Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Iran University of Science and Technology

Karatu a Iran University of Science and Technology

Loading

A wannan rubutun zamu gabatar muku da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Iran wato Iran University of Science and Technology, ku kasance da mu domin sanin wannan jami’ar da kuma samun bayani akan yadda ake karatu a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Iran da kuma sharuɗan karɓar ɗalibi a wannan jami’a.

Gabatarwa

An assasa Iran University of Science and Technology ne a shekarar 1929 a matsayin babbar kwaleji zamanin daular Ƙajar a cikin garinTehran, kuma a wancan lokacin za’a iya kiran wannan jami’ar a matsayin jami’a ta biyu mafi kyau a Iran. Babbar harabar wannan jami’a tana cikin garin Tehran, inda sauran rassanta suna garin Bushehr, Damavand, da garin Noor.

Reshen Arak: A halin yanzu an bunƙasa wannan reshen ya koma mai zaman kansa.

Reshen Damavand: An ƙaddamar da shi ne a shekarar 2005, inda ake yin karatun Mechanical Engineering ɓangaren digiri a ciki, a halin yanzu tsarin bunƙasa shi da magana akan gine-gine da kayan aikinsa na cigaba da gudana.

Reshen Noor: An assasa shi ne a shekarar 2004 kuma akwai ɗalibai 200 da suke karatu a wannan jami’ar. Ana yin kwas 13 a ɓangaren digiri na biyu (Masters) a nan.

Reshen Behshahr: An assasa wannan reshen ne a shekarar 1994 a garin Behshahr. Lokacin da aka assasa shi, ana yin kwasa-kwasai uku ne kawai a wannan sashen, kwasa-kwasan sun haɗa da Computer Engineering, Industrial Engineering, da kuma Applied Mathematics. A shekarar 2009 kwas ɗin Electrical Engineering ya samu shiga jerin kwasa-kwasan da ake yi a wannan reshen. Har zuwa watan Satumban shekarar 2009, ana karɓan ɗalibai masu karatu da dare ne kawai, bayan wannan lokacin ne aka fara karɓar ɗalibai a tsarin karatun rana shima a kwas biyu kawai, kwas ɗin Electrical Engineering da na Applied Mathematics. Daga ƙarshe a shekarar 2012, reshen Behshahr ya koma (jami’ar) Mazandaran University of Science and Technology.

Tun bayan assasa ta, wannan jami’a ta canja suna da muhallinta fiye da sau ɗaya:

A lokacin assasawa (1929): Sunan High Art Gallery, a titin 30 Tir

Shekarar 1957: (Canjin Suna zuwa) Tehran Institute of Technology

Shekarar 1963: (Canjin suna da muhalli) High art gallery, Unguwar Narmak (muhallinta na yanzu)

A shekarar 1972: (Canjin suna zuwa) Makarantar kimiyya da fasaha ta Iran

A shekarar 1978: Bunƙasa makarantar zuwa jami’ar kimiyya da fasaha ta Iran (Iran University of Science and Technology)

A halin yanzu, Ɗalibai 10,837 da Malamai 608 suke aiki a cikin wannan muhallin. jami’ar ta wallafa maƙalolin ilimi guda 23,244 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida, hakazalika ita ce mawallafiyar mujalloli 13 na musamman, kuma akwai taruka 70 waɗanda wannan jami’ar ce ta shirya su. Ɗalibai 32,000 ne suka kammala karatunsu a wannan jami’a a matakin digiri da masters.

Martabar Iran University of Science and Technology

Tsarin martabawa na Shanghai In aka duba ingancin koyarwa, ingancin mambobin kwamitin kimiyya, natijojin bincike-bincike, sakamakon aiki tuƙuru da wannan jami’a tayi ne ya sa jami’ar (Iran University of Science and Technology) ta samu shiga cikin sahun manyan jami’o’i 1000 na duniya a wannan tsari na martaba jami’o’i da auna kimarsu. ta samu martaba ta 801-900 wanda ci gaba ne idan aka kwatanta da martabarta a shekarar da ta gabata (martaba ta 901-1000).

Karatu a Iran University of Science and TechnologyMakarantu

Jami’ar Iran University of Science and Technology nada makarantu 15 da Rukunan koyarwa guda 3 masu zaman kansu wanda suka haɗa da: al’adu da koyrwar addinin musulunci, motsa jiki da yarukan ƙasasen waje.

_Makarantar Electrical Engineering
_Makarantar Management, Economics
_Makarantar Automotive Engineering
_Makaratntar Railway Engineering
_Makarantar Chemical, Oil and Gas Engineering
_Makarantar Industrial Engineering
_Makarantar Civil Engineering
_Makarantar Computer Engineering
_Makarantar Mechanical Engineering
_Makarantar Material Engineering and Metallurgy
_Makarantar Architechture and Urban Design
_Makarantar Mathematical Sciences
_Makarantar Physics
_Makarantar Chemistry
_Makarantar New Technologies

Kwasa-kwasan karatu

Wannan jami’ar kamar dai sauran jami’o’i, ana yin kwasa-kwasai masu yawa a matakai daban-daban, wasu daga cikin kwasa-kwasan sun haɗa da:

_Medical Engineering
_Automotive Engineering
_Rail transportation Engineering
_Chemical Engineering
_Biotechnology
_Industrial Engineering
_Civil Engineering
_Computer Engineering
_Architecture
_Industrial Design
_Philosophy of science
_Statistics
_Nuclear Engineering
_Crisis Management
_Islamic Economy
_Da sauransu.

