Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Azad University Najafabad

Karatu a Azad University Najafabad

Loading

Isfahan [gari na uku mafi yawan jama’a a Iran] gari ne mai ɗimbin tarihi da ke tsakiyar Iran, kudu ga Tehran. A wannan gari jami’ar Azad Najafabad take. Ku kasance tare da mu idan kuna cikin mutanen da su ke da ra’ayin karatu a wannan jami’ar Azad ta Najafabad.

Gabatarwa 

Azad University Najafabad, ɗaya ce daga jami’o’in Azad wadda ke garin Najafabad ta Isfahan, ita ce mafi girma, mafi tarihi, kuma mafi shahara a cikin rassan jami’o’in Azad na yankin Isfahan. Wannan jami’a ta fara aiki ne a ranar 4 ga watan January na  shekarar 1986 a ƙarƙashin shugabancin Sayyed Muhammad Amiri [na tsawon shekara 16], an kafa ta ne da kyautar jari daga Shahid Sayyed Muhammad Reza Mirdamadi, tare da tallafawar wasu daga cikin dattawan garin irin su Ayatullah Ezdi, tsohon limamin masallacin juma’a na garin Najafabad.
Yanzu haka jami’ar na da ɗalibai 24702, da malamai 487. Binciken da aka gudanar ya nuna cewa a wannan jami’a, an wallafa maƙalar ilimi guda 10953 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida, hakazalika an wallafa maƙala 3033 a matakin ƙasa da ƙasa a wannan jami’a. Har ila yau, jami’ar ta mallaki lambar yabo sannan kuma ita ce mawallafiyar mujalla 6 na musamman. Jami’ar Azad Najafabad ta karɓi baƙuncin manyan taruka guda 31.

Martabar Azad Najafabad University

Tsarin ranking na Times ɗaya ne daga cikin tsarukan martaba jami’o’i mafi shahara a duniya wanda bisa dogaro da bayanan da wannan tsarin ya fitar a shekarar 2022, jami’o’in Iran 58 ne su ka samu shiga sahun fitattun jami’o’i 1662 na duniya, inda jami’ar Azad ta Najafabad ta kasance ɗaya tilo a kaf jami’o’in Azad wadda ta samu shiga sahun waɗannan jami’o’in. 

Karatu a Azad Najafabad UniversityMakarantu

_Faculty of Electrical Engineering [ɗauke da membobi 60, laboratory 43, da workshop 7]
_Faculty of Computer Engineering [Membobi 36]
_Technical and Engineering College [Membobi 58, laboratory 34, workshop 30]
_Faculty of Materials Engineering [membobi 35, laboratory 14]
_Faculty of Civil Engineering [membobi 30]
_Faculty of Medical Sciences [Membobi 52, laboratory 10]
_Faculty of Art, Architecture and Urban Planning [membobi 17, laboratory 5, workshop 26]
_Faculty of Humanities [membobi 64]
_College of Nursing and Midwifery [Membobi 22, laboratory 9]
_Faculty of Law, Theology and Islamic Studies [Membobi 19]

Kuɗin Makarantar Azad University Najafabad

Kwasa-Kwasan Azad University Najafabad

_Mining Engineering
_Electric Engineering
_Computer Engineering
_Chemical Engineering
_Civil Engineering
_Mechanical Engineering
_Aerospace Engineering
_Nuclear Engineering
_Textile Engineering
_Biomedical Engineering
_ Optics and Laser Engineering
_General Medicine
_Health Sciences
_Surgery Room
_Midwifery
_Nursing
_Law
_Industrial Management
_Tourism Management
_Physical Education
_Persian Language and Literature
_History of Islam
_Jurisprudence and Principles of Islamic Law
_Business Management
_Nuclear Physics
_Statistics
_Biochemistry
_Cellular and Molecular Biology
_History of Islam
_Da sauransu…
Ku sauke wannan fayil na ƙasa domin samun cikakken list na kwasa-kwasai da matakan karatun wannan jami’a.

Kwasa-Kwasan Azad University Najafabad

Kwasa-Kwasan Azad University Najafabad

Cibiyoyin bincike da Nazari

_Advanced Materials Research Institute
_Data Fog Research Center
_Research Center for New Manufacturing Technologies
_Digital Processing and Machine Vision Research Center
_Tourism Research Center
_Research Center for the Development of Nursing and Midwifery Sciences
_Smart Microgrids Research Center
_Sports Medicine Research Center
_New Horizons Research Center in Architecture and Urban Planning
_Human Environment Research Center and Sustainable Development
_Aerospace and Energy Conversion Research Center
_Clinical Science Development Research Center
_Medical Equipment Manufacturing Growth Center

