Garin Kermanshah shi ne babban birnin jihar Kermanshah. Shi ne gari mafi yawan al’ummar kurdawa a Iran, sannan ɗaya daga cikin garuruwa masu ɗimbin tarihi da al’adu na ƙasar Iran. Kermanshah University of Medical Sciences ɗaya ce daga cikin shahararrun jami’o’in da suke wannan gari na Kermanshah. A wannan rubutu, zamu kawo muku muhimman bayanai da suka shafi karatu a Kermanshah University of Medical Sciences, kamar bayanan kuɗin makaranta, abubuwan more rayuwa, da sauransu. Saboda haka ku kasance tare da mu.
Gabatarwa
Kermanshah University of Medical Sciences, jami’a ce ta gwamnati wadda ke ƙarƙashin kulawar hukumar lafiya, kuma ana koyarda darusan da suka shafi likitanci da makamantansu a wannan jami’a. Kermanshah School of Nursing ta fara aiki a shekarar 1965 inda ta ɗauki ɗaliban nursing a matakin digiri, a wani muhalli da ke mararrabar Shir wa Khorshid a garin Kermanshah. Wannan cibiyar koyarwa ta shiga sahun sauran jami’o’in karatun likitanci, inda aka haɗe ta da sauran cibiyoyin kiwon lafiya dake wannan yankin, aka kuma canja mata suna zuwa “kermanshah university of medical sciences” wanda aka san ta da shi yanzu.
A halin yanzu a wannan jami’ar akwai ɗalibai 4394 da malamai 474. Bayanan da aka fitar sun nuna cewa zuwa yanzu wannan jami’a ta wallafa maƙalar ilimi 2381 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida. Kermanshah University of Medical Sciences tana da lambar yabo, kuma ita ce mawallafiyar mujalla 5 na musamman, kuma zuwa yanzu an gudanar da manyan taruka biyu a cikin wannan jami’a. Har ila yau, jami’ar ta wallafa maƙala 7370 a matakin ƙasa da ƙasa.
Martabar Jami’a
A sabon bayanin ranking wanda tsarin ranking na Times ya fitar a shekarar 2023, wannan jami’a ta samu shiga wannan list, inda ta auno wa kanta matsayi na 501 – 600.
Makarantu
_School of Nursing and Midwifery
_School of Medicine
_Faculty of Health
_Faculty of Nutritional Sciences
_School of Paramedicine
_School of Pharmacy
_School of Dentistry
_Sanghar School of Nursing
_Faculty of Rehabilitation Sciences
_Islamabad Health Higher Education Complex
Cibiyoyin Bincike da Nazari
_Health Research Institute
_Health Technology Research Institute
_Sleep Disorders Research Center
_Fertility and Infertility Research Center
_Medical Biology Research Center
_Drug Abuse Prevention Research Center
_Social Development and Health Promotion Research Center
_Nano Drug Delivery Research Center
_Pharmaceutical Sciences Research Center
_Research Center for Environmental Factors Affecting Health
_Medical Technology Research Center
_Oils and Fats Research Center
_Regenerative Medicine Research Center
_Infectious Disease Research Center
_Cardiovascular Research Center
_Comprehensive Center for Stem Cells and Regenerative Medicine
Asibitoci
_Imam Khomeini Hospital Islamabad West
_Shahid Chamran Kangavar Hospital
_Hazrat Rasool (PBUH) Hospital, Javanrood
_Imam Khomeini Hospital, Sanghar
_Hersin Martyrs Hospital
_Dr. Deputy Scene Hospital
_Quds Paveh Hospital
_Shahada Sarpol Zahab Hospital
_Motazadi Hospital
_Abulfazl al-Abbas (AS) Qasr Shirin Hospital
_Dr. Mohammad Kermanshahi Hospital
_Taleghani Hospital
_Farabi Hospital
_Imam Ali Hospital
_Imam Reza Hospital
_Imam Khomeini Hospital
Kwasa-Kwasai
_Medicine
_Nursing
_Midwifery
_Medical Immunology
_Clinical Biochemistry
_ Emergency Nnursing
_Internal Nursing – Surgery
_Radiobiology
_Psychiatric Nursing
_Clinical Psychology
_Medical Physics
_Physiology
_Biostatistics
_Health Education and Health Promotion
_Epidemology
_General Hygiene
_Professional Health Engineering
_Environmental Health Engineering
_Food Hygiene and Safety
_Da sauransu…
Jadawalin Kuɗin Makarantar Kermanshah University of Medical Sciences.
