Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Jami'ar Hormozgan

Karatu a Jami’ar Hormozgan

Loading

Jami’ar Hormozgan ɗaya ce daga cikin jami’o’in Ma’aikatar Ilimi, Bincike da Fasaha. Jami’ar wadda ke garin Bandar Abbas a tsakiyar lardin Hormozgan, kilomita 9 a babban titin Bandar Abbas zuwa Minab. Ku kasance tare da mu domin samun bayanai game da karatu a wannan jami’ar.

Gabatarwa

An kafa Jami’ar Hormozgan bisa zartarwar majalisar faɗaɗa karatun gaba da sakandare a takardar da suka fitar ranar 2/10/1991, tare da lasisin ƙaddamar da kwasa-kwasan karatu 6 a matakin digiri (Industrial Engineering, Mechanical Engineering, Mathematics Teaching, Physics Teaching, Persian Literature Teaching) a cikin gomman Fajr na shekarar 1991. Ta fara gudanar da ayyukanta na ilimi ta hanyar canja muhallin kwalejin fasaha ta Hormozgan (mai alaƙa da Jami’ar Shiraz) a shekarar 1992.

Akwai gine-gine masu girman murabba’in mita 55000 wadanda ake amfani yazu haka a jami’ar (Admin block murabba’in mita 6000, Hostel murabba’in mita 2000, Azuzuwa, wuraren bincike, da cibiyoyin al’adu murabba’in mita 29000).

A halin yanzu akwai kimanin ɗalibai 5500 da malamai 500 da suke kai-komo a wannan jami’a. Bincike ya nuna cewa zuwa yanzu wannan jami’a ta wallafa maƙalolin ilimi guda 4752 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida. Jami’ar Hormozgan ta mallaki lambar yabo sannan ta wallafa mujalla biyu na musamman, kuma ta shirya manyan taruka 2 zuwa yanzu. A shekarar 2023, masu bincike na wannan jami’ar ta Hormozgan sun wallafa mafi yawan maƙalolinsu ne da muhimman kalmomin “Persian Gulf” da “Covid-19”.

Karatu a Jami'ar Hormozgan

Martabar Jami’a

 • Samun matsayi na farko a jami’o’in da suka fi samarwa da ɗalibai tallafin karatu daga cibiyoyi masu zaman kansu, a tsakanin jami’o’in ƙasa bakiɗaya.
 • Samun matsayi na 7 a tsarin kimiyyar duniyar Musulunci (ISC) a fannin ayyukan zamantakewa
 • Koriyar jami’a (Green University) ta 25 a Iran, a tsarin martabawa na Greenmetric na duniya
 • Zakaran gasar Olympics ta rairayin bakin teku na ɗaliban Iran
 • Matsayi na 32 a jami’o’in Iran a shekarar 2023, a tsarin ranking na Times
 • Matsayi na 9 tsakanin jami’o’in Iran a ranking na fannoni na tsarin Shanghai a shekarar 2023, a fannin Agriculture
 • A sabon rahoton da tsarin ranking na Times ya fitar wanda shi ne na ƙarshe, jami’ar Hormozgan ta cimma matsayi na 1201 – 1500 a jami’o’in duniya

Kuɗin makarantar jami’ar Hormozgan

 

Makarantu

 • Faculty of Humanities
 • Faculty of Management and Accounting
 • Faculty of Basic Sciences
 • Faculty of Marine Science and Technology
 • _Faculty of Engineering
 • Faculty of Agriculture and Natural Resources
 • Faculty of Chemical and Petroleum Engineering

Kwasa-Kwasai

 • Department of Electrical and Computer Engineering
 • Department of Civil Engineering
 • Department of Mechanical Engineering
 • Department of Industrial Engineering
 • English Language
 • Sports Science
 • Social Sciences
 • Persian Literature
 • Handicrafts
 • Geography
 • Educational Science
 • Counseling
 • Law
 • Statistics Group
 • Department of Physics
 • Mathematics Group
 • Department of Geology
 • Department of Chemistry
 • Department of Marine Biology
 • Fisheries Department
 • Department of Atmospheric and Oceanic Non-Biological Sciences
 • Department of Accounting and Economics
 • Department of Commercial Management and Customs Affairs
 • Industrial and Government Management
 • Department of Agricultural Engineering
 • Department of Natural Resources Engineering
 • Department of Chemical Engineering
 • Department of Agricultural Sciences and Engineering
 • Department of Water Science and Engineering
 • Department of Industrial Engineering
 • Department of Computer Engineering

