Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Kerman University of Medical Sciences

Karatu a Kerman University of Medical Sciences

Loading

Garin Kerman na ɗaya daga cikin manyan garuruwan Iran, wanda ya zamo cibiyar likitanci sanadiyyar jami’ar Kerman University of Medical Sciences da kuma ayyuka masu wahala na dashen sassan jiki da akeyi a wannan cibiyar. Karanta wannan rubutu domin sanin sharuɗan jami’ar da kuma yin matsaya akan karatu a wannan jami’a ta Kerman University of Medical Sciences.

Gabatarwa

Jami’ar Kerman University of Medical Sciences da kamfus ɗinta na Khodgharan, tana gabatar da hidimomin kiwon lafiya da jinya ga al’umma baya ga harkokin karatunta. An assasa wannan jami’a ne a shekarar 1977, inda ta fara ayyukan ta da karɓar ɗalibai 50 a fagen likitanci a karon farko.
Wannan jami’a nada ɗalibai 6136, malamai 515 da mambobin fakwalti 557. Bincike ya nuna cewa, maƙaloli 2172  na ilimi a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida [maƙalolin mujalla 1047 da maƙalolin taro 1125] da maƙaloli 7873 na duniya, an bugasu ne a Kerman University of Medical Sciences, hakazalika ita ce mawallafiyar maƙala 10 na musamman. Zuwa yanzu, Kerman University of Medical Sciences  ta samu nasarar shirya manyan taruka guda 7.

Martabar Jami’a

Kerman University of Medical Sciences, karonta na farko na samun shiga tsarin ranking na Shanghai [tsarin ranking mafi inganci a duniya, wanda Jami’ar Shanghai Jiaotong dake ƙasar China ta buga karon farko a watan June na shekarar 2003] a fannin Public Health, ta samu matsayi na (3 zuwa 5) a jami’o’in cikin ƙasa, da kuma matsayi na (301 zuwa 400) a jami’o’in duniya. Baya ga haka, a yayin bayyana sakamakon Tsarin Ranking na Times, jami’ar ta samu matsayi na 801 zuwa 1000.

Karatu a Kerman University of Medical SciencesMakarantu

_Makarantar Medicine
_Makarantar Dentistry
_Makarantar Pharmacy
_Makarantar Allied Medical Sciences
_Makarantar Public Health
_Makarantar Nursing and Midwifery, Razi
_Makarantar Medical Information and Management
_Makarantar Iranian Medicine
_Makarantar Nursing, Zarand
_Makarantar Tissue Health

Cibiyoyin horo akan likitanci

_Asibitin Afzalipur
_Asibitin Shafa
_Asibitin Shahid Bahonar
_Asibitin Shahid Beheshti

Cibiyoyin Bincike

_Comprehensive Research Laboratory
_Neuroscience Research Center
_Physiology Research Center
_Hydatid Disease Research Center
_Medical Mycology and Bacteriology Research Center
_Nursing Research Center
_Center for Brain and Nerve Diseases Research
_Cardiovascular Research Center
_Pharmaceutical Research Center
_Research Center for Pharmaceutical Sciences and Cosmetic Products
_Leishmaniasis Research Center
_Health Technologies Development Center
_Environmental Health Engineering Research Center
_Infectious and Tropical Diseases Research Center
_Herbal and Traditional Medicine Research Center
_Liver and Gastroenterology Research Center
_Endocrine and Metabolism Research Center
_Shafa Hospital Clinical Research Base
_Clinical Research Base of Shahid Bahonar Hospital
_Clinical Research of Afzalipur Hospital
_Pathology and Stem Cells Research Center
_Research Institute for Future Research in Health
_Medical Informatics Research Center
_Health Service Management Research Center
_Health Research Center in Disasters and Emergencies
_Research Center for Social Factors Affecting Health
_Modeling Research Center in Health
_HIV Care Research Center and Sexually Transmitted Infections
_Oral and Dental Diseases Research Center
_Endodontology Research Center
_Research Center for Social Factors Affecting Oral Health

_Healthcare networks

_Health Center of Kerman City
_Health and Treatment Network of Arzuiye City
_Baft City Health and Treatment Network
_Bardsir Health and Treatment Network
_Raber City of Health and Treatment Network
_Raver Health and Treatment Network
_Health and Ttreatment Network of Zarand City
_Health and Treatment Network of Babak City
_Health and Treatment Network of Kohbanan City

Jadawalin   Kuɗin Makarantar Kerman University of Medical Sciences

Kuɗin makaranta na shekara ɗaya (a Dala)GroupSunan KwasFarashiTsawon Lokacin Karatu
Bachelor of Science (B.Sc)Duka Kwasa-Kwasai$3000Shekara 4
Master of Science(M.Sc)Marasa Practical$4000Shekara 2
Masu Practical$4500Shekara 2
Professional DoctorateDoctor of Medicine(M.D.)$5000Shekara 7 da rabi
Doctor of Dental Surgery (D.D.S)$5500Shekara 6
Doctor of Pharmacy (pharm.D)$5000Shekara 6
Bachelor of Medicine and Bachelor of Surgery (M.B.B.S.)$5000Shekara 5 da rabi
SpecialityResidency$6500Shekara 3 da rabi
Ph.D
FellowshipDuka Kwasa-Kwasai$7000Shekara 2 zuwa 4
Subspecialty

