تهران، میدان ولیعصر، جنب سفارت عراق، ساختمان مینو
مشهد، میدان شریعتی، نرسیده به احمد آباد ۱، طبقه بالای بانک دی

Karatu a Urmia University

Karatu a Urmia University

Loading

Jami’ar Urmia ɗaya ce daga cikin jami’o’in gwamnati masu inganci waɗanda ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimi, a lardin Azarbaijan Gharbi, a yammacin garin Urmia wadda aka assasa a shekarar 1965. Garin Urmia na nan a yammacin tafkin Urmia a ƙasan dutsen Sir. Akwai yanayi biyu na zafi da sanyi a wannan gari. Ku kasance tare da mu domin samun bayanai a kan yanayin kratu a wannan jami’a ta Urmia.

Gabatarwa

Jami’ar Urmia (a harshen turanci Urmia University)Tana da makarantu 11, cibiyar koyarwa 1, wuraren bincike 6, cibiyar karatu da bincike 1, cibiyar koyon yare, cibiyar karatun online, gidan tarihi, da sauransu. Jami’ar na da girman hekta 505, ita ce jami’a mafi daɗewa kuma mafi girma a yammacin ƙasar Iran, kuma ɗaya ce daga cikin fitattun jami’o’in ƙasar a ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimi.

Jami’ar Urmia ɗaya ce daga cikin jami’o’in Iran mafi inganci a fannonin Engineering, Human Sciences, da Basic Sciences. A halin yanzu akwai ɗalibai 14515 da malamai 485 a wannan jami’ar. Bincike ya nuna cewa zuwa yanzu jami’ar Urmia ta wallafa maƙala 18260 na ilimi a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida, da maƙala 8905 a matakin ƙasa da ƙasa, ta wallafa mujalla 6. Jami’ar ta yi nasarar shirya taruka 11 zuwa yanzu. A shekarar 2023,masu bincike na wannan jami’ar sun wallafa mafi yawan maƙalolinsu da kalmomin “physical activity” da “students” a matsayin muhimman kamlomin maƙala.

Martabar Jami’a

A ranking na jami’o’in Iran bisa la’akari da ayyukansu na kimiyya, jami’ar Urmia ta shiga sahun zaɓaɓɓun jami’o’i 7 na Iran (research-oriented), a sakamakon ranking ɗin jami’o’in gwamnati na ma’aikatar ilimi kuma, jami’ar ta samu shiga rukunin A”. A kowace shekara, ma’aikatar ilimi ta ƙasar Iran tana kasa jami’o’in ƙasar zuwa rukuni huɗu (na A, B, C, D), wannan jami’ar ta samu shiga rukunin farko na jami’o’in ƙasar (rukunin “A”) saboda cigaban da ta samu a ‘yan shekarun bayannan.

A tsarin ranking na Shanghai kuma, jami’ar Urmia ta samu matsayi na 301 – 400 a fannin “Mechanical Engineering“, a fannin “Food Science and Industry” kuma, ta samu matsayi na 201 – 300 a tsakanin jami’o’in duniya.

A tsarin ranking na Scimago kuma (Scimago Institutions Rankings), a shekarar 2022 jami’ar ta samu cigaba da mataki 77, inda ta ɗaga daga matsayi na 755 zuwa matsayi na 678 a duniya, ta kuma samu matsayi na 9 a jami’o’in Iran.

A tsarin ranking na TIMES kuma, jami’ar Urmia ta zo a matsayi na 1000 – 1200 a jami’o’in duniya. Sai kuma tsarin ranking na CWTS (Leiden), jami’ar ta samu matsayi na 800 a duniya a mahangar ilimi.

Kuɗin makarantar Jami’ar Urmia

DegreesHumanities-mathematical sciencesScienceAgriculture-technical and engineering
Bacholar 500$550$550$
Masters 600$650$700$
PhD700$800$900$

Makarantu

Faculty of Veterinary Medicine

An buɗe wannan kwalejin ne a shekarar 1975. Kwalejin Veterinary Medicine ta jami’ar Urmia, ita ce kwaleji ta uku mafi daɗewa a wannan fanni na Veterinary Medicine a ƙasar Iran bakiɗaya, inda ta biyo bayan makarantun jami’ar Tehran da Jami’ar Shiraz. A wannan kwalejin akwai sassan koyarwa kamar haka:

  • Basic Sciences
  • Pathobiology
  • Food Hygiene and Quality Control
  • Surgery and Diagnostic Imaging
  • Internal Diseases and Clinical Pathology
  • Midwifery and Poultry
  • Microbiology

Daga cikin ɗaliban da wannan kwalejin ta yaye masu ƙwazo kuma fitattu akwai Prof. Muhammad Bagher Ibrahimi.

