Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu Amirkabir University

Karatu Amirkabir University

Loading

Jami’ar Amirkabir tana ɗaya daga cikin jami’o’i mafi kyau a Iran, kuma ita ce jami’ar fasaha ta farko a ƙasar. A wannan rubutun za mu kawo muku bayani dangane da yanayin karatu a jami’ar Amirkabir domin taimaka muku wurin yin zaɓin da ya dace wajen ci gaba da karatunku. Ku kasance tare da mu.

Gabatarwa

An assasa jami’ar fasaha ta Amirkabir a mastayin jami’ar fasaha ta farko a ƙasar Iran, a shekarar 1956 a garin Tehran Sunan wannan jami’a na asali shi ne “Tehran Polytechnic” kuma an assasa ta domin bunƙasa ayyukan cibiyoyin fasaha guda biyu na lokacin, “Technology Institute” da “Higher Art Gallery”. Shekara ɗaya bayan assasa wannan jami’a, ta fara karɓar ɗalibai ta hanyar yi musu jarabawa,  sannan ta fara ayyukanta na asali da koyarwa a shekarar 1958 da kwas biyar kacal. Kwasa-Kwasan “Electricity and Electronics”, “Mechanics”, “Textile”, “Chemistry” da “Road and Construction”.

Bayan juyin juya hali ne aka canza sunan wannan cibiya ta Tehran Polytechnic zuwa Amirkabir University, bayan haka aka ƙara mata yawan makarantu da gine-gine a garuruwan Bandar Abbas, Garmsar, Mahshar, da sauransu.
Yanzu haka jami’ar fasaha ta Amirkabir na da ɗalibai 7000, malamai 148, masu muƙami a majalisiar wakilai ta ƙasa 10.
Ya kamata a san cewa jami’ar Amirkabir ta yi nasarar shigar da ƙirƙire-ƙirƙire guda 1000, ta wallafa maƙala 31100, maƙala 16300 a ISI, wanda hakan ya bata matsayi mai kyau a tsakanin jami’o’in Iran.

Martabar Amirkabir University

Jami’ar fasaha ta Amirkabir a shekarar 2023, a tsarin ranking na Times ta samu matsayi na 350-400  a jami’o’in duniya, matsayin ta na sama da na Iran University of Science and Technology, Sharif University of Technology, da kuma Khaje Nasir Toosi University of Technology. A tsarin ranking na Shanghai kuma ta samu matsayi na 401 – 500. Yanzu haka a tsarin ranking na Shanghai jami’ar na a matsayi na 604 – 700.

Makarantu da sassan koyarwa na jami’ar Amirkabir

Amirkabir University of Technology a halin yanzu tana da makarantu 16 da departments masu zaman kansu guda 6, da sassa 3 na koyarwa a garuruwan Bandar Abbas, Garmsar, da Mahshahr. Hakazalika, jami’ar na da haraba ɗaya ta harkokin ƙasa da ƙasa, da kuma cibiyar koyarwa ta online guda ɗaya.
A baya, Jami’ar Tafresh ta kasance a ƙarƙashin wannan jami’a.

Cibiyoyin sun haɗa da:
_ Industrial Management and Engineering Campus
Faculty of Industrial Engineering and Management Systems
Faculty of Management, Science and Technology
Institute of Management and Industrial Engineering

_ Electrical, Computer and Medical Engineering Campus
Faculty of Electrical Engineering
Faculty of Computer Engineering
Faculty of Medical Engineering
Research Institute of Information and Communication Technology and Power Network

_ Mechanics, Aerospace and Marine Campus
Faculty of Mechanical Engineering
Faculty of Aerospace Engineering
Faculty of Marine Engineering
Research Institute of Mechanical Engineering Technologies

_ Campus of Advanced Materials and Processes
Faculty of Chemical Engineering
Faculty of Textile Engineering
Faculty of Polymer and Paint Engineering
Faculty of Materials Engineering and Metallurgy
Advanced Materials and Processes Engineering Research Institute

_ Oil, Civil and Mining Campus
Faculty of Civil and Environmental Engineering
Faculty of Mining Engineering
Faculty of Petroleum Engineering
Zamin Civil Research Institute

Science Campus
Faculty of Mathematics and Computer Science
Faculty of Physics and Energy Engineering
School of Chemistry
Science Research Institute

Harabobi da sassan jami’ar waɗanda suke waje
Bandar Mahshahr Educational Unit
Hormozgan Educational Unit (Bandar Abbas)
Garmsar University Unit
International Campus
Kish International Campus

_ Sassan koyarwa masu Zaman Kansu
Department of Foreign Language Training
Department of Education and Human Sciences
Department of Physical Education
International Language Center

_ Sassan da suka ɗa kwasa-kwasai daban-daban
Robotic
Mechatronics
Space and Avionics Engineering
Corrosion Engineering and Protection of Materials
Energy Engineering
Information Technology
Engineering of Coasts, Ports and Marine Structures

Abubuwan alfaharin jami’ar Amirkabir

Abubuwan alfaharin Jami’ar Fasaha ta Amirkabir Tehran

Tsawon lokaci, wannan jami’a ta faɗaɗa sosai ta fuskar yawa da inganci ta yadda a yau ana ɗaukar ta a matsayin “uwar jami’o’in fasaha na ƙasa” kuma ta sami matsayi mafi girma a tsakanin cibiyoyin bincike na kimiyya ta hanyar bunƙasa ilimi, bincike. da ayyukan ɗalibai.

