Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Semnan University of Medical Sciences

Karatu a Semnan University of Medical Sciences

Loading

Semnan University of Medical Sciences ɗaya ce daga cikin jami’o’in likitanci na gwamnati da ke lardin Semnan. Jami’ar na gudanar da ayyukanta ne a ƙarƙashin kulawar Ministry of Health and Medical Education, a lardin Semnan. Domin samun ƙarin bayani game da wannan jami’a, ku kasance tare da mu.

Gabatarwa

Semnan University of Medical Sciences ta fara gudanar da ayyukanta ne a shekarar 1989, a matsayin jami’ar likitanci ta farko a Semnan. A 11 ga watan February (22 ga Bahman) na shekarar 1989 ne bisa amincewar majalisar bunƙasa jami’o’in ilimin likitanci a Iran, jami’ar karatun likitanci ta Semnan ta fara gudanar da ayyukanta ta hanyar karɓar ɗalibai 60 a fannin likitanci, lokacin tana ƙarƙashin kulawar jami’ar karatun likitanci ta Tehran (Tehran University of Medical Sciences).

Amma bisa amincewar wannan majalisar, cikin ƙasa da shekara ɗaya, aka maida ita jami’ar karatun likitanci ta Semnan (Semnan University of Medical Sciences) inda ta fara ayyukanta a shekarar 1989 da sassa kamar haka; Semnan School of Medicine, Semnan School of Nursing and Paramedicine, Shahrood School of Nursing and Midwifery (wadda aka buɗa a shekarar 1992 sannnan aka mayar da ita jami’ar likitanci a 2010), da kuma Makarantar Bahyari Hoshmand ta Damghan.

Har ila yau, an ware fili mai girman hekta 300 don gina cikakken ginin jami’ar. A makarantar likitanci (school of medicine) mai girman sama da murabba’in mita 21000, an gina wurare kamar zauren wasanni mai girman murabba’in mita 2000, hostel mai girman 5300 wanda zai ishi mutum 360.

A halin yanzu akwai ɗalibai 2756 da malamai 244 a wannan jami’a. Bayanai sun nuna cewa zuwa yanzu jami’ar ta wallafa maƙala 1452 na ilimi a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida, ta kuma wallafa maƙalar ISI guda 650. Har ila yau, jami’ar ta wallafa mujalla 1 ta musamman, sannan ta shirya taruka 7 zuwa yanzu. Baya ga haka, Semnan University of Medical Sciences ta wallafa maƙala 650 a matakin ƙasa da ƙasa.

Karatu a Semnan University of Medical Sciences

Martabar Jami’a

A sabon bayanin da tsarin ranking na Times ya fitar, wannan jami’ar tana matsayi na 1001-1200 a cikin jami’o’in duniya, ta kuma samu matsayi na 45 a cikin jami’o’in Iran.

Makarantu

_ School of Medicine
_ School of Dentistry
_ School of Pharmacy
_ Faculty of Rehabilitation
_ School of Nursing and Midwifery
_ Damghan Faculty of Health
_ Soregh Paramedical Faculty
_ Aradan Faculty of Nutrition, Food Science and Management and Information

Cibiyoyin Bincike

_ Neuromuscular Rehabilitation Research Center
_ Physiology Research Center
_ Nervous System Stem Cell Research Center
_ Abnormal Uterine Bleeding Research Center
_ Research Center for Social Factors Affecting Health
_ Nursing Care Research Center
_ Cancer Research Center
_ Comprehensive Research Laboratory
_ Salt Food Health Research Center
_ Biotechnology Research Center

Kuɗin Makarantar Semnan University of Medical Sciences

Asibitoci da cibiyoyin jinya na koyarwa

_ Kausar Medical Research Training Center
_ Amirul Mominin Medical Research Training Center
_ Damghan Province Hospital
_ Garmsar Motamedi Hospital
_ Imam Hossein Hospital, Aradan
_ 15 Khordad Hospital, Mahdishahr

Sansanonin Kiwon Lafiya

_ Semnan Health Center
_ Health and Treatment Network of Mahdishahr City
_ Damghan Health and Treatment Network
_ Health and Treatment Network of Garmsar City
_ Health and Treatment Network of Sorkheh City
_ Health and Treatment Network of Aradan City

Karatu a Semnan University of Medical Sciences

Sassan koyarwa (Departments)

School of Medicine:

Basic Sciences Departments:
_ Anatomical Sciences
_ Physiology
_ Medical Physics
_ Clinical Biochemistry
_ Immunology
_ Bacteriology and Virology
_ Parasitology and Mycology
_ Medical Biotechnology
_ Tissue Engineering and Applied Cell Science
_ Pathology
_ Islamic Teachings

Clinical Departments:
_ Social and Family Medicine
_ Women
_ Surgery
_ Children
_ Internal
_ Anesthesia
_ Emergency Medicine
_ Cardiovascular
_ Psychiatry
_ Medical Ethics

Dental College:
_ Pediatric Dentistry
_ Restorative and Beauty
_ Endodontics
_ Diseases of the Mouth, Jaw and Face
_ Periodontics
_ Dental Prostheses
_ Oral, Jaw and Facial Surgery
_ Orthodontic
_ Oral and Dental Pathology
_ Radiology of mouth, jaw and face

Faculty of Pharmacy:
_ Department of Clinical Pharmacology
_ Toxicology Department
_ Medicinal Chemistry Department
_ Department of Pharmaceutics
_ Department of Pharmacognosy
_ Department of Pharmacology

Faculty of Rehabilitation:
_ Department of Occupational Therapy
_ Department of Speech Therapy
_ Department of Physiotherapy

School of Nursing and Midwifery
_ Department Community Health Nursing Education
_ Internal Surgery Nursing
_ Children’s Nursing
_ Special Care Nursing
_ Emergency Nnursing
_ Midwifery

Damghan School of Health:
Health Education and Health Promotion
_ Occupational Health and Safety Engineering
_ Environmental Health Engineering
_ Health, Safety and Environment Management

Soreh Paramedical Faculty:
_ Operation Room Technology
_ Anesthesia
_ Radiology Technology
_ Medical Emergency
_ Health Information Technology

Aradan Faculty of Nutrition, Food Sciences and Management and Medical Information:
_ Faculty of Nutrition
_ Faculty of Food Industry

Ababen More Rayuwa

Wurin Kwana: Abubuwan da ke cikin wuraren kwanan ɗalibai sun haɗa da gado, wadrobe, carpet, labule, firiji, wurin ajiye takalmi, sai dai alhakin samar da kayan amfani na ɗaiɗaiku kamar kayan bacci (bargo, zanin gado, filo) yana wuyan ɗalibai. Abubuwan amfani na kowa da kowa a cikin hostel: Gas cooker, TV, Computer, da sauransu.

A halin yanzu jami’ar na da gine-ginen hostel guda 13 wanda suke warwatse cikin gari a garuruwan Semnan, Damghan, Sorkhe, da Aradan. Ko kuma a cikin jami’ar wanda ɗaya daga cikinsu na ɗalibai masu iyali ne, hostel 3 masu zaman kansu da ke garin Aradan kuma na mata da na maza, amma a ƙarƙashin kulawar jami’a. Akwai kuma guda ɗaya na ɗalibai mata a cikin garin na Semnan, shi ma ba na jami’ar bane amma yana ƙarƙashin kulawarta. Wurin kwanan masu iyali: Yana da sassa (suite) 16.
Daga cikin wuraren kwanan wannan jami’a akwai:
_ Wurin kwana na Andishe
_ Wurin kwana na Bustan
_ Wurin kwana na Golestan
_ Wurin kwana na masu iyali
_ Wurin kwanan ɗalibai mata na Kowsar
_ Wurin kwanan ɗalibai maza na Qods 1
_ Wurin kwanan ɗalibai maza na Qods 2
_ Wurin kwana na Salamat Sorkh
_ Wurin kwanan ɗalibai mata na Davar Abad

Babban Laburare: Babban ginin laburare mai girman murabba’in mita 2034 wanda ke ɗauke da ɗakin karatu (murabba’in mita 595), ma’ajiyar litattafai, sashen litattafai, resources, da thesis na ɗalibai (murabba’in mita 132), ɗakunan amfani da internet na ɗalibai mata da na maza (murabba’in mita 106), ɗakin seminar (murabba’in mita 40), da ɗakunan ayyukan ofis (murabba’in mita 59), kuma yana ɗauke da suna 6395 na litattafan farsi, 5375 na latin, da kuma sama da kwafin litattafai 20112 a harshen farsi, sama da guda 7404 na latin a fannonin Basic Sciences, Clinical Medicine, thesis guda 2491, project na bincike guda 517, resources na kallo da sauraro sama da guda 623 na farsi da latin, kuma yana gudanar da ayyukansa ne ga ɗalibai, malamai, da sauran ma’aikata.

Karatu a Semnan University of Medical Sciences

Yanayin Wuri

Semnan University of Medical Sciences na nan a hanyar Payambaran, garin Semnan. Jami’ar na kusa da muhimman wurare kamar Polis Rah na garin Semnan.

Saduwa da Jami’a

Adireshi: Semnan, titin Basij Setad, Semnan University of Medical Sciences and Health Services.
Shafin jami’a: https://semums.ac.ir

 

سوالات متداول راجب دانشگاه علوم پزشکی سمنان

Ko wannan makaranta na ba wa ɗaliban waje hostel?

A’a, Semnan University of Medical Sciences ba ta da wani tsari na sauke ɗaliban ƙasar waje a hostel ɗinta

Ta yaya za a samu bayani a kan kwasa-kwasan da ake yi a wannan jami’a?

Za ku iya samun bayani a kan kwasa-kwasan da ake yi ta hanyar ziyartar shafin jami’ar

Yaya ake biyan kuɗin makaranta a wannan jami’a?

A wannan jami’a da dollar ake biyan kuɗin makaranta

Related Posts
Leave a Reply

Your email address will not be published.Required fields are marked *