School of Literature and Human Sciences

An assasa wannan kwalejin a shekarar 1988 da nufin horar da ƙwararrun ma’aikata, inda aka fara da department ɗin Persian Language and Literature. Ita ce kwaleji ta 4 a jami’ar.

An fara karɓar ɗalibai ne a kwas ɗin Persian Literature a shekarar 1988, da kwas ɗin Physical Education a shekarar 1989, duk a matakin digiri. Akwai sassan koyarwa a wannan kwalejin kamar haka:

  • Educational Science
  • History
  • Geography
  • Islamic Jurisprudence
  • Islamic Studies
  • Persian Language and Literature
  • English Literature
  • English Language Translation
  • Law
  • Sociology
  • Jurisprudence and Principles of Islamic Law
  • Sport Sciences
  • Psychology
  • Istanbul Turkish Language and Literature

Faculty of Science

An assasa wannan kwalejin a shekarar 1979 inda ta fara aikinta da karɓar ɗalibai a fannin Plant Science da Physics kafin ta ƙara yawan kwasa-kwasai daga baya. A wannan kwalejin akwai sassan koyarwa kamar haka:

  • Mathematics
  • Physics
  • Biology
  • Geology
  • Nanotechnology

Faculty of Petrochemical Engineering

An assasa wannan kwalejin tare da goyon bayan hukumar jami’ar, biyo bayan assasa cibiyoyi daban-daban na petrochemical engineering a lardin na Azarbaijan Gharbi. Kwalejin na da departments ɗin Chemical Engineering, Polymer Engineering, Energy Engineering, da Petroleum Engineering, sannan ana kan ƙoƙarin bunƙasa ta.

Duka fannonin da muka ambata na wannan kwalejin an assasa su ne da ƙoƙarin Dr. Jamshid Bagherzadeh, ɗaya daga cikin malaman department ɗin Computer Engineering.

Faculty of Technology and Engineering

An assasa wannan kwaleji a shekarar 1990, bisa ƙoƙarin malaman fasaha na jami’ar irinsu Dr. Mehdi Sabet. Muhallin farko na wannan kwaleji ya kasance kilomita 1.5 a hanyar Saro kafin a maida ta muhallin da take a yanzu, a shekarar 2001. Yanzu haka wannan kwalejin yana da sassa kamar haka:

  • Civil Engineering
  • Mechanical Engineering
  • Mining Engineering
  • Industrial Engineering
  • Materials Engineering
  • Chemical Engineering
  • Polymer Engineering

Faculty of Electrical and Computer Engineering

Wannan kwalejin yanzu haka yana karɓar ɗalibai a kwas ɗin Electrical Engineering a fannonin Electronics, Power, da Telecommunications, sai kuma fannin Software a kwas ɗin Computer Engineering, a matakin digiri kenan.

A matakin masters da PhD kuma, a ƙarƙashin Electrical Engineering akwai fannonin Integrated circuits, Micromachine, Telecommunication field and System, Power Systems, da Power Electronics. A ɓangaren Computer Engineering kuma akwai Computer Networks. Kwalejin na aiki tuƙuru domin horar da ƙwararrun ma’aikata da masu bincike a fannonin da muka ambata.

  • Electrical and Electronic Engineering ( Bachelor’s, Master’s and Doctorate)
  • Engineering of Micro and Nano Electromechanical Systems (Master’s and Doctorate)
  • Power Electrical Engineering (bachelor’s, master’s, and doctorate)
  • Telecommunication Electrical Engineering (bachelor’s, master’s, and doctorate)
  • Computer Engineering – Software (BSc and Master’s)
  • Computer Engineering – Computer Networks (master’s degree and doctorate)

Faculty of Agriculture

Tana daga cikin makarantu mafi daɗewa na wannan jami’a. A cikinta akwai sassan koyarwa kamar haka:

  • Water Engineering
  • Plant Cultivation and Breeding
  • Animal Science
  • Biosystem Mechanics
  • Plant Medicine
  • Food Science and Industry
  • Soil Science
  • Gardening
  • Agricultural Economics
  • Breeding and Biotechnology

Faculty of Sports Sciences

An assasata a shekarar 2010. Daga cikin sassan koyarwa masu muhimmanci na wannan kwaleji akwai Physiology, Sports, da Corrective Exercises. Daga cikin kwasa-kwasanta akwai:

  • Pathology and Corrective Movements: Master’s Degree
  • Movement Behavior: Master’s and Doctorate
  • Sport Physiology: Clinical Physiology a matakin Matres’s, sai Cardiovascular da respiration a matakin PhD
  • Sport Managment: Master’s and Doctorate

Faculty of Arts

  • Architecture
  • Urban Engineering
  • Painting
  • Restoration and Restoration of Historical Buildings

