Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Mashhad

Karatu a Mashhad

Loading

Watakila yanayin karatu a Mashhad ya zama ɗaya daga cikin tambayoyinku. A wannan rubutun mun yi ƙoƙarin kawo muku bayanai game da birnin Mashhad wanda hakan zai taimaka muku wajen yin zaɓi mai kyau don cigaba da karatunku.

Karatu a Mashhad

Mashhad

Cikakken sunan Mashhad shi ne Mashhadu Rida, babban birnin ne a arewa maso gabacin ƙasar Iran kuma shi ne cibiyar lardin Khorasan Razavi. Yawan mutanen da ke zaune a birnin Mashhad ya kai kimanin mutum 3,001,184 wanda hakan ya sanya ya zamo birni na biyu mafi yawan jama’a a Iran kuma na 99 a duniya. Kasantuwar haramin Imam Rida (a.s) da ke cikin wannan birni, a kowace shekara yana karɓar baƙuncin maziyarta sama da mutum miliyan 29 daga ciki da wajen ƙasar.

Bayani game da birnin Mashhad

Zirga-Zirga

Ya kamata ku san cewa akwai hanyoyin jirgin ƙasa da na sama da dama a Mashhad waɗanda suka sada garin da sauran garuruwan ƙasar. Filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na HashemiNejad ɗaya ne daga cikin fiayen jirgin sama mafi girma faɗin a ƙasar wanda jiragen ciki da na waje suke tashi a cikinsa.

Abubuwan buɗe ido

Mashhad tsohon gari ne mai ɗauke da ɗimbin tarihi tare da abubuwa masu jan hankali na buɗe ido. Daga cikin wuranen tarihi na Mashhad akwai: Hubbaren Nadershah, Hubbaren Khajerabi, Hubbaren Ferdowsi, Tashar Rah Ahan, Gonbad Khashti, Gonbad Haronieh, da Makarantar Abbasghalekhan.

Wuraren buɗe ido na ɗabi’a da ke kusa da birnin Mashhad kuma sun haɗa da: Gine-Ginen Shandiz, Torghabeh, Chalidare, gian zoo na Vakil-Abad, da kuma Jejin Vakil-Abad.

Wurin shaƙatawa na Torgh (Inqilab) a gefen kudu maso gabacin Mashhad wanda ke kusa da ofishin ƴansandan hanya, ɗaya ne daga cikin manyan wuraren shaƙatawa masu masaukai da aka tanada domin ‘yangari da maziyarta. An samar da wannan park ɗin ne a shekarar 1961, inda aka yi masa kwaskwarima a shekarar 2000. Wannan park na Torgh yana da wuraren shan iska, nishaɗi, wasanni, kasuwanci, tare da filin jeji mai girman hekta 210, da kuma fili mai girman murabba’in mita 112000 wanda ake rayuwa a ciki. Har ila yau, wannan park ɗin na da nau’in itatuwa daban-daban wanda nau’in ‘acacia’ da ‘harshen sparrow’ su ne suka fi yawa a ciki.

Wurare masu jan hankali na Mashhad
Sadarwar ƙasa da ƙasa

Ofisoshin jakadanci da ke aiki a Mashhad a halin yanzu:

Turkey Turkey (2014 zuwa yanzu)
Iraq Iraq (2007 zuwa yanzu)
Kyrgyzstan Kyrgyzstan (1996 zuwa yanzu)
Turkmenistan Turkmenistan (1995 zuwa yanzu)
Tajikistan Tajikistan (1995 zuwa yanzu)
Pakistan Pakistan (1975 zuwa yanzu)
Afghanistan Afghanistan (1921 zuwa yanzu)