Kwasa-kwasan Iran University of Science and TechnologyKayan aiki da ababen more rayuwa

Iran University of Science and Technology ta yi ma ɗalibai tanadin kayan aiki da na more rayuwa kamar Wurin kwanan ɗalibai, Lburare, Cibiyoyin bincike, Ɗakunan gwaje-gwaje da Wurin bincike.

Jami’ar tana da Hostel guda 8 waɗanda ke ɗauke da ɗalibai 3050. Ɗalibai maza 2246 da ɗalibai mata 804.

Laburaren asali na jami’ar yana da girman murabba’in kilomita 2000, litattafai guda 108321, wallafe-wallafen duk shekara guda 1033 a mujalladai 60000, kaset CD guda 2300, microfilms guda 690, Project guda 2092, da kuma matattarar bayanai na e-book guda 30.

Har ila yau, wuraren wasanni a Iran University of Science and Technology sun haɗa da wuraren wasanni guda uku na wasannin ciki kamar basketball, volleyball da kuma filin wasan ƙwallon ƙafa da sauran wasanni da suka haɗa da Taekwondo, Judo, Karate, Ping Pong, Chess, Badminton, Wrestling, Kung Fu, Ɗaga kayan nauyi, Wasan takobi, hawan dutse, kibiya, Tennis, gudu da gina jiki saboda ɗalibai maza da kuma wasannin Basketball, Volleyball, Taekwondo, Karate, ping pong, chess, badminton, hawan dutse, harbin kibiya, tennis, iyo, physical fitness da gudu saboda ɗalibai mata.

Sauran abubuwa sun haɗa da masallaci, clinic, sashen cardiology, ophthalmology, gynecology, dermatology, dentistry, post office, banki, shagon litattafai da kayan rubutu, binding, ayyukan typing da photocopy, shagon hoto, wuraren cin abinci na ɗalibai maza da na ɗalibai mta, wuraren cin abinci na malamai da sauran ma’aikata, shagon takami, saloon ɗin gyaran kai, wurin wanki, gidan biredi, supermarket na ɗalibai, supermarket na malamai, da kindergarten.

Kayan aikin Iran University of Science and TechnologyNasarorin Jami’a

Ɗaya daga cikin dalilan da suka bambanta wannan jami’a da sauran cibiyoyin koyarwa, shi ne nasarorinta wanda zamu kawo muku su a taƙaice kamar haka:
_Wallafa mujalloli guda 5 na musamman kuma na duniya karon farko a Iran.
_Ita kawai keda taskar samfurorin bincike na jami’a, sauran jami’o’i basuda
_Kafa makarantar Automotive Engineering karon farko a Iran tare da haɗin gwiwar ƙungiyar bunƙasawa da zamanantar da masana’antun Iran.
_Kafa makarantar Automotive Engineering karon farko a Iran tare da haɗin gwiwar ƙungiyar bunƙasawa da zamanantar da masana’antun Iran.
_Kafa cibiyar Neurotechnology ta Iran
_Da sauransu

Sunayen cibiyoyin bincike

_Cibiyar binciken Green
_Cibiyar binciken Electronics
_Cibiyar binciken zirga-zirga
_Cibiyar binciken Engineering and Neurotechnology ta Iran
_Cibiyar binciken siminti
_Cibiyar binciken Bitumen and Asphalt Mixture
_Cibiyar bincike da fasahar sadarwa
_Antenna and Microwave Laboratory
_Cibiyar biciken Nanotronics
_Laboratory of Neuroscience and Engineering

Kuɗin makarantar Iran University of Science and Technology

Jadawalin kuɗin makarantar Iran University of Science and Technology

رشته تحصیلیمقطع مورد نظرطول مدت دوره تحصیلقیمت شهریه(سالیانه)
کلیه رشته هاکارشناسی4 سال1600$
کارشناسی ارشد2 سال1800$
دکتری3 الی 4 سال2200$

Muhallin da jami’ar take

Iran University of Science tana cikin Tehran (zone na 4) da kuma yankin gabas na wannan gari. Daga arewa, tana da iyaka da titin Delavaran da randabawul na Al Ghadeer, daga gabas kuma titin Tabataba’i Nesab da titin Zafarƙandi, daga kudu kuma titin Farjam da babbar hanyar Bagheri, daga yamma kuma da titin Hengam, kuma tana kusa da Tehranpars, Shemiran-nou, Awƙaf da Narmak. Wannan unguwar ba ta cikin tsarin musamman na zirga-zirgar ababen hawa, sannan kuma daga cikin wurare masu muhimmanci sun haɗa da gidan cin abinci na Nader, cibiyar kasuwanci ta Yas Hengam, Samiyeh Park, Lambun Sadd, wurin iyo na Sar-Poshide, 121 sound and security systems, Shokoofeh Park, Sayyidus-shuhada Park, da kuma wurin shaƙatawa na Iran University of Science and Technology.

Adireshin Iran University of Science and Technology

Adireshi: Iran University of Science and Technology, titin Daneshga, babban titin Hengam, Resalat, Tehran Iran.


Tambayoyin da ake yawan yi

  1. نحوه دریافت شهریه دانشگاه علم و صنعت به چه صورت است؟
    این دانشگاه شهریه را به صورت تبدیل نرخ نیمائی یورو به تومان دریافت می‌کند.
  2. آیا دانشگاه علم و صنعت ایران دارای تخفیف شهریه است؟
    بله، در صورتی که از طرف شرکت ما اقدام به ثبت نام کنید شهریه شما حدود 30 الی 40 درصد کاهش می‌یابد.
  3. زبان تحصیل به چه صورت است؟
    امکان برگزاری دوره به زبان انگلیسی وجود دارد ولی ارائه مدرک زبان فارسی الزامی است.

[neshan-map id=”35″]

Related Posts
Leave a Reply