Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Petroleum University of Technology

Karatu a Petroleum University of Technology

Loading

Petroleum University of Technology Jami’ar gwamnati ce wadda ta ƙunshi kwalejin Petroleum na Ahvaz, Kwalejin Petroleum na Abadan, Kwalejin Petroleum na Tehran, da kwalejin kimiyyar teku na Mahmud Abad, wasu ne daga cikin cibiyoyin koyarwa na gaba da sakandare a Iran. Ku kasance tare da mu domin samun cikakken bayani game da karatu a jami’ar fasahar man fetur (Petroleum University of Technology).

Gabatarwa

Petroleum University of Technology jami’a ce ta gwamnati a garin Abadan na lardin Khozestan, wadda aka assasa a shekarar 1939. A halin yanzu akwai ɗalibai 300 da malamai 77 a jami’ar. Jami’ar na da lambar yabo, kuma zuwa yanzu ta wallafa maƙala 2362 na ilimi a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida. Jami’ar fasahar man fetur ta mallaki lambar yabo, sannan ta wallafa mujalla 2 na musamman, kuma zuwa yanzu ta shirya taruka 7. Har ila yau, jami’ar ta yi nasarar wallafa maƙala 2013 a matakin ƙasa da ƙasa. A shekarar 2023, manazarta da masu bincike na jami’ar sun wallafa akasarin maƙalolinsu ne da muhimman kalmomin “pushing resistance” da “Shallow wells”.

A halin yanzu, jami’ar fasahar man fetur na karɓar ɗalibai a kowace shekara a duka makarantunta 4, a mabambantan kwasa-kwasai ta hanyar jarabawar shiga ta ƙasa. Tana karɓar ɗalibai ne a matakin digiri, mastas, da PhD, sannan ana koyar da duka muhimman darusa (specialized courses) a yaren turanci ne. A matakin ƙasa da ƙasa, ana yi wa wannan jami’a laƙabi da sunan “PUT”.

Karatu a Petroleum University of Technology

Martabar Jami’a

Wannan jami’a ta yi nasarar tarbiyyantar da injiniyoyi da ƙwararrun masana a fannoni daban-daban masu alaƙa da masana’antun man fetur, wanda hakan ya taimaka sosai wurin bunƙasa masana’antun man fetur a faɗin duniya. Ko da yaushe ana jin nasarori da ƙaurin suna na ƙwararrun masan waɗanda suka samu horo a wannan jami’a, a mafi yawan jami’o’i da manyan kamfanoni na duniya.
A bayyane yake cewa jajircewa da ƙoƙarin da ake yi a cikin jami’ar fasahar man fetur zai daɗa ƙaruwa ne a kullum, hakazalika masana’antar man fetur na da fata wurin samar da gagarumin cigaba ta hanyar ƙwararrun masana da ma’aikatan wannan jami’ar.

Bisa dogaro da sabon bayanin martabar jami’o’i da tsarin ranking na “Scimago” ya fitar a shekarar 2022, a fannin “Geology”, jami’ar fasahar man fetur ta samu matsayi na farko tsakanin jami’o’in Iran, matsayi na farko a gabas ta tsakiya, da kuma matsayi na 7 a duniya. Kamar yadda wannan tsarin raking ɗin ya nuna, jami’ar fasahar man fetur (a mabambantan fannoni), ta sami matsayi na 697 a duniya.

A tsarin ranking na C. W. U. R kuma, a shekarar 2017, jami’ar fasahar man fetur ta samu matsayi na 7 tsakanin manyan jami’o’in duniya a fannin Petroleum Engineering.

Makarantu

  • Abadan Faculty of Petroleum
  • Ahvaz Faculty of Petroleum
  • Tehran Faculty of Petroleum
  • Mahmudabad Faculty of Petroleum

Tehran Faculty of Petroleum

Tehran Faculty of Petroleum ita ce makarantar Accounting da Financial sciences na masana’antar mai ta ƙasa wadda aka assasa a shekarar 1957 inda ta fara aiki a matsayin cibiyar koyrwa da bincike domin samarwa da bunƙasa kimiyyar ɗan’adam da kuma samar da buƙatun masana’antun man fetur na ilimi da bincike na ƙasa. Wannan kwalejin ita ce ta fara kwas ɗin Accounting a Iran.

Domin tarbiyyantar da ma’aikata gwargwadon yawan buƙatun masana’antun mai a fannoni da matakan karatu daban-daban musamman fannin Human Science, jami’ar ta fara karɓar ɗalibai tun daga watan September na shekarar 2013 a matakin mastas, a fannoni 4 na Oil and Gas Economics, Oil and Gas Law, Financial Management, da Management of hydrocarbon reservoirs. A shekarar 2014, an sanya kwas ɗin Project Management a jerin kwasa-kwasan wannan kwalejin.

