تهران، میدان ولیعصر، جنب سفارت عراق، ساختمان مینو
مشهد، میدان شریعتی، نرسیده به احمد آباد ۱، طبقه بالای بانک دی

Karatu a University of Qom

Karatu a University of Qom

Loading

Jami’ar Qom (University of Qom) ɗaya ce daga cikin jami’o’in gwamnati na ƙasar Iran wadda ke a wani muhalli mai girman hekta 140,000 a kudancin garin Qom, a babban titin Al-Ghadir bayan an wuce Shahrake Qods. A cigaban rubutunnan za mu gabatar muku da bayani a kan yanayin karatu a wannan jami’a ta Qom.

Gabatarwa

A shekarar 1985 ne bisa amincewar majalisar ƙoli ta Al’adu, ƙari bisa ga ɗaliban hauza ilmiyya, an karɓi ɗaliban da suka kammala karatun sakandare kafin juyin musulunci, ta hanyar jarabawar shiga ta ‘konkur’. An ci gaba da ayyukan koyarwa na wannan jami’ar ne a shekarar 1988 bayan samun izini, cibiyar horar da malamai ta jami’ar Qom ta fara aiki da nufin tarbiyyantar da ƙwararrun malamai waɗanda za su ci gaba da aikin koyar da ilimin addinin musulunci a jami’o’i.

A ranar 21 ga watan June na shekarar 1997 tare da amincewar majalisar faɗaɗa makarantun gaba da sakandare, da makarantar horar da ɗalibai ta manyan makarantu da shari’a ta canza suna zuwa “Qom University” wato Jami’ar Qom. Ta fara da kwas 6 a matakin digiri, kwas 5 a masters, da kuma kwas 1 a matakin PhD. Daga ƙarshe aka fitar da sabuwar doka ta jami’ar Qom a wani taro da aka yi ranar 15/01/2000 na majalisar faɗaɗa makarantun gaba da sakandare. Daga nan kuma jami’ar ta Qom ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimi.

A halin yanzu akwai ɗalibai 8000 da malamai 245 a wannan jami’ar. Bincikenmu ya gwada cewa an wallafa maƙalar ilimi guda 8132 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida zuwa yanzu. Jami’ar Qom ta wallafa mujalla 12 na musamman sannan zuwa yanzu ta shirya taruka 6. Har ila yau, jami’ar ta yi nasarar wallafa maƙala 326 a matakin ƙasa da ƙasa. A shekarar 2023 manazarta da masu bincike na wannan jami’a sun wallafa mafi yawan maƙalolinsu da kamlomin ‘International Rights’ da ‘Human Rights’ a matsayin muhimman kalmomi.

Karatu a University of Qom

Martabar Jami’a

Wannan shekara a karon farko jami’ar Qom ta samu shiga tsarin ranking na Times wanda wannan babban cigaba ne ga jami’ar ta fuskar ilimi. Shi dai wannan tsarin ranking na Times ya fara aiki ne a shekarar 2004 inda ya ci gaba da martaba jami’o’i da cibiyoyin ilimi a kowace shekara.

Tsarin na Times ya yi la’akari da ma’aunai biyar kamar haka; ingancin koyarwa maki 30, citations maki 30, ayyukan bincike maki 30, kima a idon duniya maki 7.5, sai kuma alaƙa da masana’antu maki 2.5. Da wannan ne jami’ar ta Qom ta samu matsayi na 1200 – 1500 a tsakanin jami’o’i da cibiyoyin koyarwa na duniya a shekarar farko na shigarta wannan tsari na Times.

Kuɗin Makarantar jami’ar Qom

DegreesDurationAnnual Tuition

Makarantu da departments na koyarwa

Faculty of Engineering

 • Department of Computer Engineering and Information Technology
 • Department of Civil Engineering
 • Department of Industrial Engineering
 • Department of Mechanical Engineering
 • Department of Architectural Engineering
 • Department of Electrical Engineering
 • Department of Chemical Engineering

Faculty of Basic Sciences

 • Department of Physics
 • Department of Mathematics
 • Department of Chemistry
 • Department of Statistics
 • Department of Biology
 • Department of Computer Science

School of Management and Economics

 • Department of Business Administration
 • Department of Industrial Management
 • Department of Accounting
 • Department of Economic Sciences