Ɗakin Taro

_Ɗakin Taro na Shahid Hojaji mai hawa biyu a wuri mai faɗin murabba’in mita 425, yana ɗaukar mutum 1,350
_Ɗakin Taro na Shahid Chamran mai girman murabba’in mita 1000, yana ɗaukar mutum 750
_Ɗakin Taro na Shahid Mirdamadi mai girman murabba’in mita 500, yana ɗaukar mutum 250
_Ɗakin Taron Avini mai girman murabba’in mita 250, yana ɗaukar mutum 170
_Zauren Babban Laburare mai girman murabba’in mita 320, yana ɗaukar mutum 200
_Zauren Ferdowsi mai girman murabba’in mita 308, yana ɗaukar mutum 130
_Zauren Sheikh Bahaei
_Zauren Moawanat Sama mai girman murabba’in mita 350, yana ɗaukar mutum 100

Abubuwan Alfahari

_Ficen da ɗaliban da suka kammala karatun Civil Engineering daga wannan jami’a suka yi, da nasarar da suka samu, da karɓuwa a jami’o’in ciki da waje Iran
_Samun shigar ɗaliban Civil Engineering da wannan makaranta ta yaye cikin cibiyoyin nazari da zartarwa na ciki da wajen Iran
_Samar da sababbin ƙirƙire-ƙirƙire
_Gudanar da ayyukan bincike tare da cibiyoyin gwamnati
_Matsayi na farko a ƙididdiga da maƙalolin jami’o’in Azad da suke yankin Isfahan, a  ISI
_Mallakar wasu mujallun ilimi waɗanda Sazeman Markazi ta tantance
_Lashe matsayi na farko a bukin baje kolin nasarorin bincike karo na 6
_Lashe matsayi na farko a gasar wallafe-wallafen maƙala ta ɗaliban Human Rights a sashe na musamman na bukin mawallafa na Iran, inda suka gabatar da maƙala mai taken ‘Musulunci da Sulhu’
_Wallafa kimanin karɓaɓɓun mujallu guda1800 na cikin gida
_Wallafa maƙala 4950 a matakin ƙasa da ƙasa
_Aiwatar da ayyukan ƙarin karatu 113 da  kuɗi sama da Riyal biliyan 60
_Samar da lasisi ga cibiyoyin bincike guda 14 daga Sazman Markazi ta Islamic Azad University
_Samar da lasisn ga Cibiyar Nazarin Abubuwan Ci gaba, daga ma’aikatar Ilimi, Bincike da Fasaha
_Su suka fara lashe gasar design ta yankin Asia a 2018, inda suka yi designing kujerar ‘Ergonomic Bench of Wave and Rock’
_Lambobin zinare 4 a gasar IDA ta Amurka saboda design ɗinsu na ‘Ergonomic Bench of Wave and Rock’
_Ƙera na’urar rarraba kayan aiki ta ‘Methadone Mechanized Dispensing Device’ karon farko a duniya
_Suna kan aiwatar da ayyukan bincike 323
_Da sauransu…

Ababen More Rayuwa

_Tana da rukunin wuraren kwanan ɗalibai mata da maza, ɗauke da dukkan kayan amfani da abubuwan more rayuwa (ɗakin karatu, intanet mai ƙarfi, da sauransu)
_Samarwa ɗalibai da motar zirga-zirga
_Tana da cibiyar shawara da ayyukan da suka shafi halayyar ɗan adam domin ɗalibai
_Wuraren kwanan ɗalibai za su iya ɗauke kimanin ɗalibai 1400
_
_Kayan wasanni da suka haɗa da filin wasa mai grass carpet, filayen wasannin Volleyball, Basketball, Handball, wurin gina jiki, power house
_Da sauransu…

Kayan aikin Azad University NajafabadYanayin Wuri

Azad University Najafabad (jami’a kuma cibiyar koyarwa ta gaba da sakandare) na cikin lardin Isfahan, garin Najafabad, a titin Molavi. Ta fuskar yanayin wuri kuma, jami’ar na kusa da Self Service na Daneshga, da kuma ATM na Bank Melli.

Adireshin Azad University Najafabad

Adireshi: Azad University Najafabad, Titin Daneshga, Najafabad, Isfahan


Tambayoyin da ake yi game da karatu a Azad University Najafabad

  1. Da wane yare ake karatu a wannan jami’a?
    Da farsi ake duka karatuttukan wannan jami’a, hakan yana nufin cewa ɗalibai masu son karatu a wannna jami’a lazim ne su fara shiga azuzuwan koyon yaren farsi.
  2. Ko akwai buƙatar bizar karatu domin yin jarabawa?
    A’a

Loading

Related Posts
Leave a Reply

Your email address will not be published.Required fields are marked *