Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a University of Kashan

Karatu a University of Kashan

Loading

University of Kashan (Jami’ar Kashan) ita ce jami’a ta farko kuma jami’a mafi girma ta garin Kashan [babban birnin lardin Isfahan] wadda tana cikin garin na Kashan.

Gabatarwa

An karɓi lasisin assasa jami’ar a shekar 1973, inda ta fara aiki a watan September na shekarar 1974 a matsayin cibiyar koyarwa ta gaba da sakandare tare da ɗalibai 200, a fannonin Mathematics da Physics. Makarantar ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a ƙarƙashin ma’aikatar ilimi har zuwa shekarar 1979 bayan juyin musulunci na Iran, inda Kashan Higher School of Sciences ta koma ƙarƙashin kulawar jami’ar Isfahan.

 

A shekarar 1983 bayan sake buɗe jami’o’i (bayan juyin musulunci na Iran), jami’o’in wannan yanki sun koma ƙarƙashin kulawar jami’ar Tarbiat Moallem ta Tehran, inda suka canja kalar kwasa-kwasan da suke yi, su ka maida hankali wurin bunƙasa kwasa-kwasan Human Sciences. A shekarar 1989, bayan bunƙasar kwasa-kwasan da take yi, ta zama jami’a mai zaman kanta inda ta ci gaba da aiki da suna Jami’ar Tarbiat Moallem ta garin kashan, kafin ta fara koyar da kwasa-kwasan Engineering a shekarar 1994 wanda bayan wannan ne aka tabbatar da jami’ar Kashan a matsayin cikakkiyar jami’a. Bayan shekara ɗaya, an ƙarawa jami’ar Faculty of Architecture saboda buƙatuwar masana’antun yankin da ayyukan fasaha.

Jami’ar na da ɗalibai 900, malamai 630, da membobin kwamitin ilimi 300. Bincike ya nuna cewa Jami’ar Kashan ta wallafa maƙalar ilimi 7126 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida, ta karɓi baƙuncin taruka 10, sannan ta wallafa mujalla 12 na musamman. Baya ga haka, jami’ar ta wallafa karɓaɓɓun maƙala 5580 a matakin ƙasa da ƙasa.

Martabar Jami’a

Martabar (rank) jami’ar Kashan a tsarin ranking na Shanghai [wanda ya shahara wurin ranking ɗin jami’o’i] wanda aka kafa a shekarar 1998, a bayanan da wannan tsarin ya fitar na shekarar 2020, a fannoni uku (Mechanical Engineering, Chemical Engineering, da Energy Science & Engineering), jami’ar Kashan ta zo na farko a cikin jami’o’i 500 na duniya.

Karatu a University of KashanMakarantu

_Faculty of Human Sciences
_School of Engineering
_Faculty of Architecture and Art
_Faculty of Chemistry
_Faculty of Electronic Education
_Faculty of Mathematical Sciences
_Faculty of Natural Resources and Earth Sciences
_Faculty of Physics
_Faculty of Literature and Foreign Languages
_Kashan University Campus
_Faculty of Mechanical Engineering
_Electrical and Computer Faculty
_Sisters Campus

Kuɗin Makarantar University of Kashan

Kuɗin Makarantar University of Kashan

Kwasa-Kwasai

_Solid Mechanics
_Mechanical Design
_Energy Conversion
_Functional Design
_Facilities
_Architectural Engineering
_Handicrafts
_Archaeology
_Islamic Art
_Statistics and Applications
_Applied Mathematics
_Math
_Computer Science
_Electric Engineering
_Computer Engineering
_Natural Resources Engineering
_Nature Tour
_Desertification
_Environment
_Manufacturing
_Power Plant and Energy
_Dynamic Systems and Control
_Heat and Fluids
_Da sauransu…

Ku sauke wannan fayil na ƙasa domin samun cikakken list na kwasa-kwasan wannan jami’a.

