[gtranslate]
تهران، میدان ولیعصر، جنب سفارت عراق، ساختمان مینو
مشهد، میدان شریعتی، نرسیده به احمد آباد ۱، طبقه بالای بانک دی

Karatu a Jami'ar Guilan

Karatu a Jami’ar Guilan

Loading

Jami’ar Guilan (University of Guilan) na ɗaya daga cikin jami’o’in da ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimi, kana ɗaya ce daga cikin manyan jami’o’in arewacin ƙasar Iran. WannanJami’ar na daga cikin jami’o’in gwamnati mafi inganci. An assasata ne a shekarar 1974 bisa amincewar majalisar faɗaɗa karatun gaba da sakandare. Ku kasance tare da mu don samun bayanai masu amfani game da yanayin karatu a wannan makarantar.

Gabatarwa

An assasa jami’ar Guilan a shekarar 1974 bisa amincewar majalisar faɗaɗa karatun gaba da sakandare. An buɗa jami’ar ne a tsakanin shekarar 1975 zuwa 1976 a ƙarƙashin yarjejeniyar gwamnatin Iran da tsohuwar gwamnatin ƙasar Jamus, inda jami’ar ta fara aikinta na koyarwa a shekarar 1977 tare da ɗaukar ɗalibai 155 a kwasa-kwasai 9. A shekarar 1977, kwalejin Management da kwalejin Business na garin Rasht (assasawar shekarar 1967) waɗanda a wancan lokacin su kaɗai ne makarantun gaba da sakandare a kaf lardin Gilan, aka haɗe waɗannan makarantun biyu da jami’ar Guilan inda suka ci gaba da ayyukansu na koyarwa tare da ɗalibai 605 a kwasa-kwasai 14 har zuwa ƙarshen shekarar 1979.

Jim kaɗan bayan aukuwar juyin musulunci na Iran, wannan jami’a ta Guilan ta ci gaba da aiki a ƙashin kanta ba tare da dogaro da ƙasar Jamus ba. Ta ci gaba da karatu tare da ɗalibai 500 da kwas 8, kafin daga bisani a samar da makarantun Basic Sciences, Technology, Agricultural Science, Human Science, da Medicine. Daga baya kuma aka gina makarantun Physical Education, Sport Science, Natural Resources, Architecture, da Art.

A halin yanzu akwai ɗalibai 16229 da malamai 883 a wannan jami’a. Bincike ya nuna cewa jami’ar ta wallafa maƙalar kimiyya guda 18089 zuwa yanzu, a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida. Jami’ar ta mallaki lambar yabo sannan kuma ta wallafa mujalla 18 na musamman, kuma ta shirya taruka 30 zuwa yanzu. A shekarar 2023, masu bincike na wannan jami’a sun wallafa mafi yawan maƙalolinsu ne da kalmomin “IRAN” da “ACCOUNTING” a matsayin muhimman kalmomi.

Karatu a Jami'ar Guilan

Martabar Jami’a

A tsarin ranking na Shanghai, Jami’ar Guilan ta samu matsayi na 8 a tsakanin jami’o’in ƙasar Iran a shekarar 2014. A tsarin ranking na TIMES kuma, jami’ar ta samu matsayi na 6 tsakanin jami’o’in Iran a shekarar 2019.

A sabon sakamakon ranking wanda tsarin URAP ya wallafa, Jami’ar Guilan ta samu matsayi na 1092 a tsakanin jami’o’in duniya, da kuma matsayi na 13 a tsakanin jami’o’in ma’aikatar ilimi ta Iran. Har ila yau, Jami’ar Guilan ta samu matsayi na 260 a tsakanin jami’o’in yankin Asia a tsarin ranking na TIMES a shekarar 2018. Jami’o’i 359 ne suka samu shiga wannan ranking na shekarar 2018 daga yankin Asia bayan an tantancesu. Daga ƙasar Iran kuma Jami’ar Guilan, Jami’ar Ferdowsi ta Mashhad, da Jami’ar Isfahan, su ne suka samu makin da ake buƙata suka kuma samu matsayi na 200 zuwa 300 na fitattun jami’o’in yankin Asia.

