Jami’ar Kharazmi wadda ke amsa sunan Jami’ar Tarbiat Moallem a baya, ɗaya ce daga cikin jami’o’in gwamnati da ke ƙarƙashin ma’aikatar ilimi, wadda aka sawa sunan Muhammad Bn Musa Kharazmi wani masanin kimiyya ɗan ƙasar Iran wanda aka yi a ƙarni na uku. Jami’ar na nan a garin Tehran da garin Karaj. Ku kasance tare da mu domin samun bayanai game da yanayin karatu a jami’ar ta Kharazmi.
Gabatarwa
An assasa jami’ar ne a shekarar 1919, tsawon wannan lokaci an sauya mata suka lokuta daban-daban, sannan an ƙaƙƙara girman campus ɗinta. A halin yanzu jami’ar na karɓar ɗalibai a mabambantan kwasa-kwasai na Basic Sciences, Human Science, Educational Sciences, da Engineering, a matakai daban-daban na karatu. Jami’ar ta Kharazmi ita ce cibiyar koyarwa ta gaba da sakandare ta farko a ƙasar Iran, tana da tarihin fiye da ƙarni ɗaya. Hakazalika ita ce jami’a ta farko ta horar da malamai a Iran, dukda cewa yanzu al’amuran da suka shafi horar da malamai sun koma hannun jami’ar Farhangiyan.
An sauya sunan jami’ar a shekarar 1912 daga “Darul Moalimin” zuwa “Daneshsarae Aali“, a shekarar 1974 kuma aka maida ita “Tarbiat Moallem“. An samu amincewar majalisar bunƙasa karatun gaba da sakandare da ma’aikatar ilimi a kan canjawa jami’ar suna zuwa Jami’ar Kharazmi a shekarar 2002 da 2003, amma saboda jinkirin da aka samu na amincewar majalisar juyin al’adu, ba’a canja sunan ba sai farko-farkon shekarar 2012.
A halin yanzu akwai ɗalibai 14542 da malamai 480 a wannan jami’a. Bayanai sun nuna cewa jami’ar Kharazmi ta wallafa maƙalar kimiyya guda 17994 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida zuwa yanzu. Jami’ar ta mallaki lambar yabo, sannan ta wallafa mujalla 22, kuma ta wallafa maƙala 6438 a matakin ƙasa da ƙasa. Zuwa yanzu an gudanar da taruka 25 a jami’ar Kharazmi.
Kuɗin makarantar jami’ar Kharazmi
Faculty | B.A./BSc. | M.A/MSc. | Ph.D. |
---|---|---|---|
Literature andHumanities,Law andPoliticalSciences,PsychologyandEducationalSciences,PhysicalEducationand SportsSciences, andGeography,Management,Economics,FinancialSciences | € 1200 per year | € 1500 per year | € 2300 per year |
Biology,Chemistry,Physics, Earthsciences,Mathematicaland Computersciences,Engineering,Art andarchitecture | € 1400 per year | € 2000 per year | € 3000 per year |
Persian Placement Test (EPT) | €15 | ||
Beginner | €90 | ||
Pre-Intermediate | €90 | ||
Intermediate | €90 | ||
Upper Intermediate | €90 | ||
Advanced | €90 | ||
Test and certificate cost | €45 |
Fees | Afghanistan, Syria, Yemen (Iranian Rials) | Other Countries (Euro) |
---|---|---|
Application fee process | ||
Pre-Admission | ||
Final Registration | ||
Airport Transfer(Based on request) | ||
Hostel fee(Based on request) | ||
Food (2 Meals/day) | ||
Insurance and Sport Activity(Based on request) | ||
Family Insurance and Sport Activity(Based on request) |
Martabar Jami’a
A sakamakon da tsarin ranking na TIMES ya fitar na shekarar 2023, Jami’ar Kharazmi ta samu matsayi na 601 – 800 a fannin Social Sciences a tsakanin jami’o’in duniya, inda ta samu matsayi na 4 zuwa na 6 a tsakanin jami’o’i da cibiyoyin koyarwa na ƙasar Iran. A fannin Engineering da fasaha kuma (fannonin chemical engineering, civil eng, electrical eng, da mechanical eng), jami’ar Kharazmi ta samu matsayi na 801- 1000, a fannin Basic Sciences kuma (physics, chemistry, mathematics, statistics, geology) ta samu matsayi na 1001+ a tsakanin jami’o’in duniya.
A jimilla, jami’ar ta samu matsayi na 1201 – 1500 tsakanin sauran jami’o’in duniya. An yi la’akari da ma’aunai 5 ne a wurin martaba jami’o’in kamar haka; ayyukan bincike (maki 14.1), koyarwa (maki 31.3), kima (maki 24.6), kuɗin shiga (maki 19.4).
