Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Yasouj

Karatu a Yasouj

Loading

Garin Yasouj yana tsakiyar lardin Kuhgiluyeh o Boyer-Ahmad, a ƙasan duwatsun Zagros da Dana, tsayin 1870 daga saman teku. Hadafinmu na gabatar muku da wannan rubutu mai taken ‘Karatu a Yasouj’ shi ne gabatarwa da kuma sharhi a kan yanayin al’adu, karatu, iska, yawon buɗe ido, da sauran bayanai game da wannan gari.

Karatu a Yasouj

Yasouj

Yasouj (ma’ana muhallin da furen yas ke fita da yawa) saboda yanayinta mai daɗi, a na yi mata kirari da sunan babban birnin ɗabi’a na Iran. Yaren mutanen Yasouj shi ne Leri, su lerawa ne na asali kuma ‘yan shi’a. A ƙidayen shekarar 2016, akwai mutane 134532 a wannan gari. Garin Boyer-Ahmad na da yankuna 4 masu suna Markazi, Drohan, Margono Lorab, 2 Shahr, da 13 Dahestan. Garin Yasouj na cikin yankin tekun Mediterrenean da ke da matsanancin yanayi, inda matsakaicin mizanin ruwan sama da ke sauka duk shekara a wannan gari ya kai milimita 865, kuma yana ɗaya daga cikin garuruwan Iran da suka fi samun ruwan sama bayan garin Rasht.
Saboda yawan ruwan sama da ake samu a wannan yanki da kuma ciyayi masu kyau, kiwon dabbobi da noma su ne babban ginshikin tattalin arzikin garin.Tuntuka, darduma, katifu, madubai, tufafin gida kala-kala, da sauransu sune mafi kyawun zaɓi na yin tsaraba daga wannan gari.
Kamar sauran yankuna na Iran, garin Yasouj shi ma yana da nasa al’adu na musamman. Ɗimbin tarihi na wannan birni ya sanya garin mallakar al’adun gargajiya masu kyau. Ɗaya daga cikin bukukuwan da suka keɓanci wannan gari na Yasouj shi ne Pandshekani da ake yi cikin Nouruz. A wannan bukin mutane su na zuwa ziyarar manya da waɗanda suke cikin juyayi a danginsu tare da kai musu kyautar baƙaƙen tufafi.
Bukin chalegaram Kenon shi ma ɗaya ne daga cikin al’adun mutanen garin Yasouj inda mutane ke dafa abinci kala-kala na gargajiya kwana ɗaya kafin sabuwar shekara. Mutane sun yi imanin cewa ta hanyar ɗumama murhunsu a wannan lokaci, za su samu kwanciyar hankali da kuma albarka a abincinsu a shekara sabuwa.

Cikakken bayani a kan garin Yasouj

Karatu

A garin Yasouj akwai cibiyoyin ilimi da jami’o’i guda 16, ɗauke da kimanin ɗalibai 21797 da malamai 888. Bincike ya nuna cewa akwai maƙalar ilimi guda 15160 da suka ƙunshi maƙalar mujalla 2029 da maƙalar taro guda 8111 da a ka buga a tarukan ilimi na cikin gida, akwai kuma maƙalar ƙasa da ƙasa guda 2029 da suka fito daga waɗannan cibiyoyi. Ɗaya daga cikin ingantattun cibiyoyin koyarwa na wannan garin ita ce Jami’ar Yasouj (Yasouj University). Domin samun ƙarin bayani za ku iya ziyartar wannan rubutu mai taken Karatu a Yasouj University.

Jami'o'in Yasouj

Nishaɗi da wuraren yawon buɗe ido

Yasouj na daga cikin garuruwan Iran masu burgewa wanda dalilin kasantuwar koguna biyu (kogin Bashar da Mehrian), waterfall, dam ɗin Shah Qasim, idon ruwa daban-daban, da dazukan Balot a cikin wannan gari, ya zama ɗaya daga cikin manyan wuraren yawon buɗe ido wanda kowane mai yawon buɗe ido mai sha’awar ɗabi’a zai so zuwa a cikin tafiye-tafiyensa.
_ Waterfall
_ Dana Mountain Range
_ Kogin Bashar
_ Tal Khosrow
_ Kakan Village
_ Tang Ganjaei
_ Dena ski Resort
_ Forest Park
_ Tang Mehrian
_ Morpise Plain
_ Ƙoramar Morzard
_ Shah Qasim Dam
_ Gidan Tarihi
_ Qole Pazan
_ Khungah copper Cave
_ Koh Ab
_ Imamzade Abdullah
_ Tal Mohrei
_Da sauransu…

Yawon buɗe ido a Yasouj

Cibiyoyin magani da asibitoci

_ Shahid Mofateh Clinic
_ Shohadae Gomnam Hospital
_ Farhangian Clinic
_ Shahid Beheshti Hospital
_ Imam Jafar Sadiq (AS) Clinic
_ Sadra Clinic
_Shahid Rajaei Hospital
_ Salman Hospital
_ Imam Sajjad (AS) Hospital
_ Omid Hospital
_Da sauransu…

Hotal Hotal na garin Yasouj

_ Azadi Hotel
_ Aram Hotel
_ Dal Dana Hotel
_ Jahangardi Hotel
_ Bagheri Olympic Hotel
_ Parsian Hotel
_Da sauransu…

Ɗakunan Karatu

_ Imam Khomeini Public Library
_ Imam Ali (AS) Public Library
_ Central Library
_ Ostad Mohammad Bahman Begi Library
_ Shohadae Ali Abad Central Library
_ Fateme Zahra (AS) Library
_ Shahid Beheshti Public Library, Margon
_Da sauransu…

Cibiyoyin Kasuwanci

_ Atlas Commercial Center
_ Bazar Jom’e Sharaf Abad
_ Tus Commercial Complex
_ Pasaj Mellat
_ Pasaj Omid
_Cherry Shopping Center
_Da sauransu…

Gidajen cin abinci

_ Lian Traditional Restaurant
_ Kebabi 4 Loghme
_ Gol Maryam Restaurant
_ Yaghoush Traditional Restaurant
_ Bajnaq Traditional Restaurant
_ Shandiz Restaurant
_ Bakhtyari Restaurant
_ Mobin Restaurant
_ Chelo kebabie Golpaygani
_ Zima’s Dining Room & Daizi House
_ Kolbeh Restaurant
_Da sauransu…

Related Posts
Leave a Reply