تهران، میدان ولیعصر، جنب سفارت عراق، ساختمان مینو
مشهد، میدان شریعتی، نرسیده به احمد آباد ۱، طبقه بالای بانک دی

Karatu a Urmia

Karatu a Urmia

Loading

Urmia (ma’ana garin ruwa) ɗaya ne daga cikin manyan garuruwan iyakar ƙasar Iran wanda ke lardin Azarbaijan Garbi (tsakanin tafkin urmia da tsaunukan yammacin lardin) a yankin arewa maso yammacin ƙasar. Manufarmu a wannan rubutu ita ce bayanin yanayin karatu, al’adu, yanayin iska, shaƙatawa, yawon buɗe ido, da sauransu na garin Urmia.

Karatu a Urmia

Urmia

Garin Urmia (ana kuma kiransa da sunan Parise Iran) shi ne gari na goma mafi yawan jama’a wanda aka ƙirga mutane 736224 masu zama cikinsa a shekarar 2016. Garin na cikin wani yanki mai yawan tsaunuka (dutsen qiz qal’e, dutsen panje si, johodha, dutsen mah, da sauransu), wannan ya sa garin ke da sanyi da ruwan sama mai yawa a lokacin hunturu, amma a lokacin zafi yanayinsa matsakaici ne.
Garin Urmia na ɗauke da ƙabilu mabambanta amma mafi yawan mutanen garin turkawan azarbaijan ne. Yaren mafi yawancin mutanen garin turkanci ne. Sauran mutanen garin sun haɗa da kurdawa, aramnawa, da ashuri.
Garin na daga cikin yankuna mafi arziki na Azarbaijan kasantuwar cewa yana ɗauke da albarkatun ƙasa da na ɗan’adam masu yawa. Azariyawa musulmi ne kuma ƴan shi’a. A tare da su kuma akwai musulmin ahalus sunnah hanafiyawa, shafi’iyyawa, ashuriyawa, da kuma kiristoci.

Bayani a kan Urmia

Karatu

Akwai jimillar cibiyoyin ilimi da jami’o’i guda 40 a lardin Azarbaijan. Bayanai sun nuna cewa waɗannan cibiyoyin sun wallafa maƙalolin ilimi guda 42549 ciki har da maƙalar mujalla 6193 da ta taro guda 22178, da wasu maƙaloli a matakin ƙasa da ƙasa. Daga cikin ingantattun jami’o’in garin Urmia akwai Urmia University of Medical Sciences. Domin samun ƙarin bayani kuna iya garzayawa maƙalar Karatu a Urmia University of Medical Sciences.

Jami'o'in Urmia

Zirga-Zirga

Garin Urmia shi ne gari na biyu mafi cinkoson ababen hawa, an ƙarfafa tsarin zirga-zirga da motocin gama-gari domin rage yawan cinkoson. Akwai motocin autobus masu yawo iya cikin gari, da motocin taksi da mutane ke amfani da su. Yawan ababen hawa da hayaƙi a garin ne ya sanya garin ya shiga sahun garuruwan da suka fi kowasu garuruwa gurɓataccen iska a Iran.

Nishaɗi da wuraren yawon buɗe ido

Garin Urmia na da yanayi na musamman, hakan ya sa ya zama ɗaya daga cikin garuruwan yawon buɗe ido.
_ Tafkin Urmia
_ Cocin Naneh Maryam
_ Tafkin Marmishow
_ Tafkin Dalamper
_ Ƙauyen Band
_ Ginin Shahardari
_ Seh Gonbad
_ Shaikh Tappe Park
_ Sulak waterfall
_ Kasuwar Urmia
_ Cocin Marsargiz
_ Masallacin Sardar
_ Gidan tarihi na Urmia
_ Babban masallaci
_ Gidan Ansari
_ Kogon Tamtameh
_ Gidan ƙanƙara na Doqoz Pelle
_ Cocin St. Peter
_ Goe Tappeh
_ Makarantar Hedayat
_ Gidan Shaharbani (babban gidan tarihi na anthropology)
_ Da sauransu…

Yawon buɗe ido a Urmia

Cibiyoyin Magani

A garin Urmia ne aka buɗe asibitin zamani na farko, cibiyar karatun likitanci ta farko, tashar talabijin ta cikin gida ta farko, wallafe-wallafen cikin gida na farko, da kuma cibiyar wasan volleyball ta farko a ƙasar Iran.
_ Asibitin Imam Khomeini
_ Asibitin Imam Reza
_ Asibitin Shahid Erfaniyan
_ Hazrat Fatemeh (PBUH) Specialized Polyclinic
_ Asibitin Shahid Qalipur Bukan
_ Asibitin Hazrat Zahra (AS)
_ Asibitin Ayatollah Taleghani
_ Asibitin Khatamal Anbiya
_ Asibitin Shahid Motahhari
_ Asibitin Qamar Bani Hashim Khoe
_ Asibitin musamman na zuciya na Sayyedu Shohada (AS)
_ Asibitin Nabi Akram (S)
_ Asibitin Fajr Mako
_ Asibitin Shahid Madani Khoe
_ Asibitin Abbasi Miyando Ab
_ Asibitin Azarbaijan
_ Cibiyar magani ta Farabi
_ Asibitin Dr. Solati
_ Da sauransu…

Hotal Hotal

_ Ana Hotel
_ Arya Hotel
_ Park Hotel
_ Kara Hotel
_ Sahel Hotel
_ Iran Park Hotel
_ Mehmansarsa Jahangardi Urmia
_ Mah Kimiya Hotel
_ Bahar Apartment Hotel
_ Morvarid Hotel
_ Nasir Hotel
_ Da sauransu…

Ɗakunan Karatu

_ Laburaren Shahid Bahnar
_ Laburaren Markazi
_ Laburaren Shahid Motahhari
_ Laburaren gari na Allameh Tabataba’ei
_ Laburaren gari na Farhang
_ Laburaren gari na Qa’em (AF)
_ Laburaren gari na Shahid Mehdi Amini
_ Laburaren Imam Ali (AS)
_ Laburaren Shahid Ibrahim Mazaheri
_ Laburaren Farhang
_ Laburaren Qur’an wa Itrat
_ Laburaren Bamdad Omid
_ Laburaren Baba Sa’ei
Da sauransu

Cibiyoyin Kasuwanci

Saboda kasancewar garin Urmia a bakin iyaka, yana da cibiyoyin kasuwanci masu yawa.
_ Milad Noor Shopping Center
_ Berlan Shopping Center
_ Turk Mall
_ Pardis Shopping Center
_ Berelian Shopping Center
_ Pasaj Jalali
_ Tooba Shopping Center
_ Pasaj Tanakura
_ Pasaj Azarbaijan
_ Pasaj Paku
Amirkabir Shopping Center
_ Da sauransu…

Related Posts
Leave a Reply