Karatu a Jami’ar Art University of Isfahan
Jami’ar fasahar zane-zane ta Isfahan (Art University of Isfahan) tana daya daga cikin jami’o’in gwamnati na ƙasar Iran, a lardin Isfahan. Wannan jami’a na daga cikin manyan jami’o’i guda huɗu a ƙasar waɗanda suka ƙware a fannoni da suka shafi zane-zane da fasaha. Tana da babban matsayi a ilmance a jerin jami’o’in Iran da na duniya. Ku kasance tare da mu don samun cikakken bayani game da karatu a wannan jami’a.
Gabatarwa
A matsayinta na matattara ta ilimin gaba da sakandare a fannonin zane-zane, An fara assasa Jami’ar Art University of Isfahan da sunan “Isfahan College Campus” a shekarar 1976. Hadafinta na asali shi ne horar da ƙwararru a ɓangaren adanawa da kuma dawo da martabar gine-gine da kayan tarihi. A matsayinta na kwalejin gaba da sakandare ta farko mai wannan hadafin a ƙasar Iran, ta fara da karɓar ɗalibai a fannoni daban-daban a matakin digiri na farko irin su archaeology, painting, interior architecture, construction, chemistry, da kuma textile, sai kuma kwas ɗin “restoration of buildings and historical artifacts” a matakin mastas.
A shekarunta na farko-farkon assasawa, an alaƙanta ta da jami’ar Farabi (Farabi University). To amma bayan ta ɗauki ɗalibai a karo na biyu, an rufe jami’ar a lokacin juyin musulunci da aka yi a Iran, inda aka sake buɗe ta a shekarar 1983 bayan juyin juya hali na al’adu.
Jami’ar na da kimanin ɗalibai 3000 da malamai 290. Bincikenmu ya nuna cewa jami’ar ta wallafa maƙalolin kimiyya guda 3,742 a mujallu da tarukan cikin gida. Jami’ar ta wallafa mujalla 3 keɓantattu sannan kuma ta shirya taruka 5 zuwa yanzu.
A bisa ƙa’idoji na wallafa maƙalolin kimiyya, jami’ar fasahar zane-zane ta Isfahan ta samu martabobi daban-daban tsawon shekaru. Ana ba ma jami’ar da ta fi kowace jami’a yawan wallafe-wallafen kimiyya matsayi na ƙoli (na farko), yayin da ake martaba sauran waɗanda suka biyo baya daidai da ƙwazonsu. Ana auna kowace makaranta ne a matakai biyu: na farko shi ne la’akari da sauran tsararrakinta, na biyu kuma bisa la’akari da fitattun cibiyoyin binciken kimiyya na ƙasar. Wannan jami’a ta Isfahan ta samu martabobi daban-daban a mabambantan shekaru. Ta riƙe matsayi na farko a tsakanin jami’o’in Iran wanda hakan ya sa ta zama jami’ar fasahar zane-zane ta ɗaya a ƙasar.
Makarantu da Kwasa-Kwasai
Faculty of Conservation and Restoration
Wannan sashen na jami’ar Art University of Isfahan shi ne na farko a makarantun ƙasar Iran. Tun daga shekarar 1976 yake aikin horar da ƙwararrun ma’aikata a matakin digiri da na mastas (da kwasa-kwasai biyu) a matsayin sashen koyarwa na farko na jami’ar. Kwasa-Kwasan karatu a wannan sashen sun haɗa da:
Digiri
- Restoration of Historical Works
- Restoration and Revival of Historical Buildings
Master’s
- Restoration of Historical and Cultural Objects
- Restoration and Revival of Historical Buildings and Fabrics
- Archaeology
- Archaeometry
PhD
- Restoration of Objects
- Restoration of Buildings
- Archaeology
Faculty of Advanced Art Studies and Entrepreneurship
Wannan ɗaya ce daga cikin kwalejoji biyar na jami’ar fasahar zane-zane ta Isfahan. An fara yunƙurin samar da kwalejin da zai haɗa fasahar zane-zane (art) da kasuwanci ne a shekarar 2010. Bayan samun izini daga ma’aikatar kimiyya (ministry of science), inda kwalejin ya fara aiki a watan October na shekarar 2012 da kwasa-kwasai guda bakwai (digiri a kwas ɗin Museum Studies da Tourism, sai mastas a kwasa-kwasan Cultural Entrepreneurship, Tourism Management, Art Economics, Urban Economics, da kuma Museum Management).