Karon farko kenan da aka fara waɗannan kwasa-kwasai uku a Iran; Management of Hydrocarbon Reservoirs, Finance, da Investment in Oil and Gas. A lokaci guda, an shirya tsarin karatu na kwas ɗin Management of Hydrocarbon Reservoirs da na Financing and Investment in Oil and Gas ne a wannan kwalejin.

Ahvaz Faculty of Petroleum

Ayyukan koyarwa na Ahvaz Faculty of Petroleum sun fara ne daga shekarar 1983 (a lokacin yaƙin Iran da Iraq). An gudanar da waɗannan ayyukan ilimi da na bincike ne a fannin tace mai da iskar gas, da kuma Petrochemical Engineering.

Wannan kwaleji ita ce mafi girma daga cikin kwalejojin jami’ar, Kuma tana cikin garin Ahvaz. Kwas mafi muhimmanci a matakin digiri na wannan kwalejin shi ne Petroleum Engineering, sannan akwai kwasa-kwasan Electrical da Chemical Engineering.

Abadan Faculty of Petroleum

Kafin mai ya dawo ƙarƙashin ikon gwamnati, kamfanin mai na Birtaniya da Iran yana da makaranta a Abadan wadda ke karɓar ɗalibai waɗanda suka kammala karatun sakandare tare da ba su digirin Engineering bayan shekaru uku na karatu. Kashi biyu bisa uku na injiniyoyin kasar Iran na masana’antun mai wannan cibiyar ce ta samar da su, sauran kuma an samar da su ne daga babban gidan ajiye kayan tarihi da ke birnin Tehran.

Bayan mayar da man fetur ƙarƙashin gwamnati da kuma cire hannu daga kamfanin mai na Iran da Birtaniya, an rufe wannan makarantar mai. Bayan juyin mulkin 28 Mordad a shekarar 1953, Ali Asgar Pourhomayoun ya yanke shawarar kafa kwalejin man fetur a makarantar fasaha ta gaba da sakandare, wanda aka ware daga majalisar al’adu aka mayar da ita zuwa majalisar tattalin arziki ta ƙasa shekaru biyar kafin lokacin. Ministan tattalin arziki na ƙasa Fakhreddin Shadman wanda ya hau kan karagar mulki a shekara ta gaba, yana da ra’ayin cewa ya kamata ɗaliban jami’ar man fetur su karanci darussan theory a Tehran, darussan practical kuma a Abadan, amma ra’ayin Reza Jafari ministan harkokin man fetur da al’adu shi ne a mayar da malamai Abadan, inda aka aiwatar da wannan ra’ayin nasa bisa amincewar majalisa.

Mahmodabad Faculty of Marine Science

Ɗaya ce daga cikin cibiyoyin koyar da marine sciences na farko da suka fara aiki a shekara ta 1985 a birnin Mahmudabad da lardin Mazandaran. Wannan cibiya, wacce ɗaya ce daga cikin kwalejojin jami’ar fasahar man fetur, tana horar da ma’aikatan ruwa da za su yi aiki a kan jiragen ruwa da ke tafiya tekuna. Bayan kammala karatun ɗalibai a wannan cibiya, yawanci kamfanonin sufurin jiragen ruwa na ƙasar Iran ne ke ɗaukarsu aiki, kamar kamfanin dakon man fetur na Iran da kuma jigilar kayayyaki na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Karatu a Petroleum University of Technology

Kwasa-Kwasai

Digiri:

  • Safety Engineering and Technical Inspection
  • Chemical Engineering
  • Petroleum Engineering
  • Mechanical Engineering
  • Electrical Engineering
  • Acoounting

Masters:

  • Chemical Engineering – HSE
  • Oil Exploration Engineering
  • Mechanical Engineering – applied design
  • Civil Engineering – Engineering of coasts, ports and marine structures
  • Technical Inspection Engineering
  • Petroleum Engineering – Exploitation
  • Petroleum Engineering – hydrocarbon tanks
  • Petroleum Engineering – drilling
  • Gas Processing and Transmission Engineering
  • Instrumentation and Automation Engineering
  • Finance – financing and investing in oil and gas
  • Oil and Gas Law
  • Oil and gas Economics
  • Management of Hydrocarbon Reservoirs

PhD:

  • Petroleum Engineering
  • Chemical Engineering – transfer phenomena and separation processes

Kuɗin makarantar jami’ar fasahar man fetur

MajorsAnnual tuition in dollars
Bacholar 1,100$
Masters 1,400$
PhD2,800$

Alfanun karatu a jami’ar fasahar man fetur

– Domin inganta yawa da ingancin malamai da membobin tsangayar ilimi da samun sabbin fasahohi, Jami’ar fasahar man fetur tana da damar yin ayyuka na haɗin gwiwa tare da sauran manyan cibiyoyin bincike da masana’antu na duniya.