 

Sauran Kuɗaɗe (a dala)SunaBayaniFarashiNau’in biya
Karon farko daga airport zuwa makaranta (bisa buƙata)Idan an buƙata$10Sau ɗaya
Wurin kwana da AbinciAƙalla ɗaki 4 da abinci sau 3 a rana$100Duk wata
InsuranceLafiya$75Duk Shekara

Kwasa-Kwasan Kerman University of Medical Sciences

_Neonatal and Perinatal Medicine
_Endocrinology and Metabolism of Adults
_Dermatopathology
_Children’s Skin
_Cytopathology
_Ergonomics
_Old age Health
_Human Ecology
_Nursing
_Consultation in Midwifery
_Psychiatric Nursing
_Anatomical Sciences
_Clinical Biochemistry
_Physiology
_Medical Parasitology
_Human Genetics
_Medicinal Chemistry
_Anesthesia
_Orthopedics
_Psychiatry
_Obstetrics and Gynecology
_Ophthalmology
_General Surgery
_Emergency Medicine
_Radio Oncology
_Ear, Throat, Nose and Head and Neck Surgery
_Neurological Diseases
_Internal Diseases
_Pharmaceutical Sciences
_Management Sciences
_Molecular Medicine
_Dental Science
_Medical Informatics
_Pharmaceutical Nanotechnology
_Endodontics
_Restorative Dentistry
_Dental Prostheses
_Librarianship and Medical Information
Da sauransu.
Ku sauke wannan fayil domin samun bayanai akan kwas ɗin da kuke buƙata da matakin karatu.

Kwasa-Kwasan Kerman University of Medical Sciences

Kwasa-Kwasan Kerman University of Medical SciencesAbubuwan more rayuwa

Babban Laburare: Babban laburare kuma cibiyar ajiye documents na Kerman University of Medical Sciences na ɗaya daga cikin manyan laburare na ilimin likitanci a garin Kerman wanda aka assasa a shekarar 1986. Girman wannan laburaren murabba’in mita 800 kuma yana cikin ginin Abu Ali Sina dake makarantar Medical Engineering ta Afzalipur. A halin yanzu, wannan laburaren nada litattafai 29,911, thesis 8,337, documents na na’ura guda 380,011, da kuma na kallo da saurare guda 470.
A 2001, bayan haɗe laburaren Medical School da babban laburare, tun sanda ya fara aiki, babban laburaren ya sami isa ga sababbin bayanai na likitanci da ayyukan da suka shafi likitanci [da manufar haɓaka matakin wayar da kai akan kimiyya da haɓaka bincike da ayyukan bincike a fagen ilimin likitanci da makamantan fagage a cikin mafi ƙanƙantar lokaci] ta hanyar amfani da sabbin kayan aiki na laburare da sabbin fasaha domin aiwatar da ayyukan maziyartanta. Saboda haka, domin inganta ayyuka, ya sayi sabbin hanyoyin samun bayanai da kasussukan CD masu alaƙa da mujallolin likitanci da sabbin litattafan farisanci da na latin a wuraren baje kolin litattafai ciki da wajen ƙasa.
Hostel: Sashen kula da harkokin hostel shi keda alhakin samarwa ɗalibai da wurin kwana da kayayyakin walwala. Baƙin ɗalibai ma zasu iya amfani da waɗannan kayayyakin.
List ɗin wuraren kwana:
Na maza: Golestan, Shahid Heydari Moghadam, Sajjad
Na mata: Bostan 1, Bostan 2, 22 Bahman, Taha, Ummu Abiha
Ma’aurata: Ashiyane Madaran, Afzalipur

Kayan aikin Kerman University of Medical SciencesMuhalli:

Kerman University of Medical Sciences (jami’a kuma cibiyar koyarwa ta gaba da sakandare) na nan cikin garin Kerman a titin Ibn Sina. Wannan jami’a tana kusa da wurare da cibiyoyi kamar Masallacin Az-Zahra, Masallacin Al-Mahdi (ATF), Fuka Cafe, Masallacin Payambar Azam Pardize, da kuma Technical Examination Center for Light vehicles No. 2.

Adireshin Kerman University of Medical Sciences 

Adireshi: Babban titin Mustafa Khomeini, Titin Shahid Inayatullah Heydari, Heydari, Ibn Sina, Kerman.


Tambayoyin da ake yawan yi game da karatu a Kerman University of Medical Sciences

  1. Wasu takardu ake buƙata domin yin rajista a Kerman University of Medical Sciences?
    Passport, Hoto, Transcripts, Degree Certificate, CV, Motivation Letter, Recommendation Letter.
  2. Yaushe ne lokacin ɗaukar ɗalibai a wannan jami’a?
    A wannan jami’a, ana ɗaukar ɗalibai ne sau 1 a shekara kawai, cikin watan September jami’ar ke ɗaukar ɗaliban waje.
  3. Shin ɗaliban Iraq zasu iya yin transfer a wannan jami’ar?
    A’a

[neshan-map id=”13″]

Related Posts
Leave a Reply