Faculty of Natural Resources

  • Pasture and Watershed
  • Forestry
  • Fisheries

Faculty of Economics and Management

An assasa wannan kwalejin a shekarar 2006 domin ƙarfafa bunƙasar tattalin arziki na lardin Azarbaijan Gharbi, bisa amincewar hukumar makarantar (jami’a). Department ɗin Economics shi ne department ɗin asali na wannan kwalejin wanda ya fara aiki a shekarar 1991 bisa ƙoƙarin Dr. Masoud Mansori, da karɓar ɗalibai 40 a matakin digiri. Yanzu haka wannan kwaleji yana karɓar ɗalibai a kwasa-kwasai kamar haka:

  • Economic Sciences (bachelor’s, master’s and doctorate)
  • Accounting (bachelor’s and master’s)
  • Management (bachelor’s and master’s)

Faculty of Chemistry

Da fari department ne na chemistry wanda aka buɗa a shekarar 1976 inda ya fara aikin koyarda darasin chemistry da malamai membobin tsangayar ilimi guda 2. A watan October na shekarar 1995 bisa amincewar ma’aikatar ilimi, aka fara yin kwas ɗin pure chemistry a matakin digiri, daga 1997 kuma aka fara yin Organic Chemistry a matakin Masters tare da kwasa-kwasai irinsu Analytic Chemistry, Physical Chemistry, Mineral Chemistry, da Applied Chemistry, yanzu haka an yaye ɗalibai a fannoni biyar a wannan department. A shekarar 2017 ne aka mayar da wannan department na chemistry kwaleji.

  • Analytical Chemistry
  • Organic Chemistry
  • Mineral Chemistry
  • Physical Chemistry

Cibiyar Koyarwa ta Shahid Bakri Miandoab

Wannan cibiyar tana ƙarƙashin jami’ar Urmia ne kuma ita kaɗai ce babbar cibiyar koyarwa wadda ke ƙarƙashin ma’aikatar ilimi kaitsaye a kudancin lardin Azarbaijan Gharbi. Cibiyar na ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin koyarwa na gaba da sakandare na Iran waɗanda ba su da tsara, ta fuskacin yanayin muhalli mai kyau, tana da girman kimanin hekta 80,000 ɗauke da gine-gine masu girman murabba’in mita 18,000 na azuzuwan karatu, ofisoshi, cibiyoyin bincike, da sauransu. Cibiyar za ta iya ɗauke sama da ɗalibai 2500.

Wuraren bincike

  • Urmia Lake Studies Research Institute
  • Artemia and Aquaculture Research Institute
  • Microelectronics Research Institute
  • Biotechnology Research Institute
  • Nanotechnology Research Institute
  • Research Institute of Social Studies

Ababen More Rayuwa

A mahangar ɗaliban da suka kammala karatunsu a wannan jami’a ta Urmia da kuma waɗanda suke karatu cikinta yanzu, daga cikin kayan aiki da abubuwan more rayuwa na wannan jami’ar akwai masauki, ɗakin karatu na ɗalibai maza da na mata, abubuwan walwala, da sauransu. Ga jerin kayan wasanni na jami’ar Urmia.

  • Swimming pool
  • Filin wasan ƙwallon ƙafa na haki
  • Zauren gina jiki (gym)
  • Filin wasa na rairayi
  • Zauren wasan table tennis
  • da sauransu…

Laburaren Jami’a

Jami’ar na da laburare wanda tayi tanadi domin amfanin ɗalibai a kowane matakin karatu wanda za su iya yin rizab na littafin da suke buƙata ta online domin su karɓi aro.

Laburaren na da zauren karatu biyu (na maza da na mata) inda ɗalibai za su iya keɓewa don karanta littafai.

Hostel

Jami’ar Urmia na da hostel guda 13 na kanta, hostel mai zaman kansa da kuma masaukin haya. Bisa dokokin hostel na jami’o’i, ɗaliban digiri na iya amfani da hostel tsawon shekara 4 na karatunsu, ɗaliban masters shekara 2, ɗaliban PhD shekara 6, non-scholarship masters shekara 4, masu yin masters da PhD a haɗe kuma shekara 6.

Yanayin Wuri

Jami’ar Urmia na nan a garin Urmia, titin Keshavarzi. A kusa da jami’ar akwai wurare kamar Faculty of Agriculture ta jami’ar Urmia, Faculty of Basic Sciences, Pardis Nazloo, da kuma West Azarbaijan Science and Technology Park.

Adireshi: Lardin Azarbaijan Gharbi – Urmia – Kilomita 11 a babbar hanyar Saro – Urmia University

Shafin jami’a: https://www.urmia.ac.ir

Related Posts
Leave a Reply

Your email address will not be published.Required fields are marked *