Makarantu
- Faculty of Geographical Sciences
- Faculty of Engineering and Technology
- School of Basic Sciences
- Faculty of Mathematical and Computer Sciences
- Faculty of Psychology and Educational Sciences
- Faculty of Literature and Humanities
- Faculty of Law and Political Science
- School of Physical Education and Sports Sciences
- School of Chemistry
- Faculty of Biological Sciences
- Faculty of Physical Sciences
- Faculty of Earth Sciences
- Faculty of Management and Accounting
- Faculty of Financial Sciences
- Faculty of Economics
- Faculty of Management
Hrabobi
Tehran Campus
Wannan harabar tana tsakiyar garin Tehran, a titin Shahid Mofateh Junobi (tashar metro ta davazdah daulat, layi na 4, da layi na 1 na tashar taleghani). Girmanta hekta 2, kuma an yi ginin ne da tsarin Markov Engineering na ƙasar Russia.
Harabar Karaj
Wannan harabar tana da girman hekta 270 wadda aka fara aikin gina ta a unguwar Hesarak a shekarar 1977 (a garin Karaj). Wannan reshen na jami’ar yana da tsarin gidajen malamai da ma’aikata, block 23 na hostel ɗin ɗalibai, swimming pool, admin block, da makarantu. A watan February na shekarar 2009 ne aka fara ayyukan gina babban laburaren jami’ar da kuma ɗakin taro. A duka harabobin biyu (na Tehran da Karaj) ana gudanar da ayyukan koyarwa da na bincike.
Kwasa-Kwasai
- Geographical Sciences
- History
- Private Law
- Management
- Philosophy of Education
- Curriculum
- Education Management
- Educational Psychology
- Consultation and Guidance
- Geology
- Chemistry
- Biology – plant sciences
- Biology – animal sciences
- Mathematics
- Physics
- Persian Language and Literature
- Arabic Literature
- Teaching English
- Physical Education and Sports Science
Cibiyoyin Bincike
- Information and Communication Technology Center
- Center for Entrepreneurship and Communication with Society
- Center for the Growth and Development of Technology Units
- APA Center
- Water Research Center
- Oil Research Center
- Laboratory Animal Breeding Center
- Skills Training and Career Counseling Management Center
- Plasma Research Institute
- Kinetic Sciences Research Institute
- Research Institute of Applied Sciences
- Convergent Sciences Research Institute
- Institute of Natural Disasters and Risk Management
- Research Institute of Philosophy and Comparative Law
- Green Chemistry Research Institute
- Ƙungiyoyin Bincike na Jami’ar Kharazmi
- Bahar Persian Language and Literature Research Institute
- Mathematical research institute of Dr. Mosaheb
- Educational, Psychological and Social Research Institute
Ababen More Rayuwa
- Zauren wasanni
- Rufaffen Swimming Pool
- Wurin cin abinci
Wuraren kwanan jami’ar
Duka rassa biyun jami’ar suna da hostel na ɗalibai na maza da na mata. A reshen Tehran, akwai wuraren kwana kamar haka; Laleraz, Sahand, Shamsabad, Baharestan, Motahhari, Tauhid, Rudsar, Shahid Hosaini, da Samiyeh. A Karaj kuma akwai block 23 mabambanta na hostel ɗin ɗaliɓai, (kowane block na da girman murabba’in mita 4000 kuma yana ɗaukar mutum 300).
Laburaren Jami’a
Laburarukan jami’ar Kharazmi sun kasu kamar haka: A duka harabobin jami’ar (Tehran da Karaj) akwai babban laburare da cibiyoyin taskace bayanai domin sauƙaƙe ayyukan karatu, bincike, thesis, maƙaloli, litattafan karatu, da sauransu ga ɗalibai.
Baya ga haka, a duka kwalejojin jami’ar akwai laburare wanda ya keɓanci wannan kwalejin da buƙatunta domin sauƙaƙawa ɗalibai wahalan neman abunda suke buƙata da littafi ko resources. Babban laburaren Karaj kaɗai yana da kwafin littafai 210820 a harshen farsi, larabci, da latin, tare da rubutun hannu kwafi 113, a wani gini mai hawa 6.
Yanayin Wuri
Jami’ar Kharazmi na nan a unguwar Hesarak ta garin Tehran, a titin Shahid Beheshti. Akwai muhimman wurare a kusa da jami’ar kamar irinsu; cibiyar rigakafin jami’ar Kharazmi, gidanmai na Sadat, da wurin gyaran mota na Hami da Amiran reshen Hesarak, da kuma CNG Hesarak. Tashar bus mafi kusa da jami’ar ita ce tashar Parking Garbi, hakan ya sauƙaƙe zirga-zirga ga ɗalibai da ma’aikata marasa abun hawa.
Adireshi
Tehran: Titin Shahid Mofateh, kafin a ƙarasa Inqilab, block 43
Karaj: Ƙarshen titin Shahid Beheshti – Meidane Daneshga
Shafin jami’a: https://khu.ac.ir