Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Sharif University of Technology

Karatu a Sharif University of Technology

Loading

Mutane na buƙatar masaniya da bayanai masu inganci domin zaɓen wuri da kuma kwas ɗin da zasu karanta. Hakan ne zai basu damar yin zaɓi mafi kyau, a mataki mafi muhimmanci na rayuwarsu. Maudu’in wannan rubutu shi ne ‘Karatu a Sharif University of Technology’ wanda a ciki za mu yi ƙoƙarin gabatar muku da wannan jami’a, matakinta na ilimi, da sauransu.

Gabatarwa

An buɗe wannan jami’a ne a shekarar 1965 bisa umarnin Muhammad Reza Pahlavi [har zuwa kafin  juyin musulunci da aka yi a shekarar 1979,  ana kiranta da rubutaccen sunan  Aali Hazrat Hamayoni, wato Shahensha Aryamhar,  ya kasance  sarki na biyu kuma na ƙarshe a  daular Pahlavi wanda ya yi sarautar Iran daga shekarar 1941 zuwa 1978,  shi ne  sarkin Iran na ƙarshe. Muhammad Reza Shah daga saukar mahaifinsa  Reza Shah, aka rantsar da shi a  majalisar ƙasa, a haka ya kai ga sarautar Iran inda aka tumɓuke shi da juyin musulunci da aka yi a shekarar 1979] sannan Professor  Muhammad Ali Mujtahidi Gilani  ya jagoranci  aza tubalin gininta da sunan  Aryamhar University of Technology.

Bayan  juyin juya hali na 1979, Aryamhar University of Technology ta samu sauyin suna zuwa sunan ɗaya daga ɗaliban da ta yaye,  Majid Sharif Waqefi [ɗaya daga cikin tsofaffin membobin  ƙungiyar Mojahedine Khalgh], wanda aka kashe inda  sunanta ya koma Sharif University of Technology.
A halin yanzu wannan jami’a na da ɗalibai 10242, da malamai 480. Bincike ya nuna cewa Sharif University of Technology ta wallafa maƙalar ilimi guda 16198 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida wanda daga cikinsu akwai maƙalar mujalla guda 2637, da maƙalar taro guda 13561. Har ila yau, ta wallafa karɓaɓɓun maƙaloli guda 26999 a matakin ƙasa da ƙasa. Jami’ar ta mallaki lambar girma kuma ta wallafa mujalla 6 na musamman. Hakazalika jami’ar ta shirya taruka 111.

Martabar Jami’a

A tsarin ranking na QS, Sharif University of Technology ta samu matsayi na 334 a tsakanin jami’o’in duniya, da matsayi na 84 a tsakanin jami’o’in yankin Asia. Ta wani janibin kuma wannan jami’ar ta samu matsayi na 401 – 450 idan an yi la’akari da kwasa-kwasai da wasu al’amura.

Har ila yau, jami’ar ta samu matsayi na 701 – 800 a tsarin ranking na Shanghai. A daidai lokacin da shi kuma tsrain ranking na TIMES ya bayyana Sharif University of Technology a matsayi na 301 – 350.

Karatu a Sharif University of Technology

Makarantu

_Faculty of Electrical Engineering
_Chemical and Petroleum Engineering
_Engineering and Material Science
_Faculty of Mechanical Engineering
_Science Engineering
_Faculty of Physics
_Faculty of Mathematics
_Faculty of Chemistry
_Industrial Engineering
_ Faculty of Civil Engineering
_Computer Engineering
_Department of Philosophy of Science
_Faculty of Aerospace Engineering
_Faculty of Management and Economics
_Energy Engineering

_Ƙungiyoyin Ɗalibai

_Imam Ali (AS) People’s Student Aid Society
_Sharif University Poetry and Literature Center
_Deep Scientific Association
_Sharif University Student Basij
_Mountain Group of Sharif Students
_Sharif University Music Center
_Group of Environmentalists
_Farda Sabz Charity
_Center of Helpers
_Islamic Student Association
_Sharif Islamic Society
_Students Union Council
_Sharif International Association of Petroleum Engineers (Sharif SPE)
_Cultural Scientific Group  Chemistry
_Mahdovian Assembly of Sharif University

Cibiyoyin koyarwa

_Department of Philosophy of Science
_Center of Languages and Linguistics
_Research Institute of Science and Nano Technology
_Physical Education
_Workshops
_Graphic Center
_Center for Islamic Education and Sciences

Laburare

Sharif University of Technology na da babban laburare ɗaya da wasu keɓantattu guda 10 wanda suka fara aiki tun lokacin buɗa makaranta:
_Laburaren Chemical and Petroleum Engineering
_Laburaren Engineering and Materials Science
_Library of Philosophy of Science Department
_Aerospace Engineering Library
_Laburaren Mathematics and Industries
_Laburaren Biochemistry
_Laburaren Management
_Laburaren Physics
_Laburaren Imran
_Laburaren Electronics

