Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Sahand University

Karatu a Sahand University

Loading

Sahand University of Technology ɗaya ce daga cikin manyan jami’o’in fasaha na Iran. Domin sauƙaƙe ma ɗalibai masu shawarar fara karatu a wannan jami’a, a wannan maƙala za mu kawo muku bayanai da suka shafi wannan jami’a kamar tarihinta, kwasa-kwasan ta, abubuwan more rayuwa, nasarorinta, da sauransu.

Gabatarwa

Sahand University ita ce jami’ar fasaha ta farko bayan juyin musulunci na ƙasar Iran wadda an assasa ta ne a shekarar 1989 ƙarƙashin jagorancin Dr. Muhammad Ali Kinejad wanda yanzu memba ne a majalisar ƙoli ta juyin juya halin al’adu tare da Mohandis Mirhossein Musavi firaministan lokacin, da nufin horar da ƙwararru da jajirtattun ma’aikata waɗanda masana’antun ƙasar su ke buƙata, da kuma samar da damar aiwatar da ayyukan bincike da bunƙasa masana’antun ƙasar.

Jami’ar Sahand na da ɗalibai 3922, malamai 155, da membobin tsangayar ilimi 200. Bincike ya nuna cewa zuwa yanzu jami’ar ta wallafa maƙalar ilimi guda 4314 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida[540 مقاله ژورنالی و 3774 مقاله کنفرانسی], da maƙala 4250 a matakin ƙasa da ƙasa. Sahand University ta mallaki lambar yabo kuma ta wallafa mujalla 1 ta musamman. 

Martabar Sahand University

Shugaban Sahand University ya tabbatar da shigar jami’ar a tsarin ranking na Times inda a ranking ɗinsu na shekarar 2023 ta yi nasarar samun matsayi na 1001 – 1200 tsakanin fitattun jami’o’i 1662 daga ƙasashe 99 mabambanta na duniya,  da kuma matsayi na 10 a tsakanin jami’o’i 58 na Iran, da matsayi na farko a jami’o’in lardin Azarbaijan ta gabas.

Karatu a Sahand University

Makarantu

_ Faculty of Chemical Engineering
_Faculty of Electrical Engineering
_ Faculty of Materials Engineering and Metallurgy
_ Faculty of Petroleum Engineering
_ Faculty of Mathematics and Applications
_ Faculty of Mechanical Engineering
_ Faculty of Civil Engineering
_ Faculty of Medical Engineering
_ Faculty of Polymer Engineering
_ Faculty of Mining Engineering
_School of Basic Sciences

Cibiyoyin Bincike

_ Nano Structure Materials Research Center
_ Reactor and Catalyst Research Center
_ Research Institute of Polymer Materials
_ Device Analysis Research and Service Center
_ Center for the Growth of Technology Units
_ Earthquake Research Center
_ Science and Religion Studies and Research Center

 

Jadawalin Kuɗin Makaranta na Sahand University

A Sahand University of Technology, dole ne ɗaliban ƙasar waje na biyan kuɗi dala 50 kafin su fara ayyukan registration.

*Haka kuma Jami’ar Sahand na amfani da salon koyarwa na Research Training kuma suna da jarabawar kammalawa.

Kwasa-Kwasan Sahand University of Technology

_ Materials Engineering – the Identification and Selection of Engineering Materials
_Casting Material Engineering
_ Nanotechnology – the trend of nanomaterials
_ Metallurgical Engineering and Materials – welding orientation
_ Materials Engineering – corrosion and protection of materials
Materials Engineering – metal extraction trend
_ Oil Discovery
_ Tanks
_ Drilling
_ Exploitation
_ Energy Systems
_ Vehicle Power Train Systems
_Energy Conversion
_ Aerospace Structures
_ Electrical Engineering – control orientation
_ Applied Design _ Mechanics of Solids
_ Particle Physics
_ Plasma Physics
_ Dense Material
_ Pure Mathematics
_ Process
_ Applied Mathematics (optimization)
_ Geotechnical Engineering
_ Earthquake Engineering
_ Structural engineering
_ Electrical Engineering Majoring in Telecommunication Systems
_ Mining Engineering – mineral processing trend
_ Mining Engineering – Mineral Extraction
_Da sauransu…
Domin samun bayani a kan kwasa-kwasai da matakan karatu, ku sauke wannan fayil:

Kwasa-Kwasan Sahand University of Technology

Kwasa-Kwasan Sahand University
Abubuwan Alfahari

_ Zaɓar Dr. Ali Akbar Babalo a matsayin matashin masanin kimiyya na ƙasa, wanda cibiyar kimiyya ta jamhuriyar musulunci ta yi
_ Zaɓar fitaccen malami na ƙasa daga Sahand University.
_ Zaɓar malaman jami’ar sahand a matsayin fitattun masu bincike na lardi
_ Malaman jami’ar su 20 sun samu shiga ƙungiyoyin kimiyya da bincike na duniya da na ƙasa
_ Shigar jami’ar a sahun fitattun jami’o’in Iran a consortium na bunƙasa haƙar mai daga ma’adanai
_ Samun matsayi na farko a sashen kasuwannin ƙasa, da kuma samun matsayi na farko wurin ƙera kayan aikin ɗakin gwaje-gwaje da na masana’antu
_ Samun matsayi na farko a jarrabawar kammala karatun digiri na biyu da na uku ta ƙasar
_ Lashe design mafi kyau a bukin “Science to Action”
_ Zaɓar sashen koyarda motsa jiki na jami’ar sahand a matsayin fitacce na ƙasa baki ɗaya a ciki shekara 7, wanda ma’aikatar ilimi ta yi
_ Zaɓar ƙungiyar kimiyya ta Electrical-Control Engineering a fagen ayyukan bincike, a matsayin fitatta, a bukin ‘Harkat’

Ababen More Rayuwa

Babban Laburare: Wannan laburaren ya fara aiki ne lokaci guda da jami’ar ita kanta, sanda aka assasa ta a shekarar 1989. Babban hadafin ɗakunan karatu na jami’o’i shi ne samar wa ɗalibai, malamai, da masu bincike damar saduwa da tsararrun bayanai na kimiyya domin bunƙasa ilimi. An kafa babban laburaren karatu na jami’ar ne domin biyan buƙatun ɗalibai, malamai, da ma’aikata na karatu, nazari, bincike, da sauransu, kuma shi ke da alhakin tattarawa da tsara tarin litattafai, mujallu, labarai, rahotannin bincike, na gani da na saurare kuma a halin yanzu yana da membobi sama da 1600.
Wurin Kwana:  Sashen kula da harkokin wuraren kwana; Sahand University of Technology wanda ya tanadi masauki ga ɗalibai sama da dubu biyu, shi ke tafiyar da al’amuran hostel biyu na ɗalibai maza da na mata. Ana saukar ɗalibai ne tare da la’akari da matakin karatunsu, jinsinsu, da kuma garuruwansu. Motar jigila, tsarin abinci, wasu ne daga cikin irin hidimomin da jami’a take yiwa ɗalibanta.

Kayan aikin Jami'ar SahandYanayin Wuri

Sahand University of Technology na nan cikin garin Sahand a titin Farzangan, Qazi Tabatabaei. Wannan jami’a na kusa da wurare kamar Melika Complex, da wurin koyon tuƙi na Baharan. Tashar bus mafi kusa da jami’ar ita ce tashar hostel ɗin Mohebbi, hakan ya sauƙaƙe zirga-zirga ga ɗalibai da ma’aikata waɗanda basu da abun hawa na kansu.

Adireshin Sahand University of Technology

Adireshi: Tabriz, sabon garin Sahand, titin Farzangan, bolvare Shahid Ghazi Tabatabaei, titin Pajohesh 2, Sahand University of Technology


Tambayoyi game da karatu a Sahand University

  1. Ya yanayin biyan kuɗin makaranta yake a Sahand University?
    Wannan jami’a tana karɓar toman ne a matsayin kuɗin makaranta.

Loading

Related Posts
Leave a Reply

Your email address will not be published.Required fields are marked *