Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Jami'ar Bu-Ali Sina

Karatu a Jami’ar Bu-Ali Sina

Loading

Jami’ar Bu-Ali Sina University (Bu-Ali Sina University) ita ce cibiyar ilimi mafi girma kuma tushen tarihi da wayewar Iran wadda ke tsakiyar garin Hamedan kuma a ƙasan dutsen Estreg Elvand; ingancin abubuwan ilimi da jami’ar ta samar da kuma bunƙasar karatunta na gaba da digiri, ya kai mataki mai kyau. A ci gaban wannan rubutun mun kawo muku bayanai dangane da yanayin karatu a jami’ar Bu-Ali Sina. Ku kasance tare da mu.

Gabatarwa

An ɗauki matakin farko na buɗa Bu Ali Sina a watan Maris na shekara ta 1973 bisa yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin Iran da Faransa; Shekara guda bayan haka, aka karɓo izinin buɗa ta a garin Hamedan daga majalisar bunƙasa manyan makarantu, a 1974 kenan. Bu Ali Sina ta fara ayyukanta na koyarwa a shekarar 1977 ta hanyar ɗaukar ɗalibai 200 daga matakin associate degree zuwa masters a kwas huɗu; Agriculture, Health Sciences, Environmental Sciences, da Educational Sciences.

Girman gine-ginen muhallan karatu na jami’ar ya kai kusan murabba’in mita 250,000 a wani fili mai girman hekta 122.

A halin yanzu wannan jami’ar tana da membobin tsangayar ilimi guda 440, ma’aikata 700, da kimanin ɗalibai 12,000 masu karatun a fannoni 317 a matakan digiri, mastas, da Phd. Hakazalika ta yaye kusan ɗalibai 47,000.

Daga cikin membobin tsangayar ilimi na wannan jami’a akwai waɗanda suka samu nasarori kamar; samun nasara a gasa daban-daban ta ilimi a matakin cikin gida da kuma ƙasa da ƙasa, zaɓar gwarzon malami na ƙasa, manyan masana kimiyya a duniyar musulunci, kaso na farko na manyan fitattun masana kimiyya na duniya, membobin da suka samu waɗannan nasarori sun haɗa da Abbas Afkhami Oghada, Mohammad Ali Zolfigol, Dawood Nematoullahi, Mohsen Jalali, Mohammad khanjani, Golamhosein Majzobi, da Omid Tabibzadeh Ghamsari.

Martabar Jami’a

A cewar tsarin ranking na Webometric, jami’ar Bu-Ali Sina ta samu matsayi na 1825 a jami’o’in duniya, matsayi na 561 a yankin Asia, matsayi na 80 a gabas ta tsakiya, da kuma matsayi na 23 a jami’o’in Iran. Har ila yau, tsarin ranking na Times ya bayyana jami’ar Bu Ali Sina a matsayi na 601-800 a fannin Engineering Sciences, matsayi na 801-1000 a fannin Physics, matsayi na 800+ a fannin Biology, matsayi na 301-350 a jami’o’in yankin Asia.

Hakazalika tsarin ranking na Leiden ya bayyana jami’ar a matsayi na 1000, a ma’aunin ISC kuma, jami’ar ta samu matsayi na 50 tsakanin jami’o’in Iran. Baya ga haka, jami’ar ita ce ta 5 a jami’o’in Iran ta fuskar ziyartar maƙaloli, idan an duba yawan masanan ISI tana matsayi na 5 nan ma.

Bayanai sun nuna cewa zuwa yanzu jami’ar Bu-Ali Sina ta wallafa maƙalolin ilimi guda 14193 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida. Har ila yau, jami’ar ta wallafