Mazandaran lardi ne a arewacin ƙasar Iran wanda a cikinsa akwai wata jami’ar karatun likitanci a garin Sari. A wannan rubutun mun kawo muku bayani a kan yanayin karatu a wannan jami’a ta Mazandaran University of Medical Sciences, tarihinta, makarantunta, kwasa-kwasanta, da sauransu.
Gabatarwa
Jami’ar karatun likitanci ta Mazandaran (Mazandaran University of Medical Sciences) ta fara aiki a shekarar 1975, kafin a bunƙasa babbar cibiyar koyarwa ta Midwifery (zuwa cibiyar koyarwa ta farko) a shekarar 1986. A tsawon waɗannan shekaru, an assasa jami’ar karatun likitanci ta Babol a shekarar 1985, kwalejin likitanci ta Sari a 1988, da kuma kwalejin likitanci ta Gorgan a 1992 sannan aka samar da lardin Golestan a shekarar 1988 lokacin da jami’ar likitanci ta Babol ta tsaya da ƙafafuwanta, sannan ne aka samar da Mazandaran University of Medical Sciences.
Jami’ar karatun likitanci ta Mazandaran ta ƙunshi sassa guda takwas kamar haka; karatu, jinya, kiwon lafiya, bincike, fasaha, abinci da magani, sashen kula da zamantakewa, sashen al’adu da kula da ɗalibai, da kuma sashen tafiyarwa. Jami’ar na da kimanin ma’aikata 17,000 masu aiki a wuraren kiwon lafiya 1,110 na ƙauyuka, cibiyoyin magani 280, sansanonin kiwon lafiya 54, da asibiti 24, suna gabatar da wadannan ayyukan na kiwon lafiya ne ga al’ummar wannan lardi na Mazandaran kimanin mutum miliyan uku.
Jami’ar na tafiyar da ayyukanta na koyarwa ne tare da membobin tsangayar ilimi 501, ɗalibai 8000 bayan ta yaye 16,000, kwasa-kwasai 110, sassan koyarwa da bincike 34, mujalla 13, cibiyar bincike 21, cibiyar bunƙasa ayyukan fasaha 10, masana’antu 4 na koyarwa, wuraren bincike 4, da kuma tsarin bincike sama da 5700.
Martabar Mazandaran University of Medical Sciences
Tsarin ranking na Shanghai ɗaya ne da cikin manyan tsarin ranking ɗin jami’o’i na duniya wanda ke gabatar da ayyukansa na martaba jami’o’in duniya ta hannun jami’ar Shanghai Jiao Tong ta ƙasar China. Wannan tsarin ya ƙunshi jami’o’i ne kaɗai waɗanda suka wallafa ƙirƙire-ƙirƙirensu na kimiyya a shafin Web of Science tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019. Mazandaran University of Medical Sciences ta bayyana a matsayi na 351 – 400 a jerin manyan jami’o’in duniya a shekarar 2021.
Makarantu
_ School of Dentistry
_ School of Medicine
_ School of Pharmacy
_ Faculty of Modern Medical Technologies
_ School of Nursing and Midwifery
_ School of Health
_ School of Paramedicine
_ Amol Medical Campus
_ Amol School of Paramedicine
_ Amol School of Nursing and Midwifery
_ Ramsar International Unit
_ Behshahr School of Nursing
Kwasa-Kwasai
_ Laboratory Sciences
_ Surgery Room
_ Anesthesia
_ Occupational Therapy
_ Radiology
_ Medical Documents
_ Medicine
_ Dentistry
_ Pharmacy
_ Thalassemia
_ Geriatric Nursing
_ History of Medical Sciences
_ Digestion and Liver of Adults
_ General Surgery
_ Orthopedic
_Da sauransu…
Ku sauke wannan fayil na ƙasa domin samun cikakken list ɗin kwasa-kwasan wannan jami’a.
Kwasa-Kwasan Mazandaran University of Medical Sciences
Jadawalin kuɗin makaranta da sauran kuɗaɗen Mazandaran University of Medical Sciences
Title | Annual Tuition ( in Dollars ) |
---|---|
Bachelor Degrees | 3,300$ |
M.Sc | 3,850$ |
M.B.B.S | 5,500$ |
M.D | 6,600$ |
Dentistry(D.D.S) | 5,500$ |
Pharmacy | 5,500$ |
Specialty in Medicine | 6,600$ |
Fellowship | 6,600$ |
Sub-Specialty in Medicine | 6,600$ |
Ph.D | 6,600$ |
Sauran kuɗaɗe
Title | Price | Payment type |
---|---|---|
registration | 50$ | Just once |
First transportation from the airport (upon requested) | 25$ | Just once |
Furnished accommodation (upon request) | 3,650$ | yearly |
Student insurance | 60$ | yearly |
Student family insurance | 15$ | Annually for each person |
Persian language classes (if it necessary) | 1,980$ | 120 sessions |
English language classes (if it necessary) | 3,153$ | 120 sessions |
Duba da cewa jami’ar tana garin Sari ne, ya kamata ku san cewa farashin rayuwa a wannan gari na zai kama wuraren dala 250 zuwa 300 a kowane wata.
