[gtranslate]
مشهد، میدان شریعتی، نرسیده به احمد آباد ۱، طبقه بالای بانک دی

Karatu a Shiraz

Karatu a Shiraz

Loading

Manufarmu a wannan rubutu ita ce tattauna batutuwa da suka shafi karatu a Shiraz domin sauƙaƙe muku bincike. Mun yi ƙoƙarin nazari a kan garin Shiraz ta janibobi daban- daban da kuma tasirin hakan a kan karatun ɗalibai. Ku kasance tare da mu.

Karatu a ShirazShiraz

Shiraz ɗaya ne daga cikin manyan biranen ƙasar Iran kuma shi ne cibiyar lardin Fars. Yawan mutanen da ke Shiraz ya kai kusan miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas. Hakan ya sa garin Shiraz ya zama gari na biyar mafi yawan mutane a Iran.

Bayanai a kan Shiraz

Zirga-Zirga

Dalilin kasancewarsa a tsakiyar ƙasar Iran, birnin Shiraz na da hanyoyin sadarwa na zirga-zirga masu yawa fiye da sauran garuruwa. Filin jirgin ƙasa da ƙasa na Shahid Dastgheib shi ne na biyu a Iran (bayan filin jirgin Imam Khomeini da ke birnin Tehran) a inganci da yawan kayan aiki. Hakazalika tashar jirgin ƙasa ta Shiraz wadda aka assasa a shekarar 2011 tana ɗaya daga cikin tashoshin jirgin ƙasa mafi inganci na Iran. Kamar dai sauran garuruwa, Shiraz na da hanyoyin autobus na cikin gari da tashohin mota na fasinja. Har ila yau akwai layi ɗaya na jirgin ƙasan metro da ke aiki a Shiraz yanzu haka.

Abubuwan buɗe ido

Kasancewar Shiraz ɗaya daga cikin muhimman wuraren yawon buɗe ido a Iran, cike yake da wurare da abubuwan tarihi waɗanda ake tururuwar zuwa gani daga ciki da wajen ƙasar. Daga cikin abubuwan tarihi da ke Shiraz akwai Atishkade Samikan, Makwancin Hafiz, Makwancin Khwaju Kermani, Makwancin Sa’adi, Arg Karim Khan, lambun Jahan Nama, lambun Eram, lambun Takht, lambun Cheheltan, lambun Delgosha, lambun Afif Abad, lambun Narenjistan Qavam, lambun Haft Tan, gidan Salihi, rijiyar Morteza Ali, masallacin Nasir Almalik, fadar Abu Nasr, makarantar Agha Baba Khan, gidan tarihi na Haft Tanan, taswirar Bahram, da sauransu.

Daga cikin abubuwan kallo ɗabi’a na birnin Shiraz akwai Kuhmareh Waterfall, Barm-e Delak, Qal’e Bandar Park, Melli Park, lambun Parandegan, Pirbanab, maɓuɓɓugar Joshak, maɓuɓɓugar Kharegan, maɓuɓɓugar Reychi, tafkin Dasht Arjan, tafkin Maharlo, Rokn Abad, kogin Qara Aghaj, ƙauyen Qalat, dutsen Sabzeposhan, Gardeshgah Ateshkade, da sauransu.

Akwai abubuwan addini da wuraren ibada da dama kamar ƙaburbura daban-daban na Imamzadeh da ke cikin garin Shiraz waɗanda suka zama sanadiyyar bunƙasar tsarin zamantakewa da tattalin arziki na garin. An ce a lokacin sarki Ma’amun na Abbasawa, da yawa cikin ƴaƴaye da jikokin Imam Musa Al-Kazim Imami na bakwai a jerin imaman shi’a, a garin Shiraz suka yi mafaka. An rawaito cewa dukansu ko dai mutuwa ta ɗabi’a ta riske su ko kuma hakimin Abbasawa ne ya kashe su. An iya gane ƙaburburansu bayan shekaru inda aka ci gaba da ziyararsu. Haramin Shah Charag na garin Shiraz shi ma ɗaya ne daga cikin wuraren ibada a garin Shiraz.

Garin na da manyan koren wurare saboda yanayi mai kyau da yake da shi. A arewa maso yammacin garin Shiraz akwai wani a cikin duwatsu mai suna Derak wanda ɗaya ne daga cikin manyan wuraren shaƙatawa na Iran. Akwai wurin shaƙatawa na Azadi, lambun Jahan Nama, da wurin shaƙatawa na Lona duk a cikin wuraren shaƙatawa na ɗabi’a a Shiraz.

Wani abun jan hankali kuma shi ne samuwar cibiyar baje kolin ƙasa da ƙasa a garin Shiraz wadda ita ce cibiyar baje koji mafi girma a kudancin ƙasar Iran. Wannan cibiyar na da girman kimanin murabba’in kilomita 1.7 da rufaffin zauruka guda 6 da kuma wasu uku da ake kan ginawa tare da filin baje koli mai girman murabba’in mita 3,000.

Jami'ar Shiraz

Sadarwa ta ƙasa da ƙasa

Ofisoshin jakadancin da ke aiki yanzu haka a garin Shiraz:

India India

Iraq Iraq

Karatu a Shiraz

Idan ana magana a kan manyan jami’o’in ƙasar Iran mafi kyau dole ne a ambaci jami’ar Shiraz. Jami’ar Shiraz ta ƙunshi makarantu daban-daban irin makarantar Engineering, makarantar Science, makarantar Agriculture, Veterinary Medicine, Literature and Human Science, Law and Political Science, Educational Science and Psychology, da sauransu.

Jami’ar Shiraz University of Medical Sciences na da tsufan shekaru kusan 70. Shiraz University of Technology, Faculty of Telecommunication Industries of Iran, Faculty of Electronics Industry, Shahid Bahonar Technical Faculty, Hafez Shiraz Higher Education Center, da Pasargad Shiraz Higher Educational Center wasu ne daga cikin jami’o’in garin na Shiraz. Mun tattara muku bayanan musamman game da jami’ar likitanci Shiraz, Jami’ar fasaha ta Shiraz, da kuma jami’ar Shiraz. Za ku iya samun ƙarin bayani a waɗannan maƙaloli: Karatu a Shiraz University of Medical Sciences, Karatu a Shiraz University, da Karatu a Shiraz University of Technology.

Abubuwan burgewa a Shiraz

Dalilin karatu a Shiraz

  • Garin Shiraz na iya dacewa da ku a babin karatu dalili kuwa shi ne kuɗin karatu na da sauƙi a Shiraz idan an kwatanta da sauran garuruwan Iran. To amma za ku iya samun matsala da kuɗin haya. Saboda haka abunda ya fi sauƙi shi ne ku yi amfani da hostel ɗin ɗalibai a lokacin karatunku.
  • Jami’ar Shiraz na cikin jami’o’in Iran waɗanda ake karɓar shaidar kammalawarsu a sauran ƙasashen duniya.
  • Jami’ar Shiraz ta yi tanadin kayan aiki irin su laburare, ɗakunan gwaje-gwaje, gym, da sauran wurare da abubuwan buƙatar ɗalibai.
  • Birnin Shiraz cike yake da gine-ginen al’adu da tarihi waɗanda suka daɗe sosan gaske. Samuwar waɗannan abubuwan jan hankali na al’adu da na tarihi na iya zama abin sha’awa da tunani, da kuma bincike ga ɗaliban da ke karatu a fannonin sanin al’adu da fasaha na Mashhad.
Related Posts
Leave a Reply