Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Shiraz University

Karatu a Shiraz University

Loading

Ɗaya daga cikin dalilan zuwa ƙasar Iran shi ne karatu a Iran. Jami’ar Shiraz tana sahun gaba a cika sharuɗan jami’o’in ƙasa da ƙasa, jami’ar tana cikin garin Shiraz. A kowace shekara wannan jami’a na karbar ɗalibai daga ko’ina cikin duniya, ciki harda daliban Iraƙi. Saboda haka, ga ɗaliban da ke son yin Karatu a Shiraz University, karanta wannan rubutun da kuma samun bayanai game da jami’ar shiraz abu ne mai matuƙar muhimmanci.


Gabatarwa


Jami’ar Shiraz na ɗaya daga cikin tsofaffin jami’o’in Iran. An ƙaddamar da wannan jami’ar ne a shekarar 1946. A lokacin, an kafa wannan jami’a ne a matsayin makarantar kiwon lafiya da nufin horar da ƙwararru a ilimin likitanci. Daga baya a hankali aka dinga ƙara sauran kwasa-kwasan karatu da kwalejoji a wannan makarantar. Pahlavi University, shi ne sunan wannan jami’ar kafin juyin juya hali. Daga ƙarshe bayan juyin juya hali aka canja sunanta zuwa Shiraz University.

Jami’ar Shiraz, mai tarihin fiye da rabin ƙarni, na ɗaya daga cikin manyan jami’o’i kuma masu muhimmanci na Iran, kuma ana kallon wannan jami’ar a matsayin tushen bincike-bincike na ƙasar. Tana da mambomi 670 na sassan karatu da kuma fiye da ɗalibai 16,0000. Ana yin kwasa-kwasan digiri 80, na masters 183, 102 na PhD, da kuma 1 na bayan PhD a wannan jami’ar. A matsayinta na babbar jami’a, Jami’ar Shiraz tana da alhakin horar da ƙwararrun malamai don gudanar da bincike da kuma manyan cibiyoyin ilimi a kasar. A halin yanzu jami’ar Shiraz tana da makarantu 16 da kuma babbar cibiyar koyarwa guda ɗaya kuma nan gaba kaɗan za’a buɗe wasu makarantun.
A matsayinta na uwar jami’a, Jami’ar Shiraz ta samu nasara aikinta na kafa jami’o’in Hormozgan, Bushehr, Yasouj, jami’ar masana’antu ta Shiraz, Babbar cibiyar koyarwa ta Kazeroon, da kuma kwalejin noma da albarkatun ƙasa na Darab kuma a halin yanzu, duka waɗannan manyan cibiyoyin ilimi na cigaba da gudanar da ayyukansu da kansu. Har ila yau jami’ar shiraz ita ce keda alhakin sa ido da tantance jami’o’i da manyan makarantun gaba da sakandare guda 166 a lardin Fars.

Maƙaloli 

Domin yin karatu a wannan jami’ar, yana da kyau ku san cewa jami’ar Shiraz ta wallafa maƙaloli da dama a matakin cikin ƙasa da kuma waje. Jami’ar Shiraz ta wallafa maƙala 21801 na cikin gida da kuma maƙalolin ISI guda 24087.

Hakazalika, wallafe-wallafen ilimin kimiyya na musamman da mujalloli da ake bugawa a jami’o’i suna daga cikin amintattun madogara da ake amfani da su wurin buga sabbin bayanan ilimin kimiyya. Bayanan da aka tattara a ma’ajin bayanai na maujallun Iran, ya nuna cewa Jami’ar Shiraz ce mawallafiyar mujallun kimiyya ashirin da ɗaya.

Martabar Jami’a

Bisa sabon rahoton da ma’aikatar ilimi ta Iran ta fitar, Jami’ar Shiraz na matsayi na 68 a jerin jami’o’in ƙasar Iran. Har ila yau wannan jami’a ta samu matsayi na 6 a tsakankanin jami’o’in da ba na likitanci ba.

Ya kamata ku sani cewa Jami’ar Shiraz tana da matsayi na 751 a  tsarin QS da kuma matsayi na 5 a jami’o’in Iran sannan tana da mastayin jami’a ta biyu mafi inganci a Iran kuma uwar jami’o’i bayan Jami’ar Tehran, shima wannan muhimmin abu ne da ya kamata ku sani game da Jami’ar Shiraz.

Karatu a Shiraz UniversityMakarantu

• Sashen Veterinary Medicine
• Sashen Science
• Sashen Materials Engineering and Construction
• Sashen Literature and Humanities
•Faculty of Economics, Management and Social Sciences
• Faculty of Law and Political Science
• Faculty of Theology and Islamic Studies
• Sashen Agriculture and Natural Resources na Darab
• Sashen Modern technologies
• Sashen Arts and Architecture
•Sashen Mechanical Engineering

Ginshiƙan Kimiyya

• Scientific pole of optical electronic switching devices
•The scientific pole of reproductive studies in high-yielding dairy cows
• Scientific pole of Persian cultural and literary researches
Scientific pole of plant virology
• Scientific pole of water management in the farm
•Scientific pole of studies of natural antimicrobial compounds
•Scientific pole of environmental geology risks
•Scientific Gas Pole

Kwasa-kwasan masters a Shiraz University

Kwasa-kwasan PhD na Shiraz University

Kwasa-kwasan karatu a Shiraz UniversityAbubuwan more rayuwa

Majalisar al’adu da walwala na jami’ar

An gina wannan wuri ne a hamsinonin ƙirgen shmasiyya kuma manufar gina wannan babban wurin more al’adu shi ne gudanar da bukukuwa da taruka mabanbanta, abubuwan da suka shafi wasanni, shaƙatawa, da sauransu. Saboda wannan, an gina wurare kamar haka:
Ɗakin taro mai ɗaukar mutum 550, ɗakin bukukuwa mai ɗaukar kusan mutum 250, rukunin ɗakunan taro, rukunin wuraren cin abinci da masaukan baƙi, ɗakunan wasanni, filin wasan tennis da squash, da sauransu…