Kwasa-Kwasan da ake yi a jami’ar sun haɗa da:
Digiri
- Museum
- Tourism
Master’s
- Art Research
- Urban Economics
- Art Economics
- Art Entrepreneurship
- Tourism Entrepreneurship
- Tourism Management
- Museum Management
- Philosophy of Art
Doctorate
- Art Research
Faculty of Architecture, Industrial Design, and Urban Planning
Shi kuma wannan kwalejin na Architecture and Urban Planning yana nan a ginin Towhidkhaneh. Ginin na Towhidkhaneh ya kasance wuri ne na taron sufaye da wasu ayyukansu na ibada a baya, amma a lokacin mulkin Reza Shah Pahlavi, an ƙaurace ma wurin inda aka maida shi wurin ajiye dabbobi. An ce akwai lokacin da ma aka yi amfani da shi a matsayin kurkuku a siyasance. kwasa-kwasan da ake yi a wannan kwalejin sun haɗa da:
Digiri
- Architectural Engineering
- Urban Planning Engineering
- Industrial Design
Master’s
- Architecture
- Architectural Studies
- Design of Educational Spaces
- Architecture and Energy
- Urban Design
- Urban Planning
- Regional Planning
Doctorate
- Islamic Urban Planning
- Architecture
Faculty of Visual Arts and Applied Arts
Wannan kwalejin ya fara ayyukansa ne a shekarar 1990 a daidai lokacin da jami’ar fasahar zane-zane ta Isfahan ta fara cin gashin kanta. Da fari kwalejin ya taƙaitu a fannoni biyu na Paintings da Handicrafts, daga baya ya ƙara da kwas ɗin Carpet Weaving a shekarar 1997, a shekarar 2006 kuma aka ƙara Graphic Design da Photography. Kwalejin na nan a ginin French School. Ana yin kwasa-kwasai kamar haka a wannan kwalejin:
Undergraduate
- Visual Communication (Graphic Design)
- Photography
- Painting
- Music (Composition)
Master’s
- Painting
- Graphic Design
- Illustration
Faculty of Handicrafts
Kwalejin Handicrafts na nan a titin Hakim Street, daura da masallacin tarihi na Hakim. Kwalejin na amfani da gine-ginen Shakari House da Islamic House. Ana yin kwasa-kwasai kamar haka a wannan kwalejin:
Undergraduate
- Islamic Art
- Handicrafts
- Carpet Weaving
- Calligraphy and Miniature Painting
Master’s
- Islamic Art
- Handicrafts
- Carpet Weaving
Doctorate
- Islamic Art
Abubuwan More Rayuwa
Kamar yadda kuka sani, ya kamata ace makarantar zane-zane ta yi tanadin kayan akiki na musamman kasantuwar cewa kwasa-kwasansu sun bambanta da na sauran fannoni. A kwasa-kwasan art, ana aiwatar da wasu ayyukan ne a cikin muhallin makarantar. Saboda haka jami’ar ta yi tanadin kayan aiki na musamman don amfanin ɗalibanta duba da cewa Isfahan birni ne na tarihi. Daga cikin kayan aikinta akwai tsarin karatun online mai ƙarfi wanda ɗalibai za su iya amfani da shi ba tare da matsala ba. Hakazalika akwai ingantacciyar kalandar karatu wadda makarantar ta samar domin ta zame wa ɗalibai jagora a tsawon zangonsu na karatu.
Wurin Kwanan Ɗalibai na Isfahan University of Art
Yana da kyau ɗalibai su sani cewa hostel ba sakakken wuri ba ne, kuma ba wuri ne da kowa zai yi abinda ya ga dama ba. Waɗanda suka zauna a hostel za su fahimci cewa wuri ne da mu’amalar zamantakewa ke ƙarfafuwa tsakanin ɗalibai. Kowane hostel na da nasa dokokin; ɗaya daga cikin dokokin ya shafi shige da fice na ɗalibai a tsakanin awannin da aka ayyana. A hostel ɗin maza lokutan shige-da-fice kan fara daga ƙarfe 6 na safe zuwa 11 na dare, a hostel ɗin mata kuma 6 na safe zuwa 9 na dare. Har ila yau, akan ɗauki attendance ɗin ɗalibai da dare a hostel ɗin mata.
A hostel ɗin wannan jami’a, akan ayyana mutum ɗaya a matsayin mai jagorantar wannan hostel ɗin. Akan ayyana wanda ya samu gogewa sosai da dokoki da ƙa’idojin hostel kuma zai iya zama abun koyi da jigo ga sauran ɗalibai waɗanda ba su jima da shigowa hostel ɗin ba.
Yanayin Wuri
Jami’ar fasahar zane-zane ta Isfahan na nan a yankin Naqshe Jahan na garin Isfahan, a titin Khorshid. Akwai muhimman wurare kusa da jami’ar irinsu Asibitin Khorshid, Naqsh-e Jahan Square Pool, Gidan Tarihin Ɗabi’a na Isfahan, kasuwar Qeysariyeh, Fadar Ali Qapu, kasuwar Naqshe Jahan, Gidan Tarihi na Zane-Zanen Ƙawa (Rakeb House), da sauransu.
Related Articles:
Karatu a Iran