Abubuwan Alfahari
_Samun matsayi na farko a fagen bincike a tsakanin fitattun jami’o’in likitanci na ƙasar, da kuma samun matsayi na biyu a ɓangaren binciken ɗalibai, shi ma a tsakankanin fitattun jami’o’in likitanci na ƙasa, duk a bukin ‘bincike a ilimin likitanci na Razi’ karo na 27.
_Matsayi na farko a fasaha tsakanin rukuni na biyu na fitattun jami’o’in kiwon lafiya na ƙasa, a bukin bincike a ilimin likitanci na Razi, karo na 27
_Bayyana memba na tsangayar ilimi na Kermanshah University of Medical Sciences, Dr. Saber Khazaei a matsayin zakaran kwamitin ilimin kiwon lafiya na matasa, a bukin ‘bincike a ilimin likitanci’ na Razi, karo na 27
Ababen More Rayuwa
Wurin Kwana: Wannan jami’a na da wurin kwana (hostel) guda 8 (5 na ɗalibai mata, 2 na ɗalibai maza, 1 na ɗalibai masu aure) wanda ake tafiyarwa bisa takardar ƙa’idojin masaukai, kuma duba da ƙarancin sarari da wasu dalilai, ana sauke ɗaliban gida, da na waje a masaukai masu zaman kansu (bayan na jami’a).
Waɗannan wuraren kwana sun haɗa da:
_Wurin Kwanan ɗalibai mata na Ayatullah Taleghani: A titin Shahid Beheshti, harabar asibitin Ayatullahi Taleghani.
_Rukunin wuraren kwana na ɗalibai mata mai suna Mofateh: A Farhangian faze 2, tsallaken Furushgahe Refah.
_Wurin kwanan ɗalibai mata na Bostan: A titin Parastar, tsallaken asibitin Imam Reza (as)
_Wurin kwanan ɗalibai masu auren mai suna ‘Milad’: Yana da Sassa biyu, sashe na 1 da sashe na 9 a rukunin masaukai na Milad, Shahrak Moallem, titin Hafez.
_Wurin kwanan ɗalibai maza na Bostan: A titin Parastar, tsallaken asibitin Imam Reza (as)
Wurin kwanan ɗalibai maza na Shahid Alwani: A titin Farhangiyan Faze 2, Titin Kowsar Junobi
Yanayin Wuri
Kermanshah University of Medical Sciences na nan a yankin Hafeziyeh, titin Shahid Beheshti na garin Kermanshah. Ta fuskar yanayin wuri, wannan jami’a tana kusa da cibiyoyi kamar; Sepahe Pasdarane Hazrat Nabiy Akrame Astane Kermanshah, da asibitin Imam Ali (as), asibitin Ayatollah Taleghani da na Shahid Kermanshah.
Saduwa da jami’a
Adireshi: Central Building of Kermanshah University of Medical Sciences, Titin Shahid Behesti, Kermanshah.
Shafin makaranta: www.kums.ac.ir
Tambayoyin da ake yi game da karatu a Kermanshah University of Medical Sciences
Shin wannan jami’a tana bama ɗaliban gida da na waje wurin kwana?
A’a, sakamakon ƙarancin sarari da suke da shi a wuraren kwanansu da kuma wasu dalilai da suka shafi sashen kula da al’adu na ɗalibai, suna samarwa ɗalibai wurin kwana ne a masaukai masu zaman kansu.
Me ake buƙata don yin rijista a wannan makaranta?
Passport, hoto, Transcript
Ko ɗaliban da ba Iraniyawa ba suna buƙatar takardar shaidar koyon yaren farisanci?
Eh, ɗaliban waje suna buƙatar gabatarda takardar shaidar koyon farisanci wadda suka karɓa daga ɗaya daga amintattun cibiyoyin koyon yaren farsi wadda ma’aikatar ilimi ta tantance.