Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a University of Mohaghegh Ardabili

Karatu a University of Mohaghegh Ardabili

Loading

Jami’ar Mohaghegh Ardabili ita kaɗai ce cikakkar jami’a a garin Ardabil da ke arewa maso gabacin ƙasar Iran. Ku kasance tare da mu domin samun bayanai a kan yanayin karatu a wannan jami’a ta Mohaghegh Ardabili da sharuɗan samun karɓuwa a cikinta.

Gabatarwa

An assasa jami’ar Mohaghegh Ardabili a shekarar 1978 da sunan Makarantar Agriculture a ƙarƙashin kulawar jami’ar Tabriz, inda ta fara aikinta ta da karɓar ɗalibai 30 a kwas ɗin Agriculture. Yanzu haka tana da muhallin koyarwa mai girman murabba’in mita 114,000 tare da malamai 399 membobin tsangayar ilimi, wanda daga cikinsu akwai mutum ɗaya da ya taka babban matsayi a ilimi (na Distingushed Professor), akwai professors 74, associate professors 155, assistant professor 153, da masu horarwa mutum 16. Wannan jami’a na da mujallar ilimi guda 4, tana da ma’aikata 307, da kimanin ɗalibai 12,000.

Bincike ya nuna cewa an wallafa maƙalar ilimi guda 15151 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida a wannan jami’ar. Maƙala 3348 daga cikinsu na mujalla ne, 11803 kuma na taro. Haka zalika ta wallafa karɓaɓɓun maƙaloli guda 3760 a matakin ƙasa da ƙasa. Jami’ar Mohaghegh Ardabili ta wallafa mujalla ta musamman 12, sannan zuwa yanzu ta karɓi baƙuncin taruka 53.

Martabar Jami’ar Mohaghegh Ardabili

A tsarin ranking na Times, a shekarar 2024 jami’ar Mohagegh Ardabili ta samu matsayi na 801-1000 , hakazalika a shekarar da ta gabata bayanai sun nuna cewa jami’ar ta samar wa kanta matsayi a 3 a cikin jami’o’in Iran, wanda hakan ya ɗaga darajarta zuwa cikin manyan jami’o’in duniya.

Karatu a Jami'ar Mohaghegh ArdabiliMakarantu

_ Faculty ofEngineering
_ Faculty of
Basic Sciences
_ Faculty of
Mathematical Sciences
_ Faculty of
Literature and Humanities
_ Faculty of
Social Sciences
_ Faculty of
Educational Sciences & Psychology
_ Faculty of
Agriculture and Natural Resources
_ Nemin Faculty of
New Technologies
_ Moghan Faculty of
Agricultural Sciences and Natural Resources
_ Meshkin Shahr Faculty of
Agriculture

Jadawalin Kuɗin Makarantar Jami’ar Mohaghegh Ardabili

A wannan jami’a ta Mohaghegh Ardabili, ɗalibai za su iya amfanuwa da hostel ta hanyar biyan kuɗi dala 64 a kowane term, dala 50 kuma na abinci. Haka kuma kuɗin kowane zango na koyon yaren farsi dala 60 ne.

Kwasa-Kwasai

_ Persian Language and Literature
_ English Language Teaching
_ Arabic Language and Literature
_ General Psychology
_ Archeology (prehistory/Islamic era/historical era)
_ Physical Education and Sports Science (sports physiology)
_ Geographical Sciences (urban planning/geomorphology/natural/climatology)
_ Theology and Islamic Sciences
_ Consultation
_ Handicrafts
_ Clinical Psychology
_ Tourism Management
_ Islamic Mysticism
_ Cellular and Molecular Biology
_ Organic Chemistry
_Applied Chemistry
_ Fundamental physics
_Nuclear Physics
_ Biology (animal science/plant physiology)
_ Pure mathematics (algebra/geometry/analysis)
_ Applied Mathematics (differential equations/numerical analysis)
_ Computer Science
_ Civil Engineering
_ Electrical Engineering
_ Mechanical Engineering
_ Architecture
_ Chemical Engineering
_ Computer Engineering
_ Agriculture (weed cultivation/ physiology of crop plants/ ecology of crop plants)
_ Pasture and Watershed Sciences
__Agricultural Engineering
_ Agricultural Mechanization
_ Livestock Production Technology
_ Plant Production Engineering
_ Irrigation Technology
_ Plant Breeding
_ Seed Science and Technology
_Da sauransu…
Ku sauke wannan fayil na ƙasa domin samun cikakken list ɗin kwasa-kwasai da matakan karatun wannan jami’a.

Kwasa-Kwasan Mohaghegh Ardablili University

Kwasa-Kwasan Mohaghegh Ardablili UniversityAbubuwan Alfahari

_ Kasancewa ɗaya daga cikin kason farko na jami’o’in da aka fi ambata a duniya, shekara biyu a jere (daga 2019)
_ Zaɓar ɗaya daga malaman wannan jami’ar a matsayin zakaran mai bincike na ƙasa
_ Jami’ar Mohaghegh Ardabili a karon farko ta shiga cikin jerin fitattun jami’o’i da cibiyoyin bincike na duniya waɗanda suka fi rubuce-rubuce.
_ Kasancewar jami’ar cikin fitattun jami’o’i masu tasowa a duniya, karon farko a 2021
_Da sauransu…

Ababen More Rayuwa

Wuraren kwanan da jami’ar Mohaghegh Ardabili ta tanadarwa ɗalibanta domin samun sauƙin karatu sun haɗa da:
Ɗakunan kwanan ɗalibai: ɗakuna masu gadajen ƙarfe 4, sama da ƙasa, da kayan bacci, kitchen, banɗaki, firiji, da kuma ɗakin kallo (ana ba ɗalibai idan akwai iyalai 10 aƙalla)


_ Suite masu zaman kansu: Gadajen ƙarfe 2 sama da ƙasa tare da kayan bacci, firiji, banɗaki, kitchen, babu ɗakin kallo.
Gidaje masu zaman kansu masu ɗakuna 2: Gadaje na ƙarfe 2 masu hawa biyu tare da kayan bacci, firiji, banɗaki, wurin wanka, da kitchen mai zaman kansa, babu TV.
Rukunin villa, gidaje masu ɗakuna 2, 3, ko 5: Gadajen ƙarfe masu hawa biyu tare da kayan bacci, firiji, wurin wanka, banɗaki, da kitchen. Babu Talabijin.

Kayan aikin Jami'ar Mohaghegh ArdabiliYanayin Wuri

Jami’ar Mohaghegh Ardabili na nan a unguwar Milad ta garin Ardabil, a titin Daneshga. Jami’ar tana kusa da wurare kamar Sarai Hotel, Jami’ar karatun likitanci ta Ardabil, Jami’ar Payamnoor, rukunin masaukai na Nestern, da kuma gidan abinci na Perproc.

Adireshin Jami’ar Mohaghegh Ardabili

Adireshi: Ardabil, titin Danesga, University of Mohaghegh Ardabili


Tambayoyin da aka yi game da karatu a jami’ar Mohaghegh Ardabili

  1. Shin ɗalibai ‘yan ƙasar Afghanistan za su iya yin karatu a jami’ar Mohaghegh Ardabili?
    A a, wannan jami’a bata karɓar ɗaliban Afghanistan.

Loading

Related Posts
Leave a Reply

Your email address will not be published.Required fields are marked *