Cibiyoyin Magani

_ Asibitin Imam Reza
_ Asibitin Gha’em
_ Asibitin Ido ta Khatamul Anbiya (s)
_ Asibitin Shahid Hashemi Nejad
_ Asibitin Akbar ta yara
_ Asibitin Dakta Shaikh
_ Asibitin Razavi
_ Asibitin Shahid Kamyab
_ Asibitin Dr. Shariati
_ Asibitin Ayatollah Taleghani
_ Cibiyar bincike da maganin rashin haihuwa ta Milad
_ Asibitin Ummul Banin (as)
_ Asibitin Ibn Sina
_ Asibitin tiyatar ƙwararru ta Alavi
_ Asibitin Montasirieh
_Da sauransu…

Nishaɗi da wuraren yawon buɗe ido

_ Haramin Imam Rida (a.s)
_ Khane Tawakkuli Mashhad
_ Khane Darugheh
_ Bagh Melli
_ Park Mellat
_ Jangal Jig
_ Chalidareh
_ Hubbaren Ferdowsi
_ Torghabeh
_ Park Koohsangi
_ Mojhaye Abi
_ Masallaci Goharshad
_ Park Vakil Abad
_ Khane Malak
_ Bazeh Hoor Chahartaqi
_ Hubbaren Nadershah Afshar
_ Hubbaren Pir Palandor
_ Hamam Shah Mashhad (Gidan tarihi na anthropology)
_Da sauransu…

Karatu a Mashhad

Akwai kimanin cibiyoyin ilimi da jami’o’i guda 76 a lardin Khorasan Razavi. Bincike ya nuna cewa a waɗannan cibiyoyin, an wallafa maƙalolin ilimi kimanin guda 145221 waɗanda suka haɗa da maƙalolin mujalla guda 27970 da guda 63464 a tarukan cikin gida, tare da guda 27970 a matakin ƙasa da ƙasa. Daga cikin fitattun jami’o’in garin Mashhad akwai Mashhad University of Medical Sciences, Ferdowsi University, da kum Imam Reza University.

Jami'o'in Mashhad

Dalilin karatu a Mashhad

  • Birnin Mashhad na iya zama zaɓi mai kyau domin yin karatu, dalili kuwa shi ne idan an kwatanta da kuɗin karatun ɗalibai a sauran garuguwan Iran, Mashhad ta fi sauƙin karatu. Hakazalika farashin rayuwa a garin Mashhad ya fi sauƙi bisa ga sauran garuruwa, sannan kuma ɗalibai za su iya amfanuwa sosai da zamansu a wannan gari.
  • Takardun shaidar kammala karatu waɗanda jami’o’in Mashhad ke ba wa ɗaliban ƙasashen waje, takardu ne waɗanda ingancinsu ya tabbata a ƙasashe da dama na Europe, Amerika, da sauran nahiyoyin duniya.
  • Kusancin su da ƙasashen maƙota da kuma kamanceceniyar al’adu tsakaninsu
  • An tanadarwa jami’o’in gwamnati da ma masu zaman kansu kayan aiki na karatu masu inganci. Kayan aiki kamar: Laburare, ɗakunan gwaje-gwaje, wuraren motsa jiki, wuraren zane-zane da sauran ayyukan ɗalibai.
  • Mashhad cike take da gine-gine na al’adu da na tarihi waɗanan gine-ginen tsoffi ne kuma sun daɗe sosai. Samuwar waɗannan abubuwan jan hankali na al’adu da na tarihi na iya zama abin sha’awa da tunani, da kuma bincike ga ɗaliban da ke karatu a fannonin sanin al’adu da fasaha na Mashhad.

Cibiyoyin Kasuwanci

_ Rukunin kasuwanci na Almas Sharq
_ Cibiyar kasuwnci ta Armitaj
_ Cibiyar kasuwanci ta Vesal
_ Cibiyar sayayya ta Proma
_ Borj Alton
_ Kiyan Center
_ Bazaar Jannat
_ Cibiyar sayayya ta Khorshid
_ Cibiyar kasuwanci ta Salman
_ Bazaar Ferdowsi
_ Rukunin kasuwanci na Zist Khavar
_ Rukunin kasuwanci na Vilaj Tourist
_ Rukunin kasuwanci na Nika
_Da sauransu…

Jerin fitattun jami’o’in garin Mashhad:

Related Posts
Leave a Reply