Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Koyon yaren farsi

Koyon yaren farsi

Loading

kamar sauran yaruka da ake magana da su a duniya, shi ma yaren farsi ana koyarda shi a wurare daban-daban. Ƙasar Iran ɗaya ce daga cikin manya-manyan cibiyoyin koyon yaren farsi ga waɗanda farsin ba yarensu bane, inda kowace shekara baƙi da dama daga ƙasashen waje waɗanda ke sha’awar koyon yaren su kan zo Iran su koyi yaren a makarantu ko cibiyoyin koyon yare masu zaman kansu.

A Iran akwai cibiyoyi da daman gaske da ake koyarda wannan yaren na farsi. Yawancin cibiyoyin suna da inganci kuma za ku iya samun ƙwarewa a wannan yaren ta hanyar yin kwasa-kwasansu. Cibiyar koyon yaren farsi ita ma kamar cibiyoyin koyon sauran yaruka, dole ta keɓanta da waɗansu abubuwa. Ingancin cibiyoyin yana da matuƙar mahimmanci don kuwa wasu daga cibiyoyin za su iya ɓata muku lokaci da kuɗinku saboda rashin tsari irin nasu. Wasu daga cikin ingattattun cibiyoyin koyon yaren farsi: Makarantar Dehkhoda, cibiyar koyon farsi ta jami’ar Shahid Beheshti, Tarbiat Modares, Isfahan, da sauransu. A ci gaban wannan rubutun, za mu gabatar muku da bayani akan waɗannan cibiyoyi.

Cibiyoyi da jami’o’i

 1. Dehkhoda Dictionary Institute, Tehran
 2. Tehran University of Medical Sciences
 3. Al-Zahra University
 4. Al Mustafa University
 5. Imam Khomeini International University
 6. Ferdowsi University of Mashhad
 7. Isfahan University
 8. Shahid Beheshti University
 9. Bu-Ali Sina University Hamedan
 10. Amirkabir University of Technology
 11. Alzahra University
 12. Allame Tabatabaei University
 13. University of Kurdistan
 14. Mazandaran University
 15. Shiraz University
 16. Payame Noor University
 17. Shahid Chamran University of Ahvaz
 18. Ahlul Bayt Univesrity
 19. Gilan University
 20. Ilam University
 21. Kharazmi University
 22. Tarbiat Modares University
 23. Islamic Azad University, North Tehran
 24. AJA University of Command and Staff
 25. Imam Reza International University
 26. Yazd University
 27. National Defense University
 28. University of Qom
 29. Semnan University
 30. University of Tabriz
 31. Hakim Sabzevari University
 32. Urmia University
 33. University of Kashan
 34. Razi University

A cigaban rubutunnan za mu gabatar muku da bayani a kan yadda ake koyarwa waɗannan cibiyoyi.

Dehkhoda language Institute

Makarantar yare ta Dehkhoda ta samar da sashe na musamman na yaren farsi don koyarda yaren ga waɗanda na yarensu bane. Wannan makarantar ta Dehkhoda tana daga cikin cibiyoyin da ke koyarda yaren na farsi a dunƙule ga kowa da kowa, sannan kuma a keɓance ga waɗanda suke son koyon yaren saboda wani hadafi nasu, tana taimakawa mutanen da ke son koyon yaren a kowane irin mataki suke buƙata ta hanyar gabatar musu da azuzuwan tattaunawa cikin salo na zamani.

A wannan makarantar, ana gabatar da azuzuwan koyon farsi a azuzuwa da kuma online (ta intanet). Ana gabatar da azuzuwan online ne a dandamali mafi inganci sannan akwai hanyoyin sadarwa na sauti da na kallo daga ko ina a faɗin duniya. Ana sa ido da nazari a kan azuzuwan yare na wannan makaranta akai-akai inda malamai ke gabatar ma department da rahoton kowane darasi da suka gabatar a aji.

Azfa International Center of Shahid Beheshti University

Wannan cibiyar tana ƙarƙashin kulawar jami’ar Shahid Beheshti kuma an fara ayyukan assasa ta ne a farkon shekarar 2011, a department ɗin Persian Language and Literature. Cibiyar koyarda yaren farsi ta jami’ar Shahid Beheshti ta fara aikinta ne tare da haɗin gwiwar cibiyar Bonyade Sa’adi bayan kammala daurar ƙarin ilimin yare da adabin farsi karo na 82, inda ta karɓi lasisi a watan Oktoban shekarar 2015. Cibiyar na karɓar masu sha’awar koyon yaren na farsi, daga ko’ina a faɗin duniya. Azuzuwan yare a wannan cibiyar na tsawon wata shida zuwa tara ne. Darussan da ake yi tsawon wannan lokacin sun haɗa da karatu, sauraro, magana, nahawu, da rubutu.

Irin karatun da ake yi a wannan cibiyar ya dace da kowasu irin mutane daga kowace irin ƙasa. Malaman da ke koyarwa a wannan cibiyra sun taka matakin karatu mai kyau sannan kuma suna da gogewa sosai a fannin koyar da wannan yaren na farsi, kuma suna amfani da hanyoyin zamani wurin gudanar da ayyukan nasu na koyarwa. Har ila yau, akwai kayan sauti da na kallo a azuzuwan wannan makarantar haɗi da intanet.