Karatu a Jami'ar Hormozgan

Wuraren bincike

 • Coastal Desert Research Institute
 • Mangrove Forest Research Institute
 • Study and Research Center (Hormoz Research Institute)
 • Secretariat of the specialized working group of education, research, technology and innovation of Hormozgan Province
 • The research core of Children and Adolescent Literature
 • Deep Learning Research Core
 • Research Core of Water and Environment
 • Educational and Behavioral Science Research Core
 • Innovative Program Website and Message Design
 • Medicinal Plant Research Core
 • Tsunami and Erthquake

Kayan Aikin Jami’ar Hormozgan

Jami’ar Hormozgan ta ware gagarumin kasafin kuɗi don samar da ƙarin wurare da kayan aiki saboda muhimmancin darusan da ake yi a jami’ar da kuma haɓaka matakinta na ilimi. Duba da yanayin wurin da jami’ar take, sabis ɗin jigilar ɗalibai na yau da kullum don sauƙaƙe wa ɗalibai zirga-zirga zuwa wuraren karatunsu, ɗaya ne daga cikin abubuwan wannan jami’a da ya kamata a ambata. Sauran kayan aiki sun haɗa da:

 • Laburare
 • Sabis ɗin abinci
 • Kafteriyar jami’a
 • Koren filin jami’a
 • Wurin ajiye ababen hawa
 • Internet
 • Kayan wasanni
 • Ingantattun ɗakunan gwaje-gwaje
 • Wurin kwana

Wurin kwanan ɗalibai na jami’ar Hormozgan

Wurin kwana na Pardis mai ɗaukar mutum 620 domin ɗalibai. Wannan hostel ɗin na maza ne sannan kuma yana da ɗakuna 108. Wurin kwana na Shahid Zakiri na ɗalibai maza, mai ɗaukar kimanin mutum 200 a block 2. Block na farko yana da suite 14 masu ɗaukar mutum 6, ɗayan kuma yana da suite 8 masu ɗaukar mutum 18 tare da zauren amfani da kwamfuta, sai Wurin kwana na Fatimieh na ɗalibai mata mai ɗaukar kimanin mutum 600 ɗauke da abubuwa kamar haka:

 • Ɗakin karatu
 • Zauren wasanni
 • Zauren kwamfuta

Karatu a Jami'ar Hormozgan

Yanayin Wuri

Bandar Abbas na ɗaya daga cikin manyan biranen ƙasar, haka kuma yana ɗaya daga cikin manyan tashoshin jiragen ruwa na lardin Hormozgan na ƙasar Iran. Watakila ku ji daɗin sanin cewa ana yi wa ƙasar Korea ta kudu da Bandar Busan kallon ƴan’uwan Bandar Abbas. Adireshin wannan jami’ar kuma yana garin Bandar Abbas, nisan jami’ar zuwa cikin gari kuma kilomita 9 ne a hanyar Minab.

Jami’ar Hormozgan na nan a Bandar Abbas a kan hanyar zuwa matatar iskar gas ta Serkhon. Ta fuskar yanayin wuri kuma, jami’ar na kusa da cibiyoyi kamar Kwalejin Human Science ta jami’ar Hormozgan, Sakhteman Rudaki, Ofishin ƴansanda na hanyar Minab, da cibiyar musayar lasisi ta garin Bandar Abbas. Tashar bus mafi kusa da wannan jami’a ita ce tashar bus ta Shahri wanda hakan ya sauƙaƙe zirga-zirga zuwa wannan muhalli ga ma’aikata marasa abun hawa.

Adireshi: Bandar Abbas, Babbar hanyar Palayeshgahe Gaz Serkhon

Shafin jami’a: https://hormozgan.ac.ir

Related Posts
Leave a Reply