Jami’ar Guilan har ila yau, a sabon sakamakon da tsarin ranking na Webometrics (na watan July 2023), ta samu shiga sahun fitattun jami’o’in ma’aikatar ilimi. A wannan ranking ɗin, jami’ar Guilan ta samu matsayi na 1359 a tsakanin cibiyoyin koyarwa 31000 na duniya, da kuma matsayi na 17 a tsakanin cibiyoyin koyarwa 443 na Iran.

 

Kuɗin Makarantar Jami’ar Guilan

Educational titleBacholarMastersPhD
Agricultural science€375€485€595
art and architecture€375€485€595
Science€375€485€595
Engineering€375€485€595
Literature and Humanities€330€440€550
Natural resources and marine sciences€375€485€595
Physical Education€375€485€595

Makarantu

  • Faculty of Literature and Humanities
  • School of Basic Sciences
  • East Technical College
  • Faculty of Agricultural Sciences
  • Technical College
  • Faculty of Mechanical Engineering
  • School of Physical Education and Sports Sciences
  • School of Natural Resources
  • School of Architecture and Art
  • School of Mathematical Sciences

Kwasa-Kwasai

  • Textile Engineering
  • Petroleum Engineering
  • Aerospace Engineering
  • Materials Engineering
  • Architectural Engineering
  • Mechanical Engineering
  • Agricultural Engineering
  • Railway Engineering
  • Command and Control Engineering
  • Information Technology (IT) Engineering
  • Computer Engineering
  • Civil Engineering
  • Industrial Engineering
  • Urban Engineering
  • System Engineering
  • Chemical Engineering
  • Marine Engineering
  • Robotics Engineering
  • Polymer Engineering
  • Rail Transport Engineering
  • Electrical Engineering
  • Line Engineering and Railway Structures
  • Technical Inspection Engineering
  • Biomedical Engineering
  • Power Plant Mechanical Engineering
  • Pilot Aviation
  • Flight Care Aviation
  • Aviation – air navigation
  • Financial Management
  • Hotel Management
  • Marine Management and Commerce
  • Management and Maritime Commissioner
  • Librarianship
  • Aviation Telecommunications
  • Traditional Architecture Associate
  • Maritime Associate
  • Physics
  • Civil Engineering Technician
  • Computer Science
  • Aviation Science and Technology
  • Mining Technician
  • Ship Technician
  • Economical Science
  • Hadith Science
  • Political Science
  • Mathematics
  • Psychology
  • Acoounting
  • Law
  • Aircraft Maintenance
  • Irrigation Technology
  • Customs Affairs
  • Statistics
  • Rural Development
  • Aviation Electronics
  • Agricultural Machinery Technology
  • Surgery Room
  • Nursing
  • Environmental Health
  • Health Professional
  • Optometry
  • Artificial Limbs
  • Nursing
  • Dental Nursing
  • Optometry
  • Biotechnology
  • Dental Prostheses Technician
  • Medicine
  • Nuclear Medicine Technology
  • Radiology Technology
  • Livestock Production Technology
  • Fisheries Technology
  • Plant Production Technology
  • Forestry Technology
  • Fisheries Technology
  • Acoounting
  • Pharmacology
  • Dental
  • Veterinary Medicine
  • Psychology
  • Geology
  • Biology
  • Audiologists
  • Laboratory Science
  • Nutritional Science
  • Food Science and Industry
  • Physiotherapy
  • Occupational Therapy
  • Bachelor of Law Science
  • Midwifery
  • Anesthesiology
  • Natural Resources Engineering
  • Communication Studies and Information Technology
  • Social Studies
  • Educational Science
  • Persian Language and Literature
  • Arabic Literature
  • Consultation
  • Development of Preschool Children
  • Archaeology
  • Geography
  • History
  • Theology and Islamic Sciences
  • Fiction

