[gtranslate]
Search
Unit 3, No. 15, the beginning of Ahmad Abad Street, Mashhad, Iran

Karatu a Qom

Karatu a Qom

Loading

Manufar wannan rubutu ita ce bayani a kan janibobi daban-daban da suka shafi birnin Qom domin sauƙaƙe muku bincike da kuma yanke shawara dangane da karatu a Qom. Ku kasance tare da mu.

Karatu a QomQom

Birnin Qom shi ne birni na 7 mafi girma kuma nan ne cibiyar lardin Qom a wajajen tsakiyar Iran. A aikin ƙidaya na ƙarshe da aka gudanar an samu kimanin mutum 1,201,158 a cikinsa. Saboda kasancewar haramin Sayyada Ma’asouma (AS) ƴar’uwar Imam Rida (AS) a wannan wuri, Qom gari ne na addini kuma ɗaya daga cikin wuraren ziyarar ƴan’uwa musulmi musamman mabiya mazhabin ahlulbaiti. Nan ne babbar cibiyar da ke ba ma ƴan’uwa mabiya mazhabin shi’a gurbin karatu (scholarship) a duniya. A kowace shekara ana samun kimanin mutum miliyan 20 da suka ziyarci birnin Qom.

Bayanai game da Qom

Babu nisa daga Qom zuwa masallacin jamkaran ta yadda kusan duka maziyarta sukan garzaya zuwa masallacin na jamkaran idan sun tafi Qom. Masallacin Jamkaran ɗaya ne daga cikin muhimman wuraren ibada a wurin mabiya shi’a wanda akwai mabambantan riwayoyi da ke nuna Imam Mahdi (ATF) Imami na 12 a jerin limaman shiriya ya kan halarci wannan masallacin.

Zirga-Zirga

Yana da kyau ku san cewa birnin Qom tashar jirgin ƙasa kawai yake da ita domin tafiye-tafiyen zuwa wasu garuruwa.

Qom na da babbar hanya biyu ta jirgin ƙasa; Tehran – Qom da kuma Qom – Isfahan wanda ake kan ginawa yanzu haka.

A rana ɗaya a Qom ana samun kimanin motocin bus 300 masu kai-komo a hanyoyi 40 na cikin gari domin amfanin mutanen gari. Yanzu haka akwai manyan hanyoyi guda 8 da suka keɓabci motocin autobus, wadda aka fi amfani da ita a cikinsu ita ce hanyar layi na 1, wato hanyar da ke zuwa masallacin Jamkaran daga Beheshte Ma’asoumeh.

An fara aikin samar da hanyar metro daga Qom zuwa masallacin Jamkaran har zuwa arewa maso yammacin garin Kamkar. Akwai tashoshi 14 a wannan hanyar da suke cikin Qom.

Wuraren shaƙatawa

Qom na daga cikin tsoffin garuruwan ƙasar Iran waɗanda suka shaida abubuwa da dama da suka faru a baya; wannan ne ya sa yanzu akwai birbishi na waɗannan abubuwan na tarihi a cikinsa. Daga cikin muhimman abubuwa da wurare na tarihi da ke wannan gari na Qom akwai haramin Sayyada Ma’asouma, masallacin Jamkaran, masaukin baƙi na Hauz Sultan, babban masallacin Qom, makarantar Faizieh ta Qom, da Nimche Bazaar.

Yawon buɗe ido a Qom

Karatu a Qom

Kasantuwar birnin Qom cibiya mai muhimmanci ta addini ya sa hankalin ɗaliban addini da yawa ya karkata can.

Daga cikin muhimman cibiyoyin ilimi da ke wannan garin akwai Jami’ar Qom. Jami’ar na da makarantu 6 tare da cibiyoyin koyarwa da fasaha guda 7.

Jami'o'in Qom

Cibiyoyin kiwon lafiya

_ Asibitin Shahid Fatahi
_ Asibitin Imam Reza (As)
_ Asibitin Imam Ali bn Abi Talib
_ Asibitin Kamkar-Arabnia
_ Asibitin Vali Asr
_ Asibitin Golpeygani
_ Asibitin Shahid Beheshti
_ Asibitin Izadi
_ Da sauransu….

Dalilin karatu a Qom

  • Idan kuna tunanin karatu a Qom yana da kyau ku san cewa garin Qom zai iya zama zaɓi mai kyau a gareku domin kuwa kuɗin karatu a wannan gari suna da sauƙi idan an kwatanta da sauran manyan garuruwa irin su Tehran hakazalika ba wani ƙarin azo a gani ke akwai a kuɗin masauki ba, saboda haka ba ku da matsalar tsada a wannan gari. Amma zai fi sauƙi ku yi amfani da hostel da masaukan baƙi da ke cikin gari.
  • Jami’ar Qoma na cikin jami’o’in iran mafi kyau kuma mafi inganci. Hakazalika takardun kammalawa da take bayarwa ana karɓarsu a sauran ƙasashen duniya. Jami’ar ta yi tanadin ingantattun kayan aiki na karatu irinsu laburare, ɗakunan gwaje-gwaje, wuraren wasanni, wuraren cin abinci, da sauransu don amfanin ɗalibanta.

Karatu a Iran

Karatu a Tehran

Karatu a Mashhad

Related Posts
Leave a Reply