Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Tehran

Karatu a Tehran

Loading

Idan kun zabi yin karatu a Tehran, to ku sani cewa garin Tehran a matsayinsa na babban birnin ƙasar Iran kuma gari mafi yawan jama’a, yana ɗauke da wurare da kayan karatu da suka dace da ɗalibai.

A birnin Tehran akwai kimanin cibiyoyin ilimi da jami’o’i 140 wanda a cigaban wannan rubutun za mu ambato muku fitattu daga cikinsu tare da bayanai a kansu.

Karatu a Tehran

Rayuwa a Tehran

Garin Tehran kasantuwarsa kusa da wurare daban-daban, a kuma sansanin zirga-zirga na jirgin ƙasa da na sama zuwa duka garuruwan Iran, ɗaya ne daga cikin garuruwa mafi kyau ga ɗalibai masu son ci gaba da karatu

Wannan birnin yana da Cibiyar kasuwanci mai girma sosai kuma nau’i daban-daban. Wuraren tarihi شهر تهران باعث شده تا نظر گردشگران و توریست‌های سایر کشورهای جهان را به خودش جلب کند. Amma ɗaya daga cikin illolin zama a wannan gari shi ne tsadar rayuwa wanda hakan zai iya tsaurara muku rayuwa cikin ƙanƙanen lokaci. Mai yiwuwa ma kuɗin da za ku buƙata don rayuwa a garin Tehran ya lunka na sauran garuruwa.

Bayani a dunƙule game da garin Tehran

Rayuwar ɗalibai a Tehran

Idan kuna da niyyar zaman hostel a Tehran na tsawon lokacin karatunku yana da kyau ku san cewa kuɗin hostel na jami’o’in Tehran za su kai aƙalla dala 500 a kowane zangon karatu.

Mai yiwuwa kuma ku yi tunanin kama masauki a wajen makaranta nan kuma za ku biya toman 100,000 zuwa sama a kowane dare ɗaya.

Duba da yawan makarantun da ke karɓar ɗalibai ba tare da jarabawar shiga ta “konkur” ba a cikin garin na Tehran, akwai kwasa-kwasai masu yawa mabambanta da ake yi a waɗannan makarantu.

A ƙarshe, wannan gari na Tehran yana da abubuwa da yawa da suka maida shi zaɓi mai kyau domin karatu.

Jami'o'in Tehran
Jami'o'in Tehran

Karatu a Tehran

Har ila yau, idan kuna tunanin ci gaba da karatunku a wannan gari na Tehran, ya kamata ku san cewa birnin Tehran ɗaya ne daga cikin biranen ilimi na ƙasar Iran, ɗauke da cibiyoyin ilimi guda 140. Jami’o’in lardin Tehran suna da lambar yabo ta mallakar mujallolin ilimi guda 749 kuma zuwa yanzu sun wallafa guda 11423. Lardin Tehran ya karɓi baƙuncin tarukan ilimi guda 1464, tare da lakcocin ilimi guda 704. Masu bincike na jami’o’i da cibiyoyin ilimi na lardin Tehran sun sami nasarar wallafa maƙalolin ilimi guda 989686 waɗanda suka haɗa da 148352 na labarai, da kuma 399385 a taruka da wallafe-wallafe. Akwai kuma guda 148352 da suka wallafa a matakin ƙasa da ƙasa. A shekarar 2018, an samu kimanin ɗalibai 1,464,783 masu karatu a jami’o’in lardin Tehran, lokacin akwai malamai kimanin 152,188 masu koyarwa da membobin tsangayar ilimi.

Abubuwa masu jan hankali a Tehran

Nishaɗi da wuraren yawon buɗe ido

Kasancewarsa babban birnin tarayya na ƙasar Iran, birnin Tehran ɗaya ne daga cikin wuraren buɗe ido masu muhimmanci na ƙasar. Akwai ɗaruruwan wuraren shaƙatawa a Tehran wanda za mu ambato muku wasu daga ciki a cigaban wannan rubutun:
_ Fadar Golestan
_ Gidan Tarihi na tsohuwar Iran
_ Rukunin fadodi na Sa’adabad
_ Darband
_ Gidan Tarihi na Moghaddam
_ Lambun Ferdows
_ Rukunin fada na Niyavaran
_ Bam Tehran
_ Pol Tabi’at
_ Bagh Melli
_ Bagh Negarestan
_ Mega Mall
_ Fadar Mas’oudieh
_ Chitgar Park
_ Tuchal
_ Borj Milad
_Da sauransu…

Cibiyoyin Magani

_ Asibitin Akhtar
_ Asibitin Akbar Abadi
_ Asibitin Imam Husain
_ Asibitin Sinai
_ Asibitin Shafa Yahya’iyan
_ Asibitin Shohadae Haftome Tir
_ Asibitin Shohadae Yaft Abad
_ Asibitin Ali Asghar
_ Asibitin Farabi
_ Asibitin Firouzgar
_ Asibitin Luqman Hakim
_ Asibitin Imam Khomeini
_ Asibitin Amir A’alam
_ Asibitin Baharlor
_ Asibitin Bahrami
_ Asibitin Mirza Kuchak Khan
_ Asibitin Shahid Ashrafi Isfahani
_ Asibitin Kudakane Mufid
_ Asibitin 15 Khordad
_ Asibitin Shohadae Tajrish
_ Asibitin Shahid Muhammad Hosein Fahmide
_ Asibitin Shahid Modarres
_ Asibitin Shahid Hashemi Nejad
_ Asibitin Psychiatry na Iran
_ Asibitin Hazrat Fatima (S)
_ Asibitin Shahid Rajaei
_ Asibitin Javahiri
_ Asibitin Najmieh
_ Asibitin Hazrat Rasulul Akram (s)
_ Asibitin Dr. Shariati
_ Asibitin Razi
_ Asibitin Mata na Arash
_ Asibitin Firouz Abadi
_ Asibitin Ruzbeh
_Da sauransu…

Ɗakunan Karatu

_ Laburaren Arghavan
_ Laburaren Melli
_ Laburare da gidan tarihi na Melli Malak
_ Laburaren Ashrafi Isfahani
_ Laburaren Amirkabir
_ Laburaren Lavizan
_ Laburaren Andishe
_ Laburaren Allame Amini
_ Laburaren Shaqa’eq
_ Laburaren Sizdahe Aban
_ Laburaren Shahid Mahlati
_ Laburaren Shahrake Garb
_Da sauransu…

Cibiyoyin Kasuwanci

_ Cibiyar kasuwanci ta Arg, Tajrish
_ Cibiyar kasuwanci ta Palladium
_ Rukunin kasuwanci na Iran Mall
_ Cibiyar kasuwanci ta Galleria
_ Cibiyar kasuwanci ta Tirajeh
_ Cibiyar kasuwanci ta Sana
_ Cibiyar kasuwanci ta Sam Center
_ Cibiyar kasuwanci Lux
_ Cibiyar kasuwanci ta Bam Land
_ Cibiyar kasuwanci ta Rosha
_ Atlas Mall
_ Cibiyar kasuwanci ta Kourosh
_ Cibiyar kasuwanci ta Milad Noor
_ Lavasan Sky Center
_ Cibiyar kasuwanci ta Gandhi
_ Kasuwar gargajiya ta Sattar Khan
_ Cibiyar kasuwanci ta Borj Artmes
_ Rukunin kasuwanci na Mega Mall
_ Cibiyar kasuwanci ta Tandis
_ Kasuwar Marvi
_Da sauransu…

Jerin ingattatun jami’o’i na garin Tehran:

Related Posts
Leave a Reply