Karatu a Jami'ar Guilan

Jerin kwasa-kwasan art na jami’ar

  • Photography
  • Industrial Design
  • Fabric and Clothing Design
  • Carpet Associate
  • Anthropology Associate
  • Associate of Visual Arts
  • Associate of Traditional Arts
  • Television Director
  • Graphics
  • Sculpture
  • Restoration and Restoration of Historical Buildings
  • Museum Keeper
  • Painting
  • Display
  • Visual Arts
  • Handicrafts
  • Cinema
  • Printing
  • Television and Digital Arts
  • Video Connection
  • Protection and Restoration of Historical Monuments

Cibiyoyin Bincike

Jami’ar Guilan na da wuraren bincike guda biyu yanzu haka masu sunan Caspian Sea Water Basin Research Institute da kuma Gilan Research Institute, da kuma ƙungiyoyin bincike biyu, tare da ƙungiyoyin bincike guda 2, da ginshiƙan kimiyya.

Ababen More Rayuwa

A ƙoƙarinta na ɗaukaka matakin ilimin ɗalibanta da bunƙasa ayyukanta na bincike, Jami’ar Guilan ta yi tanadi na musamman na kayan aiki kamar:

  • Sashen Bincike da Nazari wanda ya fara aiki a shekaar 2016.
  • Silkworm Research Group: A wannan cibiyar ake gudanar da bincike a kan yadda ake tattara tsutsar siliki da kuma kiwonta.
  • The scientific pole of mathematical modeling, optimization and combinatorial calculations: Wannan cibiyar ta fara aiki ne a shekarar 2019 a fannonin optimization, control, numerical linear algebra, da numerical analysis and mechanics.
  • Daga cikin abubuwan more rayuwa da jami’ar ta tanadar wa ɗalibanta akwai sabis na zirga-zirga domin kai-komon ɗalibai, hostel na ɗalibai maza da na mata, ɗakunan karatu, da zauren wasanni.

Hostel

Jami’ar ta yi tanadin kammalallen hostel domin baƙin ɗalibai waɗanda ba cikin garin Rasht suke zaune ba. Hostel ɗin jami’ar na ɗauke da duka abubuwan da ake buƙata, zauren wasanni, ɗakunan karatu, da sauransu. Sunayen wuraren kwana (Hostel) na jami’ar Guilan:

  • Wurin kwana na Mirza Kuchik Khan (na maza)
  • Wurin kwana na Bintul Huda (na mata)
  • Wurin kwana na Shahid Ansari (na mata)
  • Wurin kwana na Shahid Karimi (na mata)
  • Wurin kwana na kwalejin Natural Resources Someh Sarah

Laburaren Jami’ar Guilan

Ɗaliban wannan jami’a a kowane matakin karatu suke, suna da damar rizab ko aron kowane irin littafi suke buƙata online ta portal ɗinsu na laburaren jami’ar. Hakazalika ɗalibai na iya duba shafi 20 zuwa 30 na wallafaffun thesis, ko na na’ura.

Karatu a Jami'ar Guilan

Yanayin Wuri

Jami’ar Guilan na nan a cikin garin Rasht a Bolvare Qazvin. Tana kusa da cibiyoyi kamar hedikwatar jami’ar, swimming pool na Jihad, babban laburaren jami’ar Guilan, da kwalejin Agriculture na Jami’ar Guilan. Tashar bus mafi kusa da jami’ar ita ce tashar bus wadda take cikin jami’ar, hakan ya sauƙaƙe zirga-zirga ga ɗalibai da ma’aikatan da basu da abun hawa na kansu.

Adireshi: Rasht, babbar hanyar Khalij Fars, kilomita 5 a babbar hanyar Tehran, Jami’ar Guilan

Shafin Jami’a: https://guilan.ac.ir

Related Posts
Leave a Reply