Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Shahid Beheshti University

Karatu a Shahid Beheshti University

Loading

Ɗaya daga shahararrun cibiyoyin koyarwa na Iran, wadda keda matsayin ilimi na a zo a gani, ita ce Shahid Beheshti University (Jami’ar Shahid Beheshti) wadda zamu yi bayani game da yanayin karatunta, yanayin karɓar ɗalibai, da sauran bayanan da suka danganceta a wannan rubutu namu.

Gabatarwa

Shahid Beheshti University, jami’ar gwamnati ce dake garin Tehran (Birnin Tarayya na ƙasar Iran) wadda aka assasa a shekarar 1959 da sunan; Iran Melli University, bisa umarnin Muhammad Reza Pahlavi. A halin yanzu, wannan jami’a nada ɗalibai 17000, malamai 1290, da mambobin tsangayar ilimi 900.
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa, wannan jami’ar ta wallafa maƙalar ilimi guda 26837 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida (maƙalar mujalla 10640 da maƙalar taro 16197), da maƙala 53374 a matakin ƙasa da ƙasa. Jami’ar Shahid Beheshti ta wallafa mujalla 40 na musamman, sannan an gudanar da taruka 49 a cikin wannan Jami’a.

Martabar Shahid Beheshti University

Jami’ar Shahid Beheshti, ta samu matsayi na 901 – 1000 a tsarin ranking na Shanghai wanda hakan ya nuna tana matsayi guda da Jami’ar Shiraz da Jami’ar Tabriz a ilmance. Hakazalika a tsarin ranking na Times, matsayin Jami’ar Shahid Beheshti ya ɗaga sama idan an kwatanta da matsayinta na shekarar da ta gabata, inda yanzu tana matsayi na 601 – 800.

Karatu a Jami'ar Shahid BeheshtiMakarantu

_Faculty of Literature and Humanities
_Faculty of Theology and Religions
_School of Law
_Faculty of Economics and Political Sciences
_Faculty of Management and Accounting
_Faculty of Education and Psychology
_Faculty of Sports and Health Sciences
_Faculty of Biological Sciences and Technology
_Faculty of Earth Sciences
_Faculty of Mathematical Sciences
_Faculty of Physics
_Faculty of Chemical and Petroleum Sciences
_Faculty of Architecture and Urban Planning
_College of New Technologies and Aerospace Engineering
_Faculty of Mechanical and Energy Engineering
_Faculty of Electrical Engineering (Power_Control)
_Faculty of Engineering and Computer Science
_Faculty of Civil Engineering, Water and Environment
_ Faculty of Nuclear Engineering

Cibiyoyin Bincike

_Research Institute of Interdisciplinary Studies
_Family Research Institute
_Research Institute of Cognitive and Brain Sciences
_Research Institute of Environmental Sciences
_Research Institute of Medical Sciences and Technologies
_Virtual Space Research Institute
_Research Institute of Medicinal Plants and Raw Materials
_Laser and Plasma Research Institute
_Research Institute of Fundamental Studies of Science and Technology
_Regional Studies Institute
_Power Network Research Institute

Cibiyoyin Nazari

_Protein Research Center
_Silk Road Research Center
_Waqf Research Center
_Center for Economic and Political Studies
_Center for Extracting Non-conventional Waters
_GIS Remote Sensing Research Center
_Center for Regional Studies and Research
_Gemology Center
_Oil and Gas Exploration Research Center
_Research Center and Chair of Human Rights, Peace and Democracy

 

Jadawalin Kuɗin Makarantar Shahid Beheshti University

Kwasa-Kwasan Shahid Beheshti University

__Psychology
_Urban Planning
_
_Architecture and Energy
_
_Electrical Engineering
_
_Civil Engineering
_Computer Engineering
_Mechanical Engineering
_Aerospace Engineering
_Natural Resources Engineering
_
_Arabic Literature
_English Language and Literature
_French Language
French Language and Literature
_General Linguistics
_Islamic Philosophy
_Persian Language and Literature
_
_Muslim History and Civilization
_
_General Law
_Oil and Gas Law
_Criminal Law and Criminology
_Commercial Law and International Investment
_International Law
_Law of Economics
_Environmental Law
_
_Physics
_
_Geomorphology
_
_Geography
_
_Biology
_
_Biotechnology
_
_Analytical Chemistry
_
_Applied Mathematics
_
_Statistics
_
_Economical Science
_
_Physiology
_Da sauransu…
Ku sauke wannan fayil na ƙasa domin samun cikakken list na kwasa-kwasan da ake yi a Shahid Beheshti University.