Kuɗin Makarantar Sharif University of Technology

Kwasa-Kwasai

_Electronics
_Power
_Control
_Telecommunications (system/field)
_Structure
_ Earthquake Engineering
_Soil Mechanics and Foundations
_Road and Transportation
_Water Engineering
_Transportation Planning
_Applied design (Dynamics of Solids/Control and Vibrations)
_Energy Conversion
_Aerodynamics
_Aerial Structures
_Flight Mechanics and Satellite Control
_Propulsion
_Marine Engineering
_Bioelectric
_Industrial Engineering
_Architecture of Computer Systems (Hardware)
_Artificial Intelligence
_Software Engineering
_Information Technology
_Algorithms and Calculations
_Nuclear Engineering – Reactor
_Nuclear Engineering – Fuel Cycle
_Energy Systems Engineering
_Nanomaterials
_Nano Electronics
_Chemical Engineering
_Materials Engineering and Metallurgy
_Organic Chemistry
_Mineral Chemistry
_Physical Chemistry
_Analytical Chemistry
_ Pure Mathematics
_Applied Mathematics
_Computational Nanophysics
_Nano Science and Technology (Nanomaterials)
_Nanochemistry (Polymer Nanotechnology/Mineral Nanomaterials)
_Physics
_Computer Science
_Da sauransu…
Ku sauke wannan fayil na ƙasa domin samun cikakken list na kwasa-kwasai da matakan karatu da kuke nema.

Kwasa-Kwasan Sharif University of Technology

Kwasa-Kwasan Sharif University of TechnologyAbubuwan Alfahari

_Samun matsayi na farko a  gasar lissafi ta ɗalibai  shekara 21 a jere.
_Samun matsayi na 200 – 250 a tsakanin fitattun jami’o’i na duniya a tsarin ranking na QS (2020)
_Horar da ɗalibai sama da 46,000 a matakai daban daban na karatu.
_Su ke da mafi yawan membobin  ƙungiyar Al’adun kimiyya  a duk jami’o’in Iran
_Samun matsayi na farko a cikin cibiyoyi a bukukuwan shekara-shekara na zaɓaɓɓun Nanotechnology, daga shekarar 2008 zuwa yanzu.
_Su ke da mafi yawan ɗalibai a tsangayoyin ilimi na jami’o’in Iran
_Lashe gasar lissafi ta ɗalibai, ta ƙasa
_Samun matsayi na farko a jami’o’in fasaha na Iran a tsarin ranking na ISC (2012)
_Karɓar lambar yabo ta ‘Fields’ da fitattar ɗalibar wannan jami’a Khanom Maryam Mirzakhani ta yi (2014)
_Samun matsayi na 5 a gasar lissafi ta duniya (ƙasar Hungary)
_Da sauransu…

Ababen More Rayuwa

Wurin kwana: Wurin kwanan ɗalibai mata na Tarasht 2, wurin kwanan Shahid Shurideh, wurin kwanan ɗalibai maza na Tarasht 3, wurin kwanan Shahid Ahmadi Roshan, Mosalla Nejad, Shahid Wazwaei, Shahid Heidar Tash, da wurin kwanan Shademan. Wurin kwanan ɗalibai mata yana da suite mai ɗaukar mutum 4, mutum 6, da mai ɗaukar mutum 8. Wurin kwanan ɗalibai maza kuma yana da ɗakunan mutum 4 da na mutum 6. A duka wuraren kwanan wannan jami’a, ɗalibai suna da ɗakin karatu, zauren wasanni, shagon sayayya, filin wasa, koren fili, shagon gyaran kai, shagon ɗinki, wurin wanki da guga. Ana gudanar da tarukan addini, al’adu, da wasanni a cikin hostel. Akwai motocin da ke kai-komo a lokutan da aka tsara daga hostel zuwa makaranta ko daga makaranta zuwa hostel wanda ɗalibai zasu iya amfani da su wurin zirga-zirga. A ranakun alhamis da kuma darare ana raba abinci ne a hostel, amma dole mutum ya sayi abinci kafin lokacin rabawa, sannan kuma ya zo da wuri inda ake raba abincin domin karɓar nasa.

Kayan aikin Sharif University of TechnologyYanayin Wuri

Sharif University of Technology (jami’a kuma cibiyar koyarwa ta gaba da sakandare)  wadda ke yankin  Teymuri da ke garin Tehran  a titin Azadi, Habibzadegan, Neshiba. Ta fuskar yanayin wuri, wannan jami’a na kusa da  Digi Skull,  hakazalika  gidan cin abinci na Mehdi,  Stack,  Sharif Plus,  Ginin Sharif Technologies 2,  da kuma  Jisu Fast Food.

Adireshin Sharif University of Technology

Adireshi: Sharif University of Technology, Titin Azadi, Tehran

Sunan cibiya: Sharif University of Technology

Akwatin aike: 11365/8639

Shafin jami’a: http://www.sharif.ir


Tambayoyin da ake yi game da karatu a Sharif University of Technology.

  1. Wasu takardu ake buƙata don yin rijista a Sharif University of Technology?
    Passport, hoto, trasnscript, certificate, CV, motivation letter, recommendation letter.
  2. Ko wannan jami’a na karɓar ɗaliban ƙasar waje a matakin PhD?
    A’a
 

Loading

Related Posts
Leave a Reply

Your email address will not be published.Required fields are marked *