Daga cikin abubuwan alfahari na wannan jami’a akwai:
• Samun laƙabin ‘ginshiƙin kimiyya’ a fannonin Mechanical Engineering, Electrical Engineering, Chemical Engineering, Textile Engineering, Medical Engineering, Aerospace Engineering, Civil Engineering, Computer Engineering, da Information Technology.
• Samun babban matsayi da kyaututtuka masu yawa a bikin Khwarazmi, da manyan muƙamai a gasar Olympics ɗin ɗalibai ta ƙasa da ƙasa.
• Samun lambobin yabo masu daraja ta gwarazan ɗalibai, da ɗalibai masu fasaha daga gasa daban-daban na ɗaliban kimiyya na duniya; ciki har da sarrafa sinadarai da robot.
• Samun matsayi na farko a bincike, tsakanin jami’o’in fasaha da engineering na ƙasar a wasu darussan gwaji na ma’aikatar ilimi, bincike da fasaha.
• Samun matsayi na farko a alaƙar masana’antu da jami’o’i, da gudanar da muhimman ayyuka na ƙasa.
• Alaƙarta ta ilimin kimiyya a matakin ƙasa da ƙasa, da sanya hannu a takardun yarjejeniya tare da manyan jami’o’in duniya.
• Jawo hankalin gwarazan mutane da masu hazaƙa tare da sauƙaƙe musu yanayin karatu, kamar samar da yiwuwar karanta kwas biyu a lokaci guda ga ɗalibai masu ƙoƙari, da shiga matakin mastas da PhD ba tare da yin jarrabawar shiga jami’a ba.
• Samar da ɗakunan gwaje-gwaje na zamani da ingantattun kayan aiki tare da gudanar da ayyukan ƙasa, gami da ƙera na’urar Supercluster Supercomputer mafi sauri, da ƙerawa tare da harba tauraron ɗan adam.
• Shirya tarukan kimiyya daban-daban, tarukan ƙarawa juna sani, da wasu taruka a matakan ƙasa da ƙasa.
• Jagorantar bincike a kan nukiliya, da rawar da malamai da ɗalibai suka taka wajen nasarar da ƙasar ta samu wajen cimma tsarin makamashin nukiliya.
• Nasarar cin gajiyar “fuskoki masu tasiri”, malamai da ɗalibai abun koyi na ƙasar.
Abubuwan more rayuwa na jami’ar


Hasumiyar kimiyya da  fasaha ta jami’ar Amirkabir (ginin Abu Ali Sina)
Sashen kula da fasaha da haɓaka ƙirƙire-ƙirƙire na jami’ar Amirkabir ɗaya ne daga cikin sassan bincike na jami’ar. Manufar wannan rukunin ita ce canza sabbin ƙirƙire-ƙirƙire da nasarorin kimiyya zuwa fasahohi da kayayyakin da ƙasar ke buƙata, da kuma kafa kamfanoni masu dogaro da ilimi. Wannan rukunin ya ƙunshi sassa uku: cibiyoyin kasuwanci, haɓakawa da jagorantar kamfanoni masu dogaro da ilimi, sannan kuma yayin haɓaka al’adun kasuwanci a matakin jami’a, yana ƙoƙarin yin shirye-shiryen mayar da su kamfanoni na ilimi ta hanyar gano mutane masu ƙwazo da sabbin ra’ayoyi tare da basu tallafi na kayan aiki da suke buƙata. Har ila yau, ta hanyar samar da abubuwan da suka dace tare da ingantaccen tallafi na kamfanoni masu dogaro da ilimi, yana taimaka musu wurin samun nasarar sayar da kayayyaki da ayyukansu, ta yadda jami’a da ‘yan kasuwa za su ci gajiyar aikin.

Babban Laburaren Jami’ar
An kafa babban laburare da cibiyar tattara bayanan kimiyya na Jami’ar Fasaha ta Amirkabir (Tehran Polytechnic) a shekarar 1998, a 1999 kuma aka faɗaɗa shi domin bunƙasa ilimin kimiyya da fasaha, sannan aka nufi yi ma resources ɗin da ke ciki kyakkyawan tsari. A shekarar 1999, an ƙaddamar da tsarin lamuni na na’ura a cikin babban laburaren ta hanyar amfani da lambar ‘barcode’. A 2004 kuma, an aiwatar da shirin sarrafa teburin bayar da lamuni na ɗakunan karatu na makarantu (satellite), kuma a halin yanzu ana ba membobin laburaren lamuni ne kawai ta wannan sabuwar hanya.

Babbar Laboratory ta jami’ar Amirkabir
Tsarin ayyukan laboratory na jami’ar fasaha ta Amirkabir, wani rukunin musamman ne na kayan aiki na zamani wanda ke da tallafi na fiye da shekaru hamsin na ƙwararrun malaman jami’ar, da hadafin gabatar da ayyukan bincike ga ɗalibai, malamai, manazarta, da masana’antu daban-daban na ƙasar. Yana da yanayin samar da ingantattun hidimomin laboratory na zamani da ake buƙata daidai da sabbin dokokin ƙasa da na duniya.

Kaya da wuraren wasanni
Swimming pool, koren filin wasa, zauren wasanni, rukunin wasanni da ya haɗa da zauren karate, zauren table tennis, zauren gina jiki na mata da na maza, da zauren wasan takobi.Adireshin Amirkabir University of Technology


Sabon adireshin jami’ar: Iran – Tehran – Meidane Valiasr – titin Hafez – block na 350 
Tsohon adireshin jami’ar: Iran – Tehran – titin Hafez – block na 424 


Tambayoyi game da Amirkabir University of Technology


  1. Shin jami’ar Amirkabir na karɓar ɗalibai a matakin PhD?
    A a, wannan jami’ar bata karɓar ɗaliban ƙasashen waje a matakin PhD.

[neshan-map id=”16″]

Related Posts
Leave a Reply