Cibiyar koyon yaren farsi ta jami’ar Tarbiat Modares

Jami’ar Tarbiat Modares tare da haɗin gwiwar malamai da ƙwararrunta da kuma taimakon sababbin fasahohin koyarwa na zamani, ta tsara hanyoyin koyarda yare, gwajin ƙwarewa a yare, da kuma ayyukan koyarwa mafi inganci don mutanen da ke sha’awar koyon wannan yare na farsi. Bayan kammala daurorin yaren farsi waɗanda suka dace da kwasa-kwasansu, ɗaliban da suka koyi yaren farsi a wannan cibiyar za su iya fara karatu a kowane fanni a matakin digiri, masters, ko PhD. Haka kuma ana gabatar da darusan yaren farsi ne a azuzuwa, ko online (daga nisa), ko duka hanyoyin biyu. An shirya tsarin koyon farsi na wannan cibiyar ne da tsarin CEFR da ACTFL.

Cibiyar koyon yaren farsi ta jami’ar Al-Mustafa

Ita ma ɗaya ce daga cikin cibiyoyin da ke koyar da wannan yaren na farsi. A wannan cibiyar ma ana gabatarda karatun ne a azuzuwa ko kuma ta yanar gizo (online) sannan kuma ana amfani da litattafan koyon farsi ne waɗanda jami’ar ta Al-Mustafa ta wallafa da kanta.

Cibiyar koyon yaren Farsi ta jami’ar Isfahan

An assasa wannan cibiyar koyon yare ta Jami’ar Isfahan ne a shekarar 1984 kuma ya fara ayyukansa ne a ƙarƙashin kulawar ofishin haɗin gwiwar kimiyya da harkokin ƙasa da ƙasa na jami’ar. Tsawon wannan lokaci, cibiyar ta karɓi ɗalibai masu koyon yaren farsi daga ƙasashe daban-daban kamar America, England, Belgium, Denmark, Russia, Sweden, Norwich, Holand, da sauransu. Wannan cibiyar ta gabatar da daurori da dama ga ɗalibai da malamai masu koyarda yaren, sannan baya ga koyarda su yaren na farsi, tana basu damar gogewa da sanin al’adu da tarihin ƙasar Iran. Yanzu haka cibiyar na aiki tare da ma’aikatar ilimi da binciken fasaha, majalisar harkokin ƙasashen waje, ma’aikatar kiwon lafiya da jinya, da sauran ma’aikatu da jami’o’i domin shirya daurorin koyon yaren farsi na gajeren zango da na dogon zango (na sati biyu zuwa na shekara 1).

Cibiyar koyon yaren farsi ta Jami’ar Allameh Tabataba’i

Jami’ar Allameh Tabataba’i ta assasa cibiyar koyar da yaren farsi bisa amincewar hukumar gudanarwa ta jami’ar da kuma izinin ma’aikatar ilimi. Cibiyar tana cikin garin Tehran. A wannan cibiyar, ana amfani da hanyoyin koyarwa na zamani don gudanar da daurorin koyon yaren farsi na gajeren zango da na dogon zango, a cikin azuzuwa da kuma online (daga nisa).

Har ila yau, cibiyar tana la’akari da ɗalibai da malamanta wurin shirya ƙarin wasu daurorin farsi, kamar daurar koyon yaren farsi ta gama-gari, daurar koyon farsi ta musamman, daurar hanyoyin koyar da yaren farsi (ga malamai kenan).

Cibiyar koyon yaren farsi ta jami’ar Ferdowsi ta Mashhad

An assasa wannan cibiya ta koyon yaren farsi ne a watan September na shekarar 2013. Wannan cibiya wadda ɗaya ce daga cikin sassan wannan jami’a ta Ferdowsi, tana da azuzuwa guda 25 masu ɗauke da kayan sauti da na kallo, ɗakin taro, ɗakin karatu, da laburare. Baya ga haka, daga cikin abubuwan da suka ƙara ma wannan cibiya armashi akwai kusancinta da zaurukan wasanni, sannan kuma tana da wurin cin abinci.

Zuwa yanzu wannan cibiyar ta yaye ɗaliban farsi 21000 daga ƙasashe 38 mabambanta. Akwai malamai 61 yanzu haka a cibiyar.

Cibiyar koyon yaren farsi ta Jami’ar Al-Zahra

Wannan cibiyar ta koyar da yaren farsi ga waɗanda ba su jin yaren ta jami’ar Al-Zahra (s) ta fara ayyukanta na tattara kayan aikin da take buƙata na littafai, na’urori, samar da salon ɗaukar ɗalibai, ɗaukar malaman farsi, da sauran shirye-shirye a watan January na shekarar 2016, inda ta samu nasarar karɓar lasisin ma’aikatar ilimi a watan November na shekarar 2016. Saidai yana da kyau ku san cewa tana da tsarin karatun farsi a cikin azuzuwa ga mata ne kawai, sai kuma na online (daga nesa) ga mata da maza. A taƙaice dai, zuwa yanzu bata da azuzuwan karatu na maza (saidai ta yanar gizo).

Sharhi

An tanadi duka waɗannan cibiyoyin ne domin koya wa ɗalibai daga ko’ina a faɗin duniya yaren farsi. Domin karatu a kowane fanni a ƙasar Iran, Engineering, Medicine, Qur’an, da sauran kwasa-kwasai, tawagarmu na iya bakin ƙoƙarinta wurin sauƙaƙe muku kaiwa ga hadafofinku.

Related Posts
Leave a Reply