Asibitocin koyarwa da na jinya
_ Asibitin Imam Khomeini, Sari
_ Asibitin Fatimah Zahra (AS), Sari
_ Asibitin Plastic and Reconstructive Surgery na Zare, Sari
_ Asibitin Bu-Ali Sina, Sari
_ Asibitin ƙuna da Psychiatry, Sari
_ Asibitin Imam Ali (sashen haihuwa na garuruwan tsakiya da yammacin lardin Mazandaran), Amol
_ Asibitin Imam Reza (sashen kula da cutukan da suka shafi hanji da tiyata, na garuruwan tsakiya da yammacin lardin Mazandaran), Amol
_ Asibitin 17 Shahrivar (sashen haɗurra na garuruwan tsakiya da yammacin lardin Mazandaran-Troma), Amol
_ Asibitin Imam Khomeini (sashen kula da cututtukan da suka shafi zuciya, da tiyatar zuciya na garuruwan tsakiya da yammacin lardin Mazandaran), Amol
_ Asibitin Ahmadnejad, Katalom
_ Asibitin Imam Sajjad, Ramsar
_ Asibitin Rajaei, Tankabon
_ Asibitin Ayatollah Taleghani, Chalous
_ Asibitin Qaim, Kalardasht
_ Asibitin Shahid Beheshti, Nowshahr
_ Asibitin Imam Khomeini, Noor
_ Asibitin Valiasr, Noor
_ Shohada Hospital, Mahmoodabad
_ Imam Khomeini Hospital, Faridounknar
_ Asibitin Hazrat Zainab, Babolsar
_ Asibitin Shahid Rajaei, Babolsar
_ Asibitin Razi, Qaem Shahr
_ Asibitin Azizi, Juybar
_ Asibitin Shohada, Savadkuh
_ Asibitin Imam Hosein, Neka
_ Asibitin Imam Khomeini, Behshahr
_ Asibitin Shohada, Behshahr
_ Asibitin Saminul A’immah, Gulogah
Cibiyoyin Bincike
_ Heart Research Center
_ Diabetes Research Center
_ Orthopedic Research Center
_ Thalassemia Research Center
_ Gastrointestinal Cancer Research Center
_ Research Center for Treatment-Resistant Hospital Infections
_ Gastroenterology and Liver Research Center
_ Psychiatric Research Center
_ Pharmaceutical Sciences Research Center
_ Cell and Molecular Biology Research Center
_ Microbial Resistance Research Center
_ Center for the Research of Invasive Fungi
_ Toxoplasmosis Research Center
_ Genetics and Immunity Research Center
_ Health Research Center for Plant and Animal Products
_ Center for Traditional and Complementary Medicine Research
_ Health Sciences Research Center
_ Laboratory Animal Research Institute
Abubuwan Alfahari
_ Lashe matsayi na farko a tsakanin jami’o’in rukuni na biyu a bikin binciken kimiyyar kiwon lafiya na Razi, karo na 12 a shekarar 2005
_ Lashe matsayi na farko a tsakanin jami’o’in rukuni na biyu a bikin binciken kimiyyar likitanci na Razi, karo na 14 a 2007
_ Lashe matsayi na biyu a tsakanin jami’o’in rukuni na biyu a bikin binciken kimiyyar likitanci na Razi karo na 16 a 2008
_ Lashe matsayi na farko a tsakanin jami’o’in rukuni na biyu a bikin binciken kimiyyar likitanci na Razi, karo na 17 a 2009
_ Lashe matsayi na farko a tsakanin jami’o’in rukuni na biyu a bikin binciken kimiyyar likitanci na Razi, karo na 18 a 2011
_ Lashe matsayi na farko a tsakanin jami’o’in rukuni na biyu a bikin binciken kimiyyar likitanci na Razi, karo na 19 a shekarar 2013
_ Lashe matsayi na farko a tsakanin jami’o’in rukuni na biyu a bikin bincike na kimiyyar likitanci na Razi, karo na 20 a shekarar 2015
_ Lashe matsayi na farko a tsakanin jami’o’in rukuni na biyu a bikin binciken kimiyyar likitanci na Razi, karo na 21 a shekarar 2016
_ Lashe matsayi na farko a tsakanin jami’o’in rukuni na biyu a bikin binciken kimiyyar likitanci na Razi, karo na 22 a shekarar 2017
_ Lashe matsayi na farko a tsakanin jami’o’in rukuni na biyu a bikin binciken kimiyyar likitanci na Razi, karo na 23 a shekarar 2018
_ Samun babban matsayi a bikin bincike na Razi da bikin Kharazmi, da kuma shigarta tawagar fiyayyun jami’o’in duniya, sai kuma kasancewarta jami’a mafi girma a kundin tarihin kimiyyar duniyar Musulunci. Duka waɗannan na daga cikin nasarorin da jami’ar ta samu.
Ababen More Rayuwa
Wuraren cin abinci na jami’ar, wuraren kwanan ɗalibai, filin wasanni, clinic, cibiyar koyon yarukan waje, cibiyar koyon yaren farsi, yawon shaƙatawa, duka waɗannan na daga cikin tsare-tsaren da jami’ar ta yi tanadi wa ɗalibanta.
Yanayin muhallin da jami’ar take
Jami’ar na nan a titin Shahid Solaimani a kusa da wurare kamar gidan cin abinci na Asgharbareh, kwalejin fasaha lamba 2, gidan man Kowsar, Sayeh Roshan Printing Press, da kuma Honarestane Imam Reza.
Adireshin jami’a
Adireshi: Garin Sari, Meidane Imam, Se rahe Juybar, farkon babbar hanyar Vali Asr (ATF), Hedikwatar jami’ar Mazandaran University of Medical Sciences
Tambayoyi
- Wasu takardu ake buƙata don neman admishin a wannan makaranta?
Passport, hoto, transcript, certificate, cv, motivation letter, recommendation letter. - Shin zai yiwu a karɓi tranfer na darusa a wannan jami’a?
A’a, saidai a sake sabuwar rijista.
[neshan-map id=”11″]