تهران، میدان ولیعصر، جنب سفارت عراق، ساختمان مینو
مشهد، میدان شریعتی، نرسیده به احمد آباد ۱، طبقه بالای بانک دی

Yawon neman lafiya a Iran

Yawon neman lafiya a Iran

Loading

Rayuwa wuri guda a cikin birni na tsawon lokaci kan iya haifarda damuwa da stress, rashin bacci da sauran matsaloli makamantansu. Daya daga cikin hanyoyin magance wannan matsalar shi ne tafiye-tafiyen neman lafiya, inda mutum zai bar garinsu ko ƙasarsu zuwa wani wurin domin ganin likitoci ko masu magani. Ku kasance tare da mu don sanin yanayin ire-iren wadannan tafiye-tafiyen na neman lafiya a ƙasar Iran.

A zamanin yanzu da ake iya samun bayanai a kan harkokin lafiya da likitoci na ƙasashe daban-daban cikin sauƙi, al’amarin tafiye-tafiyen neman lafiya ya zama abu mai muhimmanci ga tsarin kula da lafiya na ƙasa da na duniya baki ɗaya. Marasa lafiya na ko’ina a faɗin duniya za su iya tattara bayanan da suke buƙata cikin sauƙi daga kafafe daban-daban su kuma zaɓi ƙasar da suke son zuwa jinya, kuma su saya wa kansu ticket na tafiya inda suke so da kansu.

Yawon neman lafiya na nufin mutum ya bar muhallinsa ko ƙasarsa zuwa wasu ƙasashen da nufin jinya ko karɓar magani ko gudanar da bincike akan lafiyarsa. Maganin zai iya shafar ɓangarori da dama na lafiya amma mafi shahara daga ciki akwai: Kula da haƙori, aikin gyaran jiki, dashen sassan jiki, matsalar rashin haihuwa, da sauransu. Ma’anar da muka bada a nan za ta iya shan bambam a wasu ƙasashen.

A wasu ƙasashen majinyatan da ke zuwa asibiti daga wata ƙasa kawai suke kira da matafiyan neman lafiya, a wasu ƙasashen kuma duk wanda ɗaya daga cikin dalilan da muka ambata a sama suka sanya shi zuwa wata ƙasa, shi ma ana iya kirsansa da wannan suna. Sunan ya ƙunshi hatta baƙin mara lafiyan da suka baro ƙasar baƙuncinsu zuwa ƙasarsu ta asali domin duba lafiyarsu, ko kuma suka bar garin da suke a cikin ƙasarsu zuwa wani gari wurin neman lafiya ba tare da sun bar ƙasar gabaɗaya ba.

Yawon neman lafiya a Iran

Masana’antar yawon neman lafiya a Iran

Tafiye-Tafiyen neman lafiya zuwa ƙasar Iran ya bunƙasa sosai ta yadda ana sa ran yawan mutanen da ke shiga ƙasar Iran domin neman lafiya zai iya kai kimanin mutum miliyan 20 a cikin shekara 20 (zuwa shekarar 2025). Cimma wannan hadafin ya ta’allaƙa da sa hannun wasu kamfanoni masu zaman kansu a harkokin tallata ayyukan lafiya a ƙasar Iran. Hakazalika gwamnatin ƙasar ma bata yi ko’inkula da lamarin ba inda ta sa hannu a takardun yarjejeniya masu yawa tsakaninta da ƙasashe daban-daban dangane da hakan. Hakazalika yunƙurin hukumar kula da yawon bude ido, majalisar harkokin waje, da tsarin likitanci duk ya bada gudummawa.

Yawon neman lafiya (Health Tourism) a taƙaice ya kasu kashi 3 kamar haka:

 1. Yawon neman lafiya (Medical Tourism)
 2. Yawon shan iska cikin ɗabi’a (Curative Tourism)
 3. Yawon jinya (Wellness Tourism)

Yawon neman lafiya (Medical Tourism)

Ya keɓanci ayyukan da suka shafi zuciya, ƙwaƙwalwa, gyaran jiki, dashen gashi, gyaran hanci, da sauransu. A taƙaice dai ya shafi sassan jiki daban-daban; sannan kuma shi ne ɓangare mafi muhimmanci kuma mafi haɗari a yawon neman lafiya. Galibi akan yi waɗannan tafiye-tafiyen ne domin neman waraka ko karɓar magani daga asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya mabambanta.