Kwasa-Kwasan University of Kashan

Cibiyoyin Bincike

_Research Institutes of Science and Nanotechnology
_Research Institute of Natural Essential Oils
_Farsh Research Institute
_Energy Research Institute
_Kashanology Research Center
_Architecture and Urban Planning Research Center
_Scientific-Applied Research Center for Water, Drought and Climate Change
_Smart Network Technology Research and Development Center

Kwasa-Kwasan University of KashanAbaben More Rayuwa

کتابخانه مرکزی:Laburare mafi girma a garin Kashan mai sunan marhum Hazrat Ayatullahi Sayyed Mahdi Yasribi limamin masallacin juma’a na garin Kashan, wanda ke cikin jami’ar ta Kashan inda mutane ke amfana da shi. Wannan laburaren yana da girman murabba’in mita 4500, kuma yana da hawa huɗu. Laburaren nada ma’ajiyar littafai guda 5, ɗakin karatu, ɗakin wallafe-wallafe, da sauransu. Laburaren yana gabatar da ayyukansa ne ga duka al’ummar garin Kashan (ba iya ɗaliban jami’ar kawai ba) saboda haɓaka al’adar karatu.

Hostel: An fara aikin sabunta sashen block 5 na hostel ɗin ɗalibai mata tare da musharakar Mr. Mustafa Kashani. A wanna aiki (na sabunta block 5) ana so ne a canja duka ƙofofi da tagogin ƙarfe na hostel ɗin zuwa na zamani don sauƙaƙe amfani da su, sannan kuma a inganta fitilun ɗakuna da corridors, a canja fitilun zuwa waɗanda ba su zuƙar lantarki sosai, a kuma canja duka ƙofofin ɗakunan.

Kayan aikin University of KashanAbubuwan Alfahari

_Lashe matsayi na farko da jami’ar Kashan ta yi a ‘Research Productivity’ tsakanin duka jami’o’in Iran
_Samun matsayi na biyu a jami’o’in Iran, da matsayi na 109 a jami’o’in duniya a tsarin ranking na GreenMetric
_Samun shiga jerin fitattun jami’o’i 10 na Iran
_Samun shiga kaso 1 na farko na zaɓaɓɓun jami’o’in duniya
_Samun matsayi na biyu a cikin jerin manyan jami’o’i a fannin Nanotechnology
_Samun matsayi na farko a jami’o’in ƙasar Iran a tsarin ranking na Times na shekarar 2019
_Jami’a ta farko a tsarin ranking na Leiden
_Samar da programming language na farko na Iran <Sayyed Ali Muhammadiye>
_Jami’ar Kashan ta samu matsayi na 5 a manyan jami’o’in Iran, a tsarin ranking na Europe
_Da sauransu…

Yanayin Wuri

University of Kashan tana cikin  garin Kashan a titin Qotb Ravandi kuma ta fuskar yanayin wuri, jami’ar na kusa da  Shahid Rajaei Technical University Ravand,  Masaukin baƙi na malamai, na University of Kashan,  Park ɗin Shahid Rajaei University,  Faculty of Basic Sciences , da kuma  swimming pool ɗin Kashan University of Medical Sciences.

Adireshin University of Kashan

Adireshi: Kilomita 6 Titin Qotb Ravandi, Kashan.


Tambayoyin da ake yi game da University of Kashan

  1. Shin, ana karatu da larabci a University of Kashan? 
    A’a, ya danganci malamin da kuma yawan ɗaliban Iraq da ke yin wannan darasi, babu wani tabbacin cewa za’a yi karatu da larabci. A lokaci guda kuma wajibi ne ɗalibi ya kawo shaidar kammala koyon yaren farsi (wanda ma’aikatar ilimi ta yadda da shi) kafin wata 9 na farkon shigarsa wannan jami’a.

[neshan-map id=”23″]

Related Posts
Leave a Reply