Kwasa-Kwasan Shahid Beheshti University

Kwasa-Kwasan Shahid Beheshti UniversityAbubuwan Alfahari

_Ayyana mambobin kwamitin ilimi 4 daga jami’ar Shahid Beheshti a matsayin jagororin kimiyya na ƙasa.
_Nasarar ɗalibin jami’ar Shahid Beheshti a taron tattaunawa na ƙasa da ƙasa kan amfani da hoto a Preclinical Research.
ـƊalibin jami’ar Shahid Beheshti ya samu lambar zinare a gasar lissafi ta duniya.
_Bayyana malamai biyu daga jami’ar Shahid Beheshti a matsayin fitattun malamai abun koyi na ƙasa.
_Fitaccen ɗalibin jami’ar Shahid Beheshti ya karbi kyautar Nobel ta Iran.
_Da sauransu…

Ababen More Rayuwa

Wurin Kwana: An buɗa rukunin wuraren kwanan Kuye Baradaran mai sassa 5 a shekarar 1991, an kuma buɗe wurin kwanan Kuye Khoharan mai sashe 4 bayan shekara 1 da buɗa Kuye Baradaran. An buɗe wurin kwanan masu iyali a yankin Valenjak, ta hanyar tallafi a shekarar 2003. Wurin kwanan Jami’ar Shahid Beheshti nada abubuwa kamar wurin cin abinci, wireless system, ɗakin karatu, masallaci, ɗakin kallo, kayan wasanni, wurin gina jiki, fili mai grass carpet, ayyukan kiwon lafiya da bada shawara, shagon kayan abinci, wurin wanki da guga, gidan burodi, shagon aski, shagon ɗinki, da sauransu.
_Wurin kwanan Kuye Baradaran mai ɗauke sashe na ɗaya zuwa na biyar da wurin kwanan Shahid Shahryari
_Wurin kwanan Kuye Khoharan mai ɗauke da sashe na ɗaya zuwa na 6.
_Wurin kwanan Kuchi  (masaukin ɗalibai mata)
_Wurin kwanan titin Keshavarz (masaukin ɗalibai mata)
_Wurin kwanan  Rastak (na ɗalibai mata)
_Wurin kwanan Ƙa’im (na ɗalibai maza)
_Wurin kwanan Shahid Ranjbaran (na ɗalibai maza)
_Wurin kwanan Rastegar (na ɗalibai maza)
_Wurin kwanan  (na ɗalibai mata)
_Wurin kwanan Bahar (na ɗalibai mata)

Abubuwan more rayuwa na jami'ar Shahid Beheshti
Yanayin Wuri

Jami’ar Shahid Beheshti tana yankin Avin na garin Tehran a babban titin Shahid Chamran, Fazlollah, Daneshjo. Ta fuskar yanayin wuri kuma, tana kusa da cibiyoyi kamar Kafe Ketab Behesht, Kamfanin Texan, Family Court No. 2, Parsian Azadi Hotel, Asibitin Ayatullahi Taleghani, Wurin sayayya na Valenjak, da kuma Faculty of Health and Safety ta jami’ar Shahid Beheshti University of Medical Sciences. Hakazalika, tashar bus mafi kusa da wannan jami’a ita ce tashar bus ta Bazar Roz.

Adireshin Shahid Beheshti University

Adireshi: Titin Daneshju, randabawul na Shahid Shahryari, titin Yemen, babbar hanyar Shahid Chamran, Tehran.


Tambayoyin da ake yawan yi game da wannan jami’a ta Shahid Beheshti

  1. Shin za’a iya yima ɗaliban ƙasar Iraq karatu cikin harshen larabci?
    Eh, amma da sharaɗin samun ɗalibai a ƙalla goma a wannan ajin.
  2. Yaushe ne lokacin yin rajista a wannan makaranta?
    A wannan jami’a, kowane matakin karatu yana da lokaci na musamman da yake karɓar takardun ɗalibai, wannan lokacin ne kaɗai za’a iya yin rajista.
Related Posts
Leave a Reply

Your email address will not be published.Required fields are marked *