Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Isfahan University of Technology

Karatu a Isfahan University of Technology

Loading

Ɗaya daga cikin abubuwa masu matuƙar muhimmanci ga ɗalibai shi ne, zaɓen jami’a da kwas ɗin karatu. A wannan rubutu za mu yi magana a kan karatu a jami’ar fasaha ta Isfahan da abubuwa daban-daban da suka shafi hakan. A wannan maƙala, mun kawo muku bayani akan makarantu, kuɗin makaranta, kuɗin hostel na wannan jami’ar, maƙalolin da ta wallafa, da kuma martabar jami’ar domin taimaka muku wurin yin zaɓinku. Ku kasance tare da mu a cigaban wannan rubutu.


Gabatarwa


Jami’ar fasaha ta Isfahan (Isfahan University of Technology) na ɗaya daga cikin jami’o’in fasaha mafi inganci na Iran. Ta fuskar girman wuri, ita ce jami’a ta farko a kaf jami’o’in ƙasar Iran. Harabar wannan jami’a kamar wani ƙaramin gari ne mai ɗauke da gine-gine da yawa a cikinsa. Daga cikin waɗannan gine-gine akwai wurin kwanan ɗalibai wanda zai iya ɗaukar mutum 5000, da gine-ginen gidajen malaman jami’a da ma’aikata. Hakazalika domin sahalewa ɗalibai da ma’aikata, wannan jami’ar ta samar musu da cibiyoyin sayyaya daban-daban.


An assasa jami’ar fasaha ta Isfahan ne a shekarar 1977. Jami’ar ta kasance sashe a cikin jami’ar fasaha ta Sharif a wancan lokacin, daga bisani bayan ɗan lokaci, ta fara gudanar da ayyukanta a ƙashin kanta.


A halin yanzu, wannan jami’a na da kwasa-kwasan karatu 194 a matakan digiri, mastas, da PhD inda kimanin ɗalibai 9051 ne suke karanta waɗannan kwasa-kwasai 194


Jami’ar na da membobin tsangayar ilimi 478, da kimanin ayyukan bincike da na masana’antu 610, tana kuma da makarantu da wuraren bincike 21.




Maƙalolin da aka wallafa a Isfahan University of Technology


Adadin maƙalolin kimiyya na cikin gida: maƙala 14915


Adadin maƙalolin ƙasa da ƙasa: maƙala 19246


Mawallafiyar mujalla 10 na musamman


Martabar Isfahan University of Technology


A nazari na ƙarshe da aka yi a matakin ƙasa da ƙasa, wannan jami’a tana matsayi na 901 – 1000 a tsarin ranking na Shanghai. Ta wani janibin kuma, jami’ar fasaha ta Isfahan ita ce ta 4 a jami’o’in Iran. A ranking na shekarar 2017, tsarin ranking na Leiden ya bayyana cewa jami’ar fasaha ta Isfahan ta ɗago da matsayi 42 bisa ga matsayinta na shekarar 2016, inda ta samu matsayi na 421 a cikin zaɓaɓɓun jami’o’i 902 na duniya, da kuma matsayi na 6 a jami’o’in Iran bisa la’akari da matakinta na ilimi.



Karatu a Isfahan University of Technology Wuraren bincike na jami’ar


• Avionics Research Institute
• Foulad Research Institute
• Research Institute of Water and Sewage
• Undersea Science and Technology Research Institute
• Research Institute of Nano Technology and Advanced Materials
• Information and Communication Technology Research Institute
• Biotechnology and Bioengineering Research Institute


Cibiyoyin koyarwa


• Central Library and Publications
• Information Technology Center
• Electronic and Open Education Center
• Technology and Communication with Industry
• APA Specialized Center
• Sheikh Bahai National Supercomputer Center
• Central Laboratory
• Innovation Management and Technology Commercialization
• Technical and Engineering Skills Training Center
• Soilless Cultivation Research Center
• Physical Education Center
• Center for Islamic Education and Persian Literature
• Language Center
• Pardis
• Entrepreneurship Center


Ginshiƙan Kimiyya


• The Radar Pole of the Country
• Sensor Pole and Green Chemistry
• Biotechnology Hub
• Technology Pole in the Steel Industry
• Risk Management and Natural Crises Pole
• Biotechnology and Bioengineering


Jadawalin Kuɗin Makarantar Isfahan University of Technology

Makarantu


• Mathematics
• Chemistry
• Physics
• Electricity and Computer
• Transportation
• Chemical Engineering
• Industries
• Natural Resources
• Mechanics
• Civil
• Agriculture
• Mining
• Materials
• Textiles


Kwasa-Kwasan Isfahan University of Technology Mujallun bincike na kimiyya


• Scientific Research Journal of Advanced Materials in Engineering
• Scientific Research Journal of Applied Ecology
• Iranian Scientific-Research Journal of Welding Science and Technology
• Iranian Physics Research Journal
• Journal of Production and Processing of Agricultural and Horticultural Products
• Scientific Research Journal of Applied Ecology
• Journal of Science and Techniques of Greenhouse Cultivation
• Journal of Plant Process and Function
• Journal of Water and Soil Sciences
• International Journal of Iron & Steel Society of Iran








Kayan aikin Isfahan University of TechnologyJerin kwasa-kwasan da ake gabatarwa a Isfahan University of Technology


A wannan sashe mun kawo muku list ɗin kwasa-kwasan da ake yi a jami’ar fasaha ta Isfahan domin ku nemi kwas ɗin da kuke buƙata.


Adireshin Isfahan University of Technology


Iran / Isfahan – Meidane Esteghlal – babban titin Isfahan University of Technology


Tambayoyin da aka yi game da jami’ar fasaha ta Isfahan




2. A wani ɓangare na garin Isfahan wannan jami’a take?
Jami’ar tana nan a Meidane Esteghlal – babban titin Isfahan University of Technology



3. A wasu matakai jami’ar take karɓar ɗalibai?
Jami’ar Fasaha ta Isfahan tana karɓar ɗalibai a duka matakankaratu na gaba da sakandire.

Loading


Related Posts
Leave a Reply

Your email address will not be published.Required fields are marked *