Jami’ar Maragheh (University of Maragheh) cibiyar koyarwa ce ta gaba da sakandare kuma ta gwamnati, wadda ke yankin Azerbaijan ta Gabas. Ku kasance tare da mu domin samun bayanai a kan karatu a wannan jami’a.
Gabatarwa
University of Maragheh, jami’a ce da ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimi, wadda aka assasa a gabacin garin Maragheh, a shekarar 1987. Wannan jami’a na karɓar ɗalibai a duka matakan karatu, a kowace shekara. Akwai ɗalibai 3700, malamai 115, da membobin kwamitin ilimi guda 134 a wannan jami’a.
Jami’ar ta fara da kwas ɗaya kacal a farko-farkon assasa ta. Bayan wani lokaci, a hankali ta bunƙasa muhallinta, ta kuma ƙara yawan kwasa-kwasan da take yi, inda ta koma Kwaleji. Bayan shuɗewar wani lokaci, bunƙasar ta da cigaban da ta samu, ya samar mata da matsayi abun kwatantawa da sauran jami’o’in Iran, a ilmance.
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa zuwa yanzu, Jami’ar Maragheh ta wallafa maƙalar ilimi guda 1749 a wallafe-wallafe da tarukan cikin Iran (maƙalar jarida 422, da maƙalar taro guda 1327), da maƙala 1870 a matakin ƙasa da ƙasa. Jami’ar Maragheh ta mallaki lambar yabo, haka zalika ta wallafa mujalla 2 na musamman.
Martabar Jami’a
Kamar yadda tsarin ranking na Times ya fitar da bayanansa a shekarar 2022, Jami’ar Maragheh ta samarwa kanta matsayi na 301-400 a fagen Engineering Sciences, tsakanin jami’o’in duniya.
Cibiyoyi da Makarantu
_School of Basic Sciences
_School of Agriculture
_Faculty of Engineering
_Faculty of Human Sciences
_Astronomy and Astrophysics Research Center
Kuɗin Makarantar University of Maragheh
Kwasa-Kwasai
_English Language Teaching
_Geography and Urban Planning
_Psychology
_Law
_Physical Education
_Mathematics and Applications (Applied Mathematics)
_Applied Chemistry
_Cell Biology, Molecular and Microbiology
_Pure Chemistry
_Cell, Molecular Biology and Biotechnology
_Nano Science and Technology (Nanochemistry)
_Pure Mathematics and Analysis
_Pure Mathematics and Algebra
_Pure Mathematics and Geometry
_Applied Mathematics and Numerical Analysis
_Chemistry and Organic Chemistry
_Chemistry and Physical Chemistry
_Biotechnology and Microbial Orientation
_Chemistry and Analytical Chemistry
_Biology of Plant Sciences and Plant Physiology
_Chemistry and Mineral Chemistry
_Biology and Genetics
_Civil Engineering and (Civil _ Water Engineering)
_Materials Engineering and Industrial Metallurgy
_Chemical Engineering
_Mechanical Engineering and Manufacturing
_Materials and Nanomaterials Engineering (Nanotechnology)
_Civil Engineering and Hydraulic Structures
_Polymer Engineering and Polymer Industries
_Biosystem Mechanical Engineering
_Technology of Plant Production (Agriculture/Horticulture)
_Agricultural Engineering (Horticultural Science/Plant Medicine/Soil Science/Agronomy and Plant Breeding)
_Da sauransu…
Ku sauke wannan fayil na ƙasa domin samun cikakken list ɗin matakan karatu da kwasa-kwasan da kuke nema.
Kwasa-Kwasan University of Maragheh
Abubuwan Alfahari
_An zaɓi ɗaya daga cikin membobin tsangayar ilimi daga sashen Chemistry na wannan jami’a, Dr. Mehdi Esrafili a matsayin fitaccen masanin Chemistry (Chemist) na ƙasa, aka kuma sanya shi cikin jerin zakarun masana ilimin kimiyya na Iran baki ɗaya bisa dogaro da bayanan ESI
_Sanya membobin tsangayar ilimi na Jami’ar Maragheh su 8 a list ɗin rukuni na biyu na fitattun masana kimiyya na duniya bisa dogaro da bayanan Scopus
_Zaɓen fitattun manazarta na wannan jami’ar a matsayin zakarun manazarta na jiha
_Lashe matsayi na farko a ɓangaren wallafe-wallafen ɗalibai a fagen al’adu, da matsayi na biyu a wallafe-wallafen Human Sciences, matsayi na shida a tsakanin jami’o’in ma’aikatar ilimi, da kuma matsayi na 11 a cikin duka jami’o’in ƙasa da aka ayyana domin karɓar kyauta a bukin ‘Wallafe-Wallafen Ɗaliban Jami’o’in Iran’.
_Karrama ƙungiyoyin ilimi a gasar ‘kula da zafi’ ta ƙasa karo na goma sha ɗaya, da lashe matsayi na farko.
_Da sauransu…
Ababen More Rayuwa
Babban Laburare: An assasa laburaren jami’ar Maragheh ne a shekarar 1987, daga bisani, a shekarar 2011 aka maida shi zuwa sabon gini kuma tun lokacin assasa shi, ta hanyar ƙwararrun ma’aikatansa, laburaren ya taka muhimmiyar rawa a wurin karatu da ayyukan binciken jami’ar.
Wurin Kwana: Jami’ar Maragheh tana da wurin kwanan ɗalibai mata da na maza wanda ke ɗauke da kimanin ɗalibai 1,300 daga mabambantan garuruwa.
Adireshin University of Maragheh
Adireshi: Shahrak Golshahr, titin Prof. Ghannadi, randabawul na Madar, Azerbaijan ta Gabas.
Tambayoyin da ake yi
- Ko akwai yiwuwar ɗaukar ɗaliban ƙasar waje waɗanda sukayi karatunsu na sakandare a makarntun Iran, a matsayin ɗaliban waje?
A’a, ba zai yiwu ba, tsarin karɓarsu zai zama dai-dai da tsarin karɓar Iraniyawa. - Ko ɗalibai daga ƙasar Afghanistan za su iya karatu a wannan jami’a ta Maragheh?
Eh, amma taimakon da jami’a zata iya yi musu iya wurin hanzarta karɓa musu bizar karatu ne kawai.
[neshan-map id=”31″]