Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Isfahan

Karatu a Isfahan

Loading

A wannan rubutun, mun yi nufin tattauna batutuwa game da garin Isfahan daga mahanga daban-daban domin ku sami damar jinjina yiwuwar cigaba da karatunku a Isfahan.

Karatu a Isfahan

Isfahan

gari ne mai ɗimbin tarihi, ɗauke da wuraren tarihi da yawon buɗe ido a tsakiyar Iran. Wannan garin shi ne babban birnin lardin Isfahan sannan kuma gari na uku a yawan jama’a, bayan Tehran da Mashhad. Har ila yau, garin Isfahan shi ne babban gari na 14 a yawan jama’a a gabas ta tsakiya, inda yake ɗauke da kimanin mutum 5,120,850. Garin na Isfahan ya shahara da tsarin gine-gine mai ƙayatarwa cikin salo irin na Iran, rufaffin gadodin tsallaka titi, masallatai da hasumiyoyi na musamman. Hakan ya sabbaba ake yi wa wannan gari kirari da laƙabin “rabin duniya”. Shataletalen “Naqshe Jahan” babban misali ne na tsarin gine-gine irin na Iran. Wannan birni na Isfahan yana da yankuna 15. Daga cikin abubuwan tarihi na wannan kyakkyawan garin akwai hasumiyar Jonban, sioseh pol, pol khaju, fadar chehel siton, fadar Aali Qapu, masallacin Shaikh Lotfollah, Zayandehrud, cocin Vanak, makarantar Chaharbagh, da Hotel Abbasi.

Haka kuma garin yana da wuraren buɗe ido na addini masu yawa. Kamar: Gidajen ibada, gidajen tarihi, majami’u, maƙabartu da sauransu. Akwai masana’antu masu aiki a garin Isfahan, kamar manyan kamfanonin ƙera jiragen sama na Iran, Mobarakeh Steel Complex, Matatar mai, masana’antar Optics ta Isfahan, Snova, Polyacryl, da kamfanin ƙarfe na Isfahan.

Bayani game da Isfahan

Zirga-Zirga

Garin Isfahan wanda ke kan manyan titunan tsakiyar ƙasar Iran, yana da hanyoyin zirga-zirgar ababen hawa masu yawa idan aka kwatanta da sauran garuruwan ƙasar ta Iran. Babban filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na wannan garin mai suna “filin jirgin sama na Shahid Beheshti” yana arewa maso gabacin garin kilomita 18 a wajen gari. Akwai kuma tashar jirgin ƙasa ta Rah Ahan wadda ɗaya ce daga cikin fiyayyun tashoshin jirgin ƙasa na Iran. Kamar dai sauran birane, garin yana da tarin motocin bas a cikin gari da tsahoshin fasinja a wajen gari. Yana kuma da layin dogo na cikin gari (metro) guda 5 mabambanta.

Wuraren shaƙatawa

Royaha Amusement Park wurin shaƙatawa ne da wasanni wanda ke samun maziyarta masu yawon buɗe ido a kowace shekara. City Center kuwa wurin shaƙatawa ne na cibiyar kasuwanci mafi girma ta garin. Park ɗin Safeh da ke gindin dutsen Safeh, ɗaya ne daga cikin wuraren shaƙatawa na jeji kuma a ciki akwai abubuwa kamar cinema, wurin wasan bowling, motocin wasa, da sauransu. Daga cikin abubuwan buɗe ido na wannan gari akwai Najwan Forest Park, Absar Water Park, Bam Shahr, da Bagh Fadak. Har ila yau, akwai sinima guda 9 a wannan garin. Garin Isfahan na da hekta 37000 wato murabba’in mita miliyan 37 na koren fili a cikin gari; wato murabba’in mita 24 ga kowane mutum, wanda hakan ya maida shi na ɗaya a kaf manyan garuruwan Iran.

Jami'o'in Isfahan

Sadarwa ta ƙasa da ƙasa

Ofishin jakadanci ɗaya kawai ke aiki a Isfahan a halin yanzu:

پرچم روسیه.svg Russia

 

Karatu

A lardin Isfahan akwai cibiyoyin ilimi da jami’o’i 67 tare da ɗalibai 140374, da malamai 6244 a cikinsu. Bincike ya nuna cewa, a waɗannan cibiyoyi an wallafa maƙalar ilimi guda 176284 waɗanda suka ƙunshi maƙalar mujalla guda 28996 da maƙalar taro guda 69198, da maƙala 28996 a matakin ƙasa da ƙasa. Mun gabatar da bayanai masu muhimmanci da kuke buƙata domin yin rijista a fitattun jami’o’in garin Isfahan irinsu Isfahan University of Medical Sciences, Isfahan University of Technology, da Azad University Najafabad. Domin samun ƙarin bayani game da waɗannan makarantun za ku iya komawa ga waɗannan maƙaloki: Karatu a Isfahan University of Medical Sciences, Karatu a Isfahan University of Technology, da Karatu a Azad University Najafabad

Abubuwan masu jan hankali na Isfahan

  • Idan kuna da niyyar zaɓar garin Isfahan a matsayin garin da za ku zauna ku yi karatu, babu shakka hakan zaɓi ne mai kyau domin kuɗin makarantar karatu a wannan garin akwai sauƙi idan an kwatanta da sauran manyan biranen Iran kamar Tehran da sauransu. Amma ku san cewa kuɗin muhalli na iya kawo muku cikas. Saboda haka abunda ya fi shi ne ku yi amfani da hostel ko masaukan baƙi da suke cikin gari.
  • Jami’ar Isfahan, hakazalika Jami’ar Fasaha ta Isfahan suna daga cikin fitattu kuma mafi ingancin jami’o’in ƙasar Iran, shaidar da suke ba ma ɗalibai bayan kammala karatu tana da kima sosan gaske a idon sauran makarantun ƙasar Iran, kuma tana da matsayi na musamman. Waɗannan jami’o’i suna da kayan aiki da tsarukan karatu mafi inganci da suka tanada irinsu laburare, ɗakunan gwaje-gwaje, rukunan wasanni da shaƙatawa, wuraren cin abinci duk domin ɗalibai.
  • Garin Isfahan shi ne gari na uku mafi girma kuma mafi yawan jama’a a Iran. Ya yi fice a matsayin babban birnin al’adu na tarihin musulunci. Har ila yau, sakamakon kyakkyawan tsarin gine-gine salon Iran da yake da shi da kuma tituna masu kyau, rufaffin gadoji, Kyawawan tunnels, gine-ginen sarauta, masallatai, da sauransu, ana yi masa kirari da “Rabin Duniya” a Iran. Saboda haka wannan gari zai iya zame muku zaɓi mai kyau ga ɗaliban kwasa-kwasai daban-daban.
Related Posts
Leave a Reply

Your email address will not be published.Required fields are marked *