Da yawan ƙasashen duniya waɗanda ake zuwa jinya sukan ƙara ƙaimi wurin hidimtawa baƙin mara lafiya da kuma yi musu ayyuka na musamman wasu lokuta domin su samu riba mai yawa. Daga cikin abubuwan masu muhimmanci ke taimaka ma ƙasashe wurin jan hankalin majinyata kuma suke da tasiri sosai a wannan fannin akwai:

 • Samuwar ƙwararrun likitoci kuma masana
 • Asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya waɗanda suka cika duka sharuɗan da ake buƙata a mahangar ƙasa da ƙasa
 • Tarihi mai kyau na ilimin likitanci
 • Kayan aikin likitanci a ƙarƙashin kulawar likitoci
 • Kammalallun kayan aiki na zamani
 • Ingantaccen Hotel mai kayan aikin da ake buƙata na zirga-zirgar matafiya

Yawon Magani (Curative Tourism)

Yawon jinya yana ɗaya daga cikin ɓangarorin yawon neman lafiya. Yawon magani na nufin zuwa wuraren kiwon lafiya daban-daban don ganin likita. Daga ciki akwai abubuwa kamar haka:

 • Idon ruwan ɗumi
 • Hasken rana
 • Magani da laka
 • Teku mai gishiri
 • Tausa
 • Wankan ganye
 • Muhalli mai kyau kuma tsaftatacce

Kasantuwar yanayi mai kyau da ɗabi’a mai yawa da ƙasar Iran take da shi, tana ɗaya daga cikin fitattun ƙasashe waɗanda ake yawan zuwa yawon neman lafiya. Baya ga ɗabi’a mai kyau da kuma yanayin masauki mai kyau da aka tanadarwa matafiyan a ƙasar Iran don samar musu da walwala da kwanciyar hanali tsawon lokacin zamansu na jiya. Yanzu haka akwai sama da idon ruwa mai ɗumi 1000 na magani a ƙasar Iran wanda baya ga amfaninsu wurin magani, suna daga cikin abubuwan da ake zuwa kallo a yawon buɗe ido a ƙasar Iran.

Yawon jinya (Wellness Tourism)

ya ƙunshi ayyukan kiwon lafiya waɗanda ba sa buƙatar tiyata irinsu tausa (massage), acupuncture, hydrotherapy, da amfani da idon ruwa mai ɗumi da mai sanyi don yin magani, da sauransu. Hadafin da yawa cikin irin waɗannan majinyatan shi ne sabunta nishaɗi, samun sukuni da natsuwa, nisantar damuwa da matsalolin rayuwarsu ba tare da mu’amalantar likita ba. Daga cikin abubuwan da zaku iya samu a ƙasar Iran a babin yawon jinya akwai hotel da gidaje a cikin jeji (masaukai a kusa da tsaunuka, hamada, da bakin ruwa) wanda hakan zai sauƙaƙe muku yawace-yawacen da za ku yi a tafiyar taku.

Dalilan zuwa ƙasar Iran yawon neman lafiya

Ya danganci a wane lokaci matafiyi zai yanke shawarar tafiya wata ƙasar neman lafiya sannan kuma me ya gamsar da shi? Babu shakka akwai abubuwa guda biyu masu muhimmanci da ke taka rawa wurin yanke shawara ga majinyacin da zai yi tafiyar, ga su kamar haka:

 1. Sauƙin kuɗin da zai biya a wata ƙasar fiye da ƙasarsa
 2. Ingancin kayan aiki da ƙwararrun likitoci a wata ƙasar fiye da ƙasarsa

Tabbbas farshin magani a wata ƙasar yana da matuƙar muhimmanci musamman a ɓangaren ayyuka da tiyatar gyaran jiki wanda su ne ayyuka mafi tsada a duniyar likitanci. Bisa la’akari da waɗannan abubuwa biyu da muka ambata musamman a ƙasashen larabawa irin su Iraq, Oman, da sauransu zuwan marasa lafiya daga waɗannan ƙasashen zuwa ƙasar Iran ya yawaita saboda ingancin cibiyoyin likitanci da sauƙin farashi.

Zuwa ƙasar Iran saboda ziyara, yawon buɗe ido, karatu, ko wani dalili daban yana da daɗi kuma ba shakka zamanku a Iran zai zama ɗaya daga cikin mafi daɗin ranakun rayuwarku saboda yanayi mai daɗi, kayan aiki, sauƙin farashin rayuwa, da sauransu.

 

Related Posts
Leave a Reply