Lardin Isfahan kamar sauran lardin Iran, shi ma yana da jami’o’i mabambanta. Tana ɗaya daga cikin cibiyoyin ilimi da jami’o’i 67 na garin Isfahan kuma a wannan rubutun zamu duƙufa wajen bayani akan karatu a Isfahan University of Medical Sciences.
Gabatarwa
Isfahan University of Medical Sciences [wadda aka assasa a shekarar 1946] jami’ar gwamnati ce kuma tana ƙarƙashin kulawar hukumar lafiya, jinya da karatun likitanci [ita ce hukumar da ke sa ido akan cibiyoyin kiwon lafiya, haka kuma ɗaya daga cikin ayyukan wannan hukuma shi ne tafiyar da jami’o’in karatun likitanci] a lardin Isfahan baya ga koyarwa da bincike, jami’ar ta bazama wurin ayyukan kiwon lafiya da jinya ga al’umma.
Zuwa yanzu akwai ɗalibai 8870, malamai 830, da mambobin kwamitin ilimi guda 890 da suke aiki a wannan jami’a. Isfahan University of Medical Sciences ita ce mamallakiya kuma mawallafiyar mujalloli na musamman guda 5. Har ila yau, an samo maƙalolin ilimi guda 4662 a wallafe-wallafe da taruka na cikin gida, da kuma karɓaɓɓun maƙaloli a matakin ƙasa da ƙasa guda 24893 daga wannan jami’a.
Martabar Jami’a
Isfahan University of Medical Sciences a tsarin ranking na Times na shekarar 2022, ta samu matsayi na biyu a tsakanin jami’o’in karatun likitanci na Iran, matsayi na 1000 zuwa 800 a jami’o’in duniya, wanda daga cikin manufofin wannan tsarin akwai kira zuwa ga musharaka da aiki gama-gari a duka ƙasashen duniya da suka cigaba, da waɗanda ke yunƙurin cigaba domin ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki akan sauye-sauyen yanayi da albarkatun ƙasa, kamar: Yanayi, tekuna, dazuzzuka, yaƙi da talauci da sauran matsaloli, cigaban karatu da kiwon lafiya, rage rashin daidaito, da ƙarfafa tattalin arziki.
Makarantu
_Makarantar Medicine
_Makarantar Pharmacy
_Makarantar Dentistry
_Makarantar Nursing & Midwifery
_Makarantar Allied Medical Sciences
_Makarantar New Technologies
_Makarantar Public Health
_Makarantar Rehabilitation
_Makarantar Management and Information
_Makarantar Nutrition and Food Sciences
Jadawalin kuɗin makarantar Isfahan University of Medical Sciences da sauran kuɗaɗe
Kuɗin Makarantar Isfahan University of Medical Sciences na Digiri da Masters | Sunan Kwas | Tsawon Lokacin Karatu | Kuɗin Makaranta |
---|---|---|---|
Doctor of Medicine(M.D) | Shekara 7 | 4700 | |
Doctor of Dentistry (D.M.D) | Shekara 6 | 4700 | |
Doctor of Pharmacology (Pharm.D) | Shekara 5 zuwa 6 | 4700 | |
Surgery M.B.B.S | Shekara 5 | 4700 | |
Dentistry B.D.S | Shekara 4 zuwa 4.5 | 4700 | |
Postgraduate of Pharmacology M.Pharm | Shekara 4 zuwa 4.5 | 4700 | |
Digirin Farko (BSc) | Shekara 4 | 2500 |
Kuɗin Makarantar PhD (a Dala) | Sunan Kwas | Tsawon lokacin karatu | Kuɗin Makaranta |
---|---|---|---|
Kwasa-Kwasan Masters M.Sc | Shekara 2 zuwa 3 | 3000 | |
Kwasa-Kwasan Ph.D | Shekara 3 zuwa 5 | 4000 | |
Speciality | Shekara 3 zuwa 5 | 5000 | |
Specilaty(dentistry) | Shekara 3 zuwa 5 | 11000 | |
Subspecialty | Shekara 2 zuwa 3 | 5000 |
Farashin Kuɗin Makaranta (a Dala) | Nau’i | Farashi | Nau’in biya |
---|---|---|---|
Rajista | 50 | Sau ɗaya | |
Inshorar Ɗalibi | 50 | Duk Shekara | |
Inshorar Ahalin Ɗalibi | 15 | Duk Shekara, akan kowane mutum ɗaya | |
Ajin Koyon Farsi (idan akwai buƙata) | 300 | Ajin ƙasa zuwa babban aji |
