Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Yasouj University

Karatu a Yasouj University

Loading

Garin Yasouj shi ne tsakiyar lardin Kohgiluyeh da Boyer-Ahmad, kuma gari ne a Boyer-Ahmad. Garin Yasouj yana a gangaren Zargos, a ƙololuwar tudun Dana mai tsayin mita 1870. Ana kiran mutanen wannan garin da suna ‘Ler’. Akwan cibiyoyin karatu da jami’o’i 16 a wannan gari, jami’ar gwamnati ta Yasouj na ɗaya daga cikin su. Sharuɗan admission da karatu a wannan makaranta, shi ne batun da zamu tattauna a wannan rubutu. 

Gabatarwa

Jami’ar Yasouj jami’a ce ta gwamnati wadda ke garin Yasouj, lardin Kohgiluyeh da Boyer-Ahmad. An assasa wannan jami’a a shekarar 1982. A shekarar farko bayan assasa jami’ar, ta kasance ne a ƙarƙashin jami’ar Shiraz, kafin ta koma jami’a mai zaman kanta a shekarar 1996. Jami’ar Yasouj ita kaɗai ce jami’ar gwamnati wadda ta cika sharuɗa a wannan lardi.
A halin yanzu akwai ɗalibai 6000, malamai 350, da membobin tsangayar ilimi 300 a jami’ar. Bincike ya nuna cewa zuwa yanzu jami’ar ta wallafa maƙalar ilimi 3558 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida[1180 مقاله ژورنالی و 2378 مقاله کنفرانسی], ta kuma wallafa maƙala 2675 a matakin ƙasa da ƙasa. Jami’ar ta Yasouj ta mallaki lambar yabo, haka kuma ta wallafa mujalla 3 na musamman. Har ila yau, jami’ar ta shirya taruka 12 zuwa yanzu.

Martabar Jami’a

Tsarin ranking na Times ɗaya ne daga cikin amintattun tsarukan ranking da ake da su a duniya, wanda ya fara ayyukansa na martaba jami’o’in duniya karon farko a shekarar 2013. A taron martaba jami’o’in yankin Asia da aka yi a 2021, jami’o’i 47 ne suka samu halarta daga Iran, inda 7 daga cikin su suka samu shiga sahun fitattun jami’o’i 100 na yankin Asia. A shekarar da ta gabata kuma jami’o’in Iran 40 ne suka samu shiga.
Yasouj University ta samu matsayi na 401 – 500 a fannonin Engineering Sciences, General Engineering, Electrical Engineering, Mechanical and Aerospace Engineering, Civil Engineering, da Chemical Engineering.

Karatu a Yasouj University

Makarantu

_Faculty of Literature and Humanities
_School of Basic Sciences
_Faculty of Technical Engineering
_School of Agriculture
_Faculty of Natural Resources and Forestry
_Faculty of Oil and Gas a garin  Gachsaran
_College of Industry and Mining a garin  Cheram

Ƙungiyoyi da Cibiyoyin Bincike da Nazari

_Natural Resources Research Institute
_Center for Social Studies and Native Linguistics
_Medicinal Plants Research Institute
_Free and Virtual Education Center
_Observatory

Kuɗin Makarantar Yasouj University

Kuɗin hostel na duka matakan karatu a wata ɗaya
Wurin kwanan ɗalibai masu aureDala 33
Wurin kwanan marasa aure (ɗakunan mutum biyu)Dala 22
Wurin kwanan marasa aure (ɗakunan mutum 4)Dala 17

 

Kuɗin abincin ɗalibai a duka matakan karatu, na mutum ɗaya
BreakfastDala 0.5
Abincin rana da na dareDala 2

Kwasa-Kwasan Yasouj University

_Political Sciences
_Literature
_Psychology
_Economy
_Educational Science
_English Language
_Theology
_Philosophy
_History
_Geography
_Rural Construction
_Welding Mechanics
_Road Infrastructure Construction and Mechanics
_Water and Gas Supply Facilities
_ Chemical Engineering
_Materials Engineering
_ Electrical Engineering
_ Computer Engineering
_Agricultural Engineering – Animal Sciences
_ Agricultural Engineering – Farming and Plant Breeding
_Plant Medicine
_Forestry, Pasture and Watershed Management
_Agricultural Entomology
_Soil Science
_Plant Pathology
_Rural Development
_Forestry
_Animal Science
_Nematodology
_Animal Gene Interbreeding
_Promotion of Agriculture and Science and Technology
_Physiology of Agricultural Plants
_Polymer
_Applied Chemistry
_Welding Mechanics
_Mathematics
_Physics
_Chemistry
_Biology
_Statistics
_Da sauransu
Ku sauke wanna fayil na ƙasa domin samun cikakken list na kwasa-kwasai da matakan karatu.

Kwasa-Kwasan Yasouj University

 

Kwasa-Kwasan Yasouj UniversityAbubuwan Alfahari

_Shiga list ɗin manyan jami’o’i 100 na yakin Asia
_Shiga jerin fitattun jami’o’i  26 masu tasowa na Iran, da kuma jerin 475 na duniya
_Samun matsayi na 2 ta hanyar wallafe-wallafen ilimi na ɗalibin Jami’ar Yasouj a bukin wallafe-wallafen ɗalibai na ƙasa karo na 7
_Da sauransu…

Yanayin Wuri

Jami’ar Yasouj tana unguwar Zir Tel a titin Zir Tel, titin Daneshga, Golzar, garin Yasouj. Ta fuskar yanayin wuri, jami’ar na kusa da wurare kamar Samiragh Sandwich, gidan gwamnati na yankin Kohgiluyeh, Babban Post Office, Yasouj Jahangardi Hotel, da kuma Ghadami Decoratiɓe Group.

Adireshin Yasouj University

Adireshi: Yasouj University, titin Daneshju, Yasouj Iran.


Tambayoyin da aka yi game da Yasouj University

  1. Ko Yasouj University na da wurin kwanan ɗalibai masu iyali?
    Eh, akwai masaukin ɗalibai masu aure amma sai ɗaliban PhD ko sama da haka ake ba, a sauran matakai, sai ɗalibai masu ƙoƙari.

[neshan-map id=”34″]

Related Posts
Leave a Reply