– Jami’ar na ba wa ɗalibanta damar yin amfani da wuraren da suka dace na karatu da walwala a yayin karatunsu.
-Saboda kusancin da take da shi da ƙungiyoyin mai da iskar gas na musamman, jami’o’i da manyan kamfanonin mai na duniya, jami’ar ta samar wa da ɗalibai da malamanta damar aiki tare da waɗannan ƙungiyoyin.

– A tsawon lokacin karatunsu, ɗaliban wannan jami’a suna da damar kasancewa a cikin masana’antar man fetur da kuma yiwuwar samun gogewar ilimin kimiyya a masana’antar.

– Gabatar da abubuwan karatu a harshen turanci yana ɗaya daga cikin alfanun karatu a wannan jami’a.

– Wurare na musamman na ilimi da jin daɗin rayuwa waɗanda ke taimaka wa ɗalibai wurin samun ingantaccen ilimi a wannan jami’a.

– Ba da tallafin karatu ga ɗalibai.

Ababen More Rayuwa

  • Alaƙa da muhimman ma’adanan bayanai da ingantattun wallafe-wallafen ilimi na ƙasashen waje kamar Onepetro, tare da damar downloading kyauta
  • Zuwan manyan kamfanonin mai irin su Total France don gudanar da hirarraki da ɗaliban da suka kammala karatunsu tare da bayar da scholarship
  • Intanet mai yawa da cajin kai-tsaye na mako-mako, ba tare da biyan kuɗi ba
  • Gidan cin abinci mai inganci, mai sayar da abinci sau uku a kowace rana
  • Karɓar litattafai da takardu kyauta waɗanda malamai suka yi amfani da su wurin koyar da ɗalibai a kowane zangon karatu a kwalejin
  • Karɓar tallafin karatu a kowane wata
  • Cikakkun kayan wasanni da na more rayuwa (filin ƙwallo, swimming pool, gym, zauren wasannin badminton, dart, chess, da sauransu) a kusa da hostel
  • Amfani da mafi ingancin kayan aikin ɗakunan gwaje-gwaje idan an kwatanta da sauran jami’o’in kasar

Karatu a Petroleum University of Technology

Wuraren kwanan ɗalibai

Wurin kwanan kwalejin Abadan:

Wannan kwalejin na da gine-gine guda 7 masu hawa biyu-biyu, kowane hawa na da sassa daban-daban masu ɗakunan kwanan mutum 4, mutum 3, da na mutum 2 tare da banɗakai, talabijin, kitchen, firiji, ac, teburin karatu da sauran kayan buƙatar ɗalibai.
Wannan hostel zai iya ɗaukar kimanin mutum 650.

Wurin kwanan kwalejin Tehran:

A wannan kwalejin ana ba duka ɗaliban da suke nesa masu buƙata wurin kwana. Ma’aikatar ilimi ta tantance duka wuraren kwanan wannan kwalejin sannan ana bai wa ɗalibai masauki ne bisa la’akari da tsawon lokacin karatunsu. Kwalejin na da hostel guda biyu.

Hostel ɗin kwalejin Marine Sciences na Mahmodabad:

Saboda gabatar da kwasa-kwasai da ake karantawa dare da rana, jami’ar ta yi ƙoƙarin samar da wuraren kwanan ɗalibai masu yalwa tare da abubuwan buƙata da suka dace. Kwalejin na da wuraren kwana kusan guda 50 masu ɗakunan kwanan mutum 2 ɗauke da abubuwan buƙatun ɗalibai kamar gado, teburi, kujeru, na’urorin ɗumamawa da sanyaya wuri, da sauransu. Hakazalika akwai ɗakin malamai ɗauke da isassun kayan aiki da aka tanada domin malamai.

Bugu da ƙari, akwai yanayi mai daɗi a inda wuraren kwanan suke tare da sautin kaɗawar taguwar ruwa wanda ke ƙara samar wa ɗalibai sukuni.
Hakazalika kwalejin na ba ma ɗalibai abinci sau uku a rana (safe, rana da dare) a duka ranakun sati (har a ranakun hutu), da tunanin cewa abincin da ake ba ɗalibai ya cika dukan sharuɗa ta fuskar yawa da kuma ingancinsa.

Yanayin wurin da jami’ar take

Adireshi:

Tehran: Titin Sattarkhan, titin Shahid Sadeghipour na kudu, titin Ghasemizadeyan

Ahvaz: Kot Abdallah, Kot, babban titin Behbahani

Abadan: Bawardeh ta yamma, Kwalejin man fetur na Abadan

Mahmodabad: Mahmodabad, Sadaf, titin Nateqnori

Shafin Jami’a:https://www.put.ac.ir

Related Posts
Leave a Reply

Your email address will not be published.Required fields are marked *