Kwasa-Kwasan Isfahan University of Medical Sciences
_General Practitioner
_Dental surgery
_Pharmacology
_Nursing
_Midwifery
_Surgery Room
_Environmental Health
_Microbiology
_Anatomical Sciences
_Parasitology
_Mycology
_Immunology
_Physiology
_Librarianship and Medical Information
_Bioelectric Engineering
_Biomaterials Engineering
_Biostatistics
_Epidemiology
_Health Education and Health Promotion
_Nutrition and Food Science
_Food safety and Hygiene
_Physiotherapy
_Speech Therapy
_Artificial Organs and Assistive Devices
__Health in Emergencies and Disasters
__Reproductive Health
_Health Service Management
__Iranian Traditional Medicine
__Medical Imaging Technology
_Pharmaceutical Nanotechnology
_Industrial Pharmacy
_Da sauransu
Domin samun cikakken bayani game da kwasa-kwasai da matakan karatu, ku sauke wannan fayil.
Kwasa-Kwasan Isfahan University of Medical Sciences
Wurare da Santocin Bincike
_Cardiovascular Research Center
_High Blood Pressure Research Center
_Cardiovascular Invasive Procedures Research Center
_Cardiac Rehabilitation Research Center
_Applied Physiology Research Center
_Heart Failure Research Center
_Children’s Hereditary Diseases Research Center
_Children’s Growth and Development Research Center
_Enviromental Research Center
_Medical Education Research Center
_Musculoskeletal Research Center
_Food Security Research Center
_Dental Implants Research Center
_Eye Diseases Research Center
_Infectious and Tropical Diseases Research Center
_Kidney Disease Research Center
_Metabolic Liver Diseases Research Center
_Bioinformatics Center
_Biosensor
_Medical Image and Signal Processing Center
_Anesthesiology and Special Care Research Center
_High Blood Pressure Center
_Skin and Skin Research Center
_Clinical Toxicology Research Center
_Psychosomatic Research Center
_Cleft Lip and Palate Research Center
_Emergency Medicine Center
_Hospital Infection Research Center
_Neuroscience Center
_Cibiyar Binciken Pharmaceutical Sciences
_Behavioral Science Research Center
_Endocrine and Metabolism Center
_Research Center for Social Factors Affecting Health
_Center for Information Technology in Health Affairs
Asibitoci
_Asibitin Isa Bin Maryam
_Asibitin Al-Zahra
_Asibitin Amin
_Asibitin Kashani
_Omid Medical-Educational Center
_Chamran Heart Hospital
_Faez Hospital
_Asibitin Farabi
_Asibitin Noor
_Asibitin Yara
_Asibitin kula da Ƙuna da Hatsari na Isfahan
Abubuwan Alfahari
_Samar da kwas ɗin Mannagment Health Information a matakin Ph.D
_Samun matsayi na 3 a tsarin ranking na Ra’ad
_Fara kwas ɗin Emergency Nursing matakin HND a Isfahan University of Medical Sciences
_Fara kwas ɗin Tissue Engineering matakin PhD a Isfahan University of Medical Sciences
_Samun babban matsayi na Cibiyar Nazarin Kiwon Lafiya da Cigaban Ilimi na Isfahan University of Medical Sciences a cikin takardar shaidar ƙasa
_Fara kwas ɗin Geriatric Health matakin Masters a Isfahan University of Medical Sciences
_Ƙaddamar da kwas ɗin Epidemology a Isfahan University of Medical Sciences
_Yarjejeniyar kan daidaiton haɓaka ilimin likitanci a yankin Haft Amashi na ƙasar (mataki na biyu da na uku)
_Samun matsayi na biyu da Isfahan University of Medical Sciences ta yi a gasar Olympiad ta ɗalibai karon farko.