Faculty of Literature and Human Sciences

 • Department of Persian Language and Literature
 • Department of English Language and Literature
 • Department of Arabic Language and Literature
 • Department of Educational Sciences
 • Department of Physical Education
 • Department of Information Science and Epistemology

School of Law

 • Department of Public and International Law
 • Department of Private Law
 • Department of Intellectual Property Rights
 • Department of Law, Penal Law and Criminology

Faculty of Theology and Islamic Studies

 • Department of Quran and Hadith Sciences
 • Department of Jurisprudence and Fundamentals of Law
 • Department of Moral Philosophy
 • Department of Islamic Philosophy and Theology
 • Department of Islamic Studies
 • Department of Shia Studies

Karatu a Jami'ar Qom

Cibiyoyin kimiyya da bincike

 • Growth Center
 • Environmental Green Research Institute
 • Institute of Management and Islamic Law
 • Research Institute of Religion and Politics
 • Research Department of Water Resources Management
 • Research Department of Light Structures
 • Women’s Research Department

Ababen More Rayuwa

 • Hostel na maza masu ɗaukar mutum 400 a jimlace
 • Hostel na mata masau ɗaukar sama da mutum 900
 • Babban Laburaren jami’a mai ɗauke da sama da sunan littafi 49908 a harshen farsi, guda 5769 a harshen latin, da maƙaloli 408 a harshen larabci, farsi, da turanci. Daga ciki akwai take 10720 na littafan farsi da larabci, guda 1500 kuma na latin.
 • Laburaren faculty of basic sciences na ɗauke da sunan littafi sama da 11000 a farsi da latin, da kuma soft copy na maƙalolin latin guda 3500.
 • Laburaren cibiyar Tarbiat Modares na ɗauke da taken littafai 10500.
 • Cibiyar sadarwa ta Intanet
 • Rufaffen zauren wasanni
 • filin wasan ƙwallon ƙafa da volleyball
 • Filin wasa mai haki
 • Restaurant
 • Masallaci
 • Swimming pool, sonar da jacuzzi
 • Babban ɗakin taro na Shaikh Mufid
 • Zauren taro na Shahid Beheshti
 • Zauren taro na Shahid Motahhari
 • Zauren taro na Andishe (saboda taruka na musamman da display)

Laburaren Jami’ar Qom

An buɗe laburaren jami’ar Qom ne a shekarar 1980, wato shekara ɗaya bayan assasa jami’ar. A tsarin intanet na ɗakin karatun jami’ar, ɗalibai za su iya karanta litattafai na musamman, labarai da ingantattun wallafe-wallafen cikin gida da na waje. Har ila yau, an kasa laburaren zuwa rassa daban-daban kamar; laburaren Faculty of Theology and Islamic Studies, laburaren School of Law, laburaren makafi na Sepideh, da laburaren ɗalibai mata na Kowsar.

Wurin kwanan jami’ar Qom

Wurin kwana yana ɗaya daga cikin abubuwa masu muhimmanci ga akasarin baƙin ɗaliban da suka samu karɓuwa a kowane irin matakin karatu. Wannan jami’a ita ce uwar jami’o’in da ke lardin Qom, saboda haka ta yi tanadin wurin kwana mai kyau ga baƙin ɗalibai waɗanda suka zo daga garuruwa masu nisa, suka samu karɓuwa a jami’ar. ɗalibai maza da mata, hatta masu iyali suna iya duba shafin intanet na hostel ɗin jami’ar domin sanin kuɗin da ake biya don kama hostel. Akwai sabbin hostel guda uku da aka assasa kwanannan, su ma za ku iya bincika kuɗinsu a shafin yanar gizo na jami’ar.

Karatu a Jami'ar Qom

Yanayin Wuri

Jami’ar Qom na nan a Meidane Mofid Daneshga, titin Mofid, Meidane Mirzaei Qommi. Jami’ar na kusa da wurare kamar Bankin Mellat, Shahid Mahalati Faculty of Political Ideology, Atka store, Faculty of Training of Ideological and Political Instructors of the IRGC, da kuma gidan abinci na Mortezavi.

Adireshi: Qom, Meidane Mofid Daneshga, Bolvare Mofid, Meidane Mirzae Qommi

Shafin Jami’a: https://qom.ac.ir

Related Posts
Leave a Reply