Karatu a Chabahar International University
Jami’ar ƙasa da ƙasa ta Chabahar (Chabahar International University) jami’a ce wadda ta fara aiki a shekarar 2002 bisa izinin Ma’aikatar Ilimi. Karatu a wannan jami’a farkon ci gaba ne ga ɗalibai a manyan matakan karatu. Domin cimma hadafinta na shiryawa da horar da ɗalibai masu hazaƙa bisa mutunta dokokin addinin musulunci da ‘yan’adamtaka, jami’ar ta tsara ayyukanta na koyarwa daidai da zamani, tare da kiyaye ƙa’idodin ilimi.
Gabatarwa
Jami’ar Chabahar jami’a ce mai zaman kanta (firabet) a cikin garin Chabahar na lardin Sistan-Baluchestan, wadda aka assasata a shekarar 2002. Yanzu haka, akwai ɗalibai 769 da malamai 52 a jami’ar. Bincike ya nuna cewa jami’ar ta wallafa maƙalolin kimiyya guda 322 a mujalloli da taruka. Har ila yau, jami’ar Chabahar ta mallaki mujalla guda ɗaya ta musamman, kuma ta shirya taruka 5 zuwa yanzu. Bayan haka, akwai wasu maƙaloli guda 4 a matakin ƙasa da ƙasa da suka fito daga wannan jami’ar Chabahar.
Yanzu haka ana yin kwas 22 a jami’ar tare da wasu 2 a matakin associate degree, 11 a matakin digiri, 10 a matakin mastas. Ma’aikatar ilimi ta Iran ce ke ba da shaidar kammala karatu ga waɗanda suka kammala karatunsu a wannan jami’a.
Jami’ar Chabahar ta fara kwas ɗinta na farko a matakin digiri tare da haɗin gwiwar Jami’ar London a ƙarƙashin makarantu 3 na Economics and Political Science, Goldsmiths, da Royal Holloway. Ana yin kwas 8 tare da haɗin gwiwar jami’ar ta London, inda ita ce ke yin jarabawar ƙarshen shekarar karatu. Hakazalika jami’ar ta London kan bayar da kwalin digiri, sannan daga bisani jami’ar ta Chabahar ta bayar da nata ita ma.
Jami’ar Chabahar na ƙoƙarin faɗaɗa dangantakar ilimi ta ƙasa da ƙasa ta hanyar ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran manyan jami’o’in cikin gida da na waje, bisa la’akari da albarkatu da shirye-shiryenta. Saboda wasu dalilai na ƙasa da ƙasa, a halin yanzu dukkan kwasa-kwasan da ake yi a jami’ar ta Chabahar, ana koyar da su ne da yaren Farsi. A fannin koyarwa da karatu mai zurfi, jami’ar na da manufar samar da ingantaccen ilimi ga ɗalibai don haɓaka matsayinsu a ilmance a keɓantattun fannoni, zurfin tunani, da zamantakewa.
Martabar Jami’ar Chabahar
A watan August na shekarar 2020, kundin bayanan jami’o’i na ƙasar Iran ya sanar da jami’ar Chabahar a matsayin ta 3 a jerin jami’o’in firabet, da kuma matsayi na 35 a duka jami’o’in ƙasar.
Kuɗin Makaranta
Kwasa-Kwasai
Bachelor’s Degree:
- Electrical Engineering
- Civil Engineering
- Mining Engineering
- Computer Engineering
- Architectural Engineering
- Banking Management
- Business Management
- Industrial Management
- English Language and Literature
- Educational Sciences
- Law
- Economics
Associate Bachelor’s Degree:
- Executive Civil Engineering
- Primary Education
Master’s Degree:
- Information Technology – E-commerce
- Civil Engineering – Construction Management
- Civil Engineering – Structures
- Educational Technology Engineering
- Financial Management
- Business Management – Marketing
- Business Administration – Finance
- International Trade Law
- Geography and Land Use Planning
Scholarship a Jami’ar ƙasa da ƙasa ta Chabahar
Jami’ar Chabahar na bayar da wani nau’i na scholarship mai suna ‘Makran Coast International Scholarship’ ga ɗaliban digiri da masters ƴan ƙasashen Afghanistan, Pakistan, India, Tajikistan, Kazakhstan, Oman, da China. Scholarship ɗin ya kasu kashi uku kamar haka: cikakken scholarship (wanda ya ɗauke kuɗin makaranta, wurin kwana, da inshorar lafiya), sai scholarship na karatu (wanda ya ɗauke kuɗin makaranta kawai), sai kuma scholarship na kashi 50% na kuɗin makaranta. Sharaɗin samun wannan scholarship ɗin shi ne ƙwarewa sosai a yaren Farsi.
Kayan aikin Jami’ar ƙasa da ƙasa ta Chabahar
- Cibiyar yare ta matasa da yara ƙanana
- Cibiyar ƙirƙira ta jami’a
- Incubator and Science and Technology Park
- Computer and Language Laboratory
- Ɗakin Computer na Zamani
- Game, Animation, and Programming Center
- Local Music Center
- Azuzuwan karatu da za su ɗauke kimanin mutum 2,000 ɗauke da kayan aiki
- Laburare mai girman murabba’in mita 250, ɗauke da na’urori da tarin litattafan cikin gida da na waje
- Student accommodation complex covering 23,000 square meters for domestic and international students
- Makarantar Kwana ta Dāna and Tunā