_Buɗa wurin kwana na Baharestan saboda ɗaliban ƙasashen waje
_Karrama Isfahan University of Medical Sciences a bukin ilimi Shahid Motahari karo na 14.
_Da sauransu
Abubuwan more rayuwa
ِHostel: Wurin kwanan maza na Baharestan, wanda an yi tanadinsa musamman domin ɗaliban waje, an buɗe shi a gaban VC na kwamitin koyarwa, bunƙasawa da tafiyar da albarkatun jami’a, tare da sauran wakilai [tare da manufar jan hankalin ɗaliban waje]. Wannan hostel mai darajar kimanin riyal biliyan 40, yana da girman murabba’in mita 1800, yana da hawa 3 da sararin ɗaukar ɗalibai 150, kowane hawa yana da ɗakuna 11 na mutum 2 da zakuna 4 masu ɗaukar mutum 5. Har ila yau, mai baiwa shugaban sashen al’adu na ɗalibai shawara na jami’ar Isfahan University of Medical Sciences ya sanar da sayen wasu hostel guda 4 na ɗalibai.
Laburare:
_ Library of Literature and Human Sciences [ya fara aiki a shekarar 1998]
_Babban laburare [ya fara aiki a shekarar 1969 kuma a halin yanzu yana da tarin litattafai masu daraja na farsi da latin da litattafan bincike, taska ta tsofaffi da sababbin mujalloli da jaridu, takardu da rubuce-rubucen hannu, da sauran documents na na’ura.]
_Laburaren Foreign Languages and Physical Education [an buɗa shi a shekarar 1975 kuma yana nan a hawa na farko na Makarantar Foreign Languages]
_Azadegan Library of Economics,Ttechnology and Engineering [an buɗa shi a shekarar 1976 kuma ya fara aiki da litattafai sama da dubu ɗaya]
_Laburaren Hostel ɗin mata na Shohada [an buɗa shi cikin hostel ɗin Shohada a shekarar 1995, yana ɗauke da kwafi 10,655 na litattafan larabci da farisanci da kwafi 94 na litattafan latin]
Laburaren Hostel ɗin maza na Shahid Bahnar [ An buɗa shi a shekarar 1995 cikin hostel na Shahid Bahnar Dormitory, yana ɗauke da kwafi26152 na litattafan farsi da kwafi 210 na litattafan latin.]
Muhalli:
Isfahan University of Medical Sciences (University and Institute of Higher Education) tana cikin grain Isfahan a Titin Hazarjarib, Ibn Sina, kuma tana kusa da Faculty of Medicine, Teriya Zaytoun Faculty of Medicine, Ɗakin taruka na Isfahan University of Medical Sciences, Medical Image and Signal Processing Research Center da kuma Farzangan Sports Complex.
Adireshin Isfahan University of Medical Sciences
Adireshi: Titin Hazar Jarib, Isfahan University of Medical Sciences and Health Services, Central Headquarters
Tambayoyin da ake yawan yi dangane da karatu a Isfahan University of Medical Sciences
- Wasu takardu ake buƙata domin yin rajista a wannan jami’a?
Passport, Hoto, Script, Certificate, CV, Motivation Letter, Recommendation Letter. - Shin wannan jami’ar tana karɓar ɗalibai a duka zanguna biyu na karatu?
Eh, a duka zango biyu February da September tana karɓar ɗalibai.
[neshan-map id=”3″]