Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Kashan

Karatu a Kashan

Loading

Garin Kashan, matattarar wayewa da al’adun Iran, wanda aka fi sani da ‘Darul Muminin’, birnin furanni da wardi, birnin gidaje da wuraren tarihi, kuma hedikwatar kafet na duniya wanda ke yammacin lardin Isfahan a tsakiyar tsaunukan Karkas a Natanz, kuma tsakiyar hamadar Iran. A wannan rubutun, mun yi nufin kawo muku bayani da sharhi a kan yanayin al’adu, karatu, ɗabi’a, yawon buɗe ido, da sauransu na wannan gari na Kashan.

Karatu a Kashan

Kashan

Kashan (Ki Ashian yana nufin wurin zaman masu mulki) nan ne asalin farkon wayewa a duniya wato Silk, wanda ya kai shekaru 7000 wanda ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin wayewar farko da aka samu a cikin birane. wannan garin, yana da gona mai girman hekta 2700 wanda hakan ya sa ya zama kan gaba wurin noman furen ‘Gol Mohammadi’, inda kowace hekta ɗaya ke samar da ton 4 na Gol Mohammadi. Kashan na ɗaya daga cikin garuruwa masu yawan jama’a a lardin Isfahan, akwai kimanin mutum 305000 a garin.
Wannan gari yana da yayani daban-daban: Yanayi irin na wurare masu tsaunuka, yanayin hamada (yankunan hamada a arewaci da gabacin garin, yankunan tsaunuka a ɓangaren kudu da yamma na wannan gari).
Al’adun da aka kiyaye a cikin shekarun da suka gabata su ne bikin ruwan fure (farawa daga farkon watan Mayu kuma yana ci gaba har zuwa karshen watan Yuni), masu wankin kafet na Mashhad, Ardahal (wanda ake gudanarwa a ranar Juma’a ta biyu a watan Oktoba), da Nakhel Gardani (wani biki na addini a ranar Ashura, wanda ake ɗaukar sanda a kan titunan garin a matsayin alamta akwatin gawar Imam Husaini (AS). Duk waɗannan bukukuwan jama’a sun kiyaye su taswon shekarun da suka gabata kuma ana ci gaba da gudanar da su da kyau a ayyanannun ranaku. Tsarabar wannan gari ta haɗa da kafet, shayin Neshalji, kukis, Haji Badami da Gulab Qamsar. Abincin gargajiya na Kashan sun haɗa da; Qeime rize, kufte chagndar, gosht adas badamjan, nama da waken soya tsimamme, nama da kabeji, kabewa, shinkafa lentil da zabibi, da kuma Ashkeneh.
Kashan ƙaramin gari ne, amma masu yawon bude ido za su iya amfanuwa. Har ila yau, akwai wuraren zirga-zirga kamar filin jiragen sama, jirgin ƙasa da tashar mota.


Cikakken bayani game da Kashan

Karatu

Amintattun cibiyoyin koyarwa na wannan gari su ne Kashan University of Medical Sciences da kuma University of Kashan. Domin samun ƙarin bayani, za ku iya komawa ga rubutun Karatu a Kashan University of Medical Sciences da kuma Karatu a University of Kashan.

Jami'o'in Kashan

Nishaɗi da wuraren yawon buɗe ido

A duk lokacin da aka ambaci sunan ‘Kashan’, saɓanin yadda mutane suke tunani cewa garin ya taƙaitu da abubuwan tarihi da al’adu ne kawai, wannan gari shi ma yana da yanayi na ɗabi’a mai jan hankali. Akwai abubuwa 333 a Kashan da suke cikin jerin abubuwan (muhimmai) da aka yi ma rajista na ƙasa, hakazalika an saka ‘Bagh Fin’ cikin list ɗin UNESCO na duniya a shekarar 2009. ‘Bagh Fin’ ɗaya ne daga cikin muhimman abubuwa kuma masu jan hankali na yawon buɗe ido wanda a ƙasance ma ya shahara.
_Abyaneh Village
_Abu Zaid Abad Desert
_Khane Abbasian
_Bagh Fin
_The Underground City of Nooshabad
_Niaser Waterfall
_The Historical House of the Tabatabais
_Silk Hill
_The Historical House of Boroujerdis
_Timcheh Amin al-Dawlah
_Karkas Mountain
_Agha Bozor Mosque and School
_Hamame Soltan Amir Ahmad
_Harpak Fire Temple
_Chartaghi Niaser (Fireplace of Niaser)
_Historic House of Ehsan
_Joshghan Qali
_Museum of Toys and Marquees
_Jalali Castle and Seljuk Fence
_Khane Qadiri
_Khane Bakuchi
_Da sauransu…

Yawon buɗe ido a Kashan

Cibiyoyin magani da asibitoci

_Asibitin Naqavi
_Asibitin Shahid Beheshti
_Asibitin Ayatollah Yathribi
_Karganjad Educational and Therapeutic Medical Center
_Ikhwan Special Clinic
_Matini Hospital
Da sauransu

Hotal Hotal

_Sabaghian Hotel
_Amirkabir Hotel
_Shirin Apartment Hotel
_Khaneraz Hotel
_Hotel Yasmin Rahab
_Baba Afzal Hotel
_Khademi Hotel
_Negarestan Hotel
_Saraye Naqi Khan Hotel
_Aryana Hotel
_Wanda Hotel
_Amirza Hotel
_Fallahi Hotel
_Manouchehri Hotel
_Sarae Kasian Hotel
_Khane Amiriha Hotel
_Khane Morshidi Hotel
_Giwak Hotel
_Da sauransu…

Ɗakunan Karatu

_Faiz Kashani’s Library
_Zarabi Library
_Ali Ibn Imam Muhammad Baqir Library
_Ayatollah Sabori Library
_Library of National Artifacts Association
_Meraj Al-Salehin Cultural and Artistic Center
_Central Library
_Amirkabir Library
_Deni Library
_Ayatollah Gharavi Library
_Abolreza Library
_Etrat Library
_Da sauransu…

Cibiyoyin Kasuwanci

_Safavie Bazaar
_Sefid Commercial Complex
_Sabz Commercial Complex
_Shafaq Commercial Complex
_Kashan Mall (Vendai Ki Ashian)
_Saif Plaza
_Jom’e Bazaar
_Bazaar
_Da sauransu…

Related Posts
Leave a Reply