aiki tare da Reuters. Sakamakon da wannan cibiyar (Times) ta fitar a shekarar 2023 ya nuna cewa, Azerbaijan Shahid Madani University ta samu matsayi na 601 zuwa 800 a tsakanin jami’o’in duniya.

Karatu Shahid Madani UniversityMakarantu

_Makarantar Basic Sciences
_Makarantar Engineering
_Faculty of Information Technology and Computer Engineering
_School of Agriculture
_Faculty of Literature and Humanities
_Faculty of Education and Psychology
_Faculty of Theology

Cibiyoyin Bincike

_Molecular Simulation Laboratory
_Institute of Applied Studies of Power Systems
_Psychological – Social Health Research Institute
_Tabavar Smart Networks Research Laboratory

 Kuɗin Makaranta 

Kwasa-Kwasai

Kwasa-Kwasan da ake yi a Shahid Madani University sun haɗa da:
_Persian Language and Literature
_Contemporary Persian Literature
_English Language Teaching
_English Language and Literature
_English Language Translation
_Arabic Language and Literature
_Arabic Language Translator
_Mystical Literature
_Ghanaian Literature
_Islamic Theology and Teachings (Islamic philosophy and theology/religions and mysticism/Quran and hadith sciences)
_Islamic Word
_Philosophy of Religion
_Pure Mathematics
_Applied Mathematics
_Physics
_Phytochemistry
_Biology (Cell and Molecular Sciences/ Plant Physiology/ Developmental Cell)
_Civil Engineering (structure/earthquake/soil/water)
_Electric Engineering
_Mechanical Engineering
_Computer Engineering
_Information Technology
__Agricultural Engineering
_Psychological
_Physiology of Physical Activity and Well-Being
_Applied Sports Physiology
_Information Science and Epistemology
_Research Training
_Curriculum
_Agricultural Entomology
_Agricultural Biotechnology
_Da sauransu…
Domin samun cikakken list ɗin kwasa-kwasai da matakan karatun da kuke buƙata, ku sauke wannan fayil.

Kwasa-Kwasan Shahid Madani University

Kwasa-Kwasan Shahid Madani University

Ababen More Rayuwa 

Laburaren Hostel: Domin ƙarfafa karatu da samarwa ɗalibai damar sarrafa lokutan faragarsu, jami’ar ta samarwa ɗalibai da laburare 3 a hostel 3 (kowane hostel laburare 1) a shekarar 2014. Litattafan da suke cikin waɗannan laburaren basu taƙaita a darusan aji kawai ba, sannan alhakin tafiyarda waɗannan ɗakunan karatu yana wuyan ɗalibai, yayinda tallafi da alhakin sayen litattafai yake wuyan babban laburaren makarantar.
Ɗakunan karatu: A cikin laburarukan Azerbaijan Shahid Madani University, akwai ɗakunan karatu biyar waɗanda zasu iya ɗaukar kusan mutum a jimlace. A ranakun jarabawa, ɗakunan karatu suna buɗe har zuwa wuraren tsakiyar dare.
Akwai sashen reference guda biyu a laburarukan jami’ar Shahid Madani, ɗaya a na cikin babban laburaren jami’ar, ɗayan kuma na cikin makarantar adabi (faculty of literature). Hadafin waɗannan sassan biyu shi ne samar da sabbin references. Suna ɗauke da fiye da rubutattun reference guda 9114 da suka haɗa da littafai, tarihohi, kayan geography, ƙamusoshi, Insakulofdiya, da sauransu na gama gari da kuma waɗanda suka shafi keɓantattun fannoni, musamman fannin Human Sciences, Theology, Engineering da Basic Sciences. Ana amfani da litattafan reference iya cikin laburare kawai (ba’a fita dashi waje).
Hostel: Duka hostel ɗin Shahid Madani University suna cikin harabar jami’ar. kuma duka  baƙin ɗalibai (daga garuruwan Tabriz, Khosrow, Sahand, Azar Shahr, Gogan, da sauran garuruwa) zasu iya amfani da hostel.
Ɗaliban matakin PhD a ɗakunan mutum biyu, ɗaliban digiri a ɗakunan mutum 4, ɗaliban Masters kuma a suit mai ɗaukar mutum 10 wanda ya haɗa da ɗakunan mutane 6 da na mutum 4.

Kayan aikin Shahid Madani UniversityYanayin Wuri

Shahid Madani University na cikin Azerbaijan ta gabas, garin Azarshahr babbar hanyar Tabriz. Jami’ar tana kusa da wurare kamar Faculty of Educational Sciences and Psychology, tashar bus ta Shahid Madani University, Qannari Mobile Cafe, da kuma General Parking. Jami’a ta farko kuma ɗaya tilo da aka alaƙanta ma jirgin ƙasa a Iran.

Adireshin Shahid Madani University

Adireshi Shahid Madani University, Marageh, Babbar hanyar Tabriz mai nisan kilomita 35, Tabriz, Azerbaijan ta gabas, Iran.


Tambayoyin da ake yawan yi game da Shahid Madani University

  1. Ya ake biyan kuɗin makaranta a wannan jami’ar?
    A wannan jami’ar ana karbar toman (kuɗin Iran) ne a matsayin kuɗin makaranta.

Loading

Related Posts
Leave a Reply

Your email address will not be published.Required fields are marked *