[gtranslate]
Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search
با شما تا اوج

Kamfanin Tolo Safiran Noor | Masu aikin karɓar bizar karatu wa ɗalibai a farashi mai sauƙi

Kamfanin Tolo Safiran Noor mai wakiltar wasu daga cikin amintattun jami’o’in ciki da wajen ƙasar Iran, yana tare da ku domin aiwatar muku da ayyuka kamar: yin rajista, karɓar admission, karɓar bizar karatu, da sauran ayyukan makaranta cikin ƙanƙanin lokaci da kuma farashi mai sauƙi, tare da taimaka muku wurin gina irin goben da kuke buƙata.

+0K

Abokanan ciniki da suka gamsu da aikinmu

+0

kammalallun fayil

+0

Awannin aiki

+0

Kwangila da jami'o'i
Fitattun labaran shafinmu a harshen larabci
Ku bibiyemu a taruka...

Bidiyoyin kamfanin Tolo Safiran Noor

Bayanai

Karramawa ga kamfanin Tolu Safiran Noor a matsayin fitatta kuma zaɓaɓɓar cibiyar jan hankalin ɗaliban ƙasashen waje, daga Hukumar Ilimi, Bincike da fasaha da kuma Hukumar kula da Al’adu da Irshadin Addinin Musulunci ta Iran a wurin bikin jan hankalin ɗaliban waje karo na farko.

Abubuwan Alfahari

Fita waje karatu, aikinmu ne...

Muna masu alfaharin sanar da ku cewa kamfanin Tolu Safiran Noor wanda ma’aikatar Ilimi, bincike da fasaha da kuma ma’aikatar al’adu da irshadin addinin musulunci ta Iran suka fara ayyanawa a matsayin fitatta kuma zaɓaɓɓar cibiyar jawo ɗaliban ƙasashen waje, na tare daku domin samar muku mafi kyawon yanayin karatu a Iran.

Ainihin Manufar Kamfanin Tolu Safiran Noor

Kamfanin Tolo Safiran Noor ya fara gudanar da aikinsa ne a fagen ayyukan da suka shafi ɗaliban ƙasashen waje a shekarar 2019. Da farko wannan kamfanin ya duƙufa ne a ayyukan da suka shafi rajistar ɗalibai kawai. Bayan shuɗewar ‘yan shekaru kaɗan ne muka cimma wannan matsaya cewa mu ɗauki ƙwararrun ma’aikata a fannin hulɗa mai tasiri, programming, da fannin gudanar da harkokin kuɗi sannan mu faɗaɗa ayyukanmu sosai zuwa cikin jami’o’in Iran. Hakazalika duk da takunkumi da aka ƙaƙabawa ƙasarmu, mun samu shiga a fagen mu’amala ta kuɗi tsakanin ƙasashe tun daga kan biyan kuɗin makaranta har zuwa sauran kuɗaɗen da suka shafi karatu. Muna alfahari da cewa tsawon wannan lokacin ma’aikatanmu suna iyakacin ƙoƙarinsu wurin ganin cewa kun samu biyan buƙatunku abokanan cinikayyarmu ta yadda har ya zama mun faɗaɗa ayyukanmu daga kan ɗaliban maƙotan ƙasashe zuwa sauran ɗaliban ƙasashen duniya kuma tsawon wannan lokacin mun yi iya bakin ƙoƙarinmu wurin ganin cewa mun samar muku da ingantattun ayyuka a ɓangaren rajista, karɓar admission, buɗa fayil ɗin karatu a ma’aikatar harkokin waje, karɓar bizar karatu, zaɓen darusa, da sauransu a zamanance kuma cikin ƙwarewa. A halin yanzu a kamfanin Tolu Safiran Noor muna alfahari da cewa sakamakon saurin aikinmu da kuma ƙarfin gogayya da muke dashi da amintaccen wurin aiki ya sanya ɗalibai da yawa da masu aiki a wannan fage na al’amuran karatun ɗalibai suka zaɓemu.

Ku damƙa dukan ayyukan da suka shafi karatunku a hannumnu ta hanyar amfani da wannan manhajar.

Manhajar Android ta Tolu Safiran Noor
0%
Robot ɗin Telegram na Tolu Safiran Noor
0%
Manhajar iOS ta Tolu Safiran Noor
0%
Sashen mu'amala da abokanan ciniki ta hanyar lambobin USSD
0%
Karon farko a Iran
Karɓar bizar karatu da izinin zama
Za mu nema muku biza da izinin zama daga kowace makaranta kuke buƙata cikin ƙanƙanin lokaci.
Rajista a fitattun jami’o’in Iran
Ku nemi fitattun jami’o’i kuma mafi daraja na Iran daga wurinmu mu kuma zamu karɓa muku admission a farashi mai sauƙi kuma da sauri.
Buɗe fayil ɗin karatu a ma’aikatar harkokin waje
Za mu miƙa fayil ɗinku a ma’aikatar harkokin waje (bayan buɗewa) domin ku sami damar tantance takardun karatunku bayan kun koma ƙasashenku.
Biyan kuɗaɗen da suka shafi karatu
Ku damƙa biyan duka kuɗaɗen da suka shafi karatunku a hannunmu tun daga kan kuɗin makaranta, kuɗin hostel, kuɗin biza da izinin zama, da sauransu cikin kwanciyar hankali da dukkan aminci.
Na musamman

Ku nemi fitattun jami'o'i daga garemu

Wasu daga cikin ayyukanmu

Lasisinmu

Aminta daga wurinku, Karɓar admission daga wurinmu

Muna masu alfaharin sanar muku cewa a tsawon shekara 9 da mukayi a wannan aiki, mun yi aiki da jami’o’i sama da 30 yanzu haka, kuma mun samu mafi kyawon sakamako.

Ra'ayin abokan cinikayyarmu

+0

Wasu daga cikin jami'o'in da sukayi aiki da mu...

Muna masu alfaharin sanar muku cewa a tsawon shekara 9 da mukayi a wannan aikin, muna aiki da jami’o’i sama da 30 yanzu haka, kuma mun samu mafi kyawon sakamako.

Ku san ma’aikatanmu

Gabatar da wasu daga cikin danginmu na Tolu Safiran Noor

Muhandis Hosein Yaqoubi
Muhandis Hosein Yaqoubi
Shugaban Kamfanin Tolu Safiran Noor

Masters a International Business Management

Khanom Faride Shirdel
Khanom Faride Shirdel
Manajar harkokin kuɗi

Masters a International Business Management

Engr. Abolfazl Khaleghi
Engr. Abolfazl Khaleghi
Manajan IT

Digiri a IT Engineering, Programmer kuma Designer

Muhandis Noshin Bakhshi
Muhandis Noshin Bakhshi
Manajar ciki kuma mai kula da sashen taimako

Masters a Computer Engineering da Artificial Intelligence