Mataimakin mai kula da sashen al’adu da zamantakewa na jami’ar, don haɓaka filin tunani, tattaunawa da gabatar da batutuwa daban-daban a cikin harabar jami’ar, ya goyi bayan ƙaddamar da ɗakin yaɗa labarai na jami’ar domin bunƙasa ƙima da ingancin buga mujllolin jami’ar akan abubuwan da suka shafi al’adu, zamantakewa, siyasa, tattalin arziki, addini, kimiyya, fasaha, adabi, wasanni, da kuma fagage na musamman, a cikin tsarin dokoki da ƙa’idojin su.
Jami’ar Shiraz tana da sama da wallafe-wallafe 150 masu lasisi a sassa kamar haka: Al’adu, zamantakewa, siyasa, fasaha, tattalin arziki, da adabi. da kuma fiye da wallafe-wallafe 107 wanda ake bugawa duk bayan wata uku, ko duk wata biyu, ko wata-wata, ko mako-mako, lokaci-lokaci, sati-sati ko bugu na musamman.

Kuɗin makarantar Shiraz University

Kuɗin Makaranta 

A Jami’ar Shiraz, dole ne ɗaliban da ba ‘yan ƙasar Iran ba su fara biyan dala 150 a matakin masters, dala 200 a matakin PhD kafin su fara hada-hadar yin rajista.

Ɗaliban Jami’ar Shiraz zasu iya amfani da wurin kwanan ɗalibai ta hanyar biyan dala 640 a duk shekara,  sannan zasu iya morar kayan abinci da abincin jami’ar bayan sun biya dala 560 duk shekara.

Idan ɗaliban waje basu samu makin da ake buƙata ba a jarabawar gwajin gogewa a yaren farsi yayin yin rajista, dole sai sun shiga ajin koyon yaren farsi a jami’ar Shiraz. Kuɗin koyon farsi a zangon farko na shekarar karatu dala 850 ne.

Kwas ɗin KaratuMatakin Karatutsawon lokacin karatuKuɗin makaranta (na shekara)
Kwasa-kwasan Literature da HumanityDigirin Farko (BSc)Shekara 4$980
Masters (MSc)Shekara 2$1120
PhDShekara 3 zuwa 4$1540
Sauran kwasa-kwasaiDigirin Farko (BSc)Shekara 4$1260
Masters (MSc)Shekara 2$1400
PhDShekara 3 zuwa 4$1960

Laburare 

Tarihin kafuwar babban laburare da taskar Jami’ar Shiraz ya samo asali ne daga shekararn1985-1986. Kafin wannan lokacin ana ɗaukar wannan laburare a matsayin ɓangare na ɗakin karatun sashen kimiyya (Laburaren Mollasadra). Tsawon wannan shekarun an ɗauke tarin litattafan da suke cikin wannan laburare wadanda suka shafi humanities, social sciences, da ilimin tarbiyya aka mayar da su zuwa laburaren Mirza Shirazi wanda daga baya aka canja sunansa zuwa Babban Laburare kuma taskar jami’ar. Ginin yanzu na wannan babban laburare mai hawa uku yana da girman kimanin murabba’in mita 11,000. Hawa na farko ya keɓanci ɗakin karatu, hawa na biyu kuma domin ajiye madogarai, tarin litattafan farsi, na larabci, litattafan latin, bayanan nazari akan yawan jama’a, ilimin tarbiyya, teburin lamuni, da kuma teburin bita. Shi kuma hawa na uku yana ɗauke da wallafe-wallafen lokaci-lokaci, projects, kundin bayanai, sashen odar maƙala, tarin nazari akan Iran na Farfesa Pop, zane-zanen Ghadir da Amin, tarin gudumawar Abbaspour, da kuma tarin abubuwan da suka shafi yara da matasa,da sassan fasaha na laburaren. A halin yanzu, Babban Laburare da Taskar killace rubututtukan Jami’ar Shiraz yana kan ƙoƙari wajen ganin cewa ɗalibai, malamai, da sauran masu amfani da shi sun samu biyan buƙatunsu aka samun bayanai ta hanyar tattarawa da samar musu da kayan aiki da na lantarki a fagagen Social Sciences, Humanities, da Moral Education. Bayan Babban Laburare na Jami’ar Shiraz wanda shine laburare mafi girma a jami’ar, akwai wasu ƙarin laburare guda 9 a wannan jami’a.

Kayan aikin Shiraz University

Adireshin Jami’ar 

Adireshi: Titin Jamhoori Islami, Hozeh Modiriyat Daneshgahe Shiraz, Shiraz.


Tambayoyin da ake yawan yi akan Shiraz University

  1. Da wane yare ake karatu a Shiraz University?
    Da yaren farsi ake gabatarda dukan karatukan da akeyi a wannan jami’a kuma dole ne ɗaliban da ba Iraniyawa ba ya zama suna da takardar shaidar kammala koyon farsi.
  2. Me ake buƙata don fassara takardun kammala karatu a Jami’ar Shiraz? 
    A Jami’ar Shiraz ana tantance takardu a website ɗin Sajjad ne kawai idan ɗalibi yana cikin karatu kuma yayi zaɓen darussa.
  3. Shin salon karatun PhD a University of Shiraz na bincike ne?
    Eh, haka ne a wasu kwas ɗin. Amma a wasu kwas irin Educational Psychology ba haka bane.

[neshan-map id=”21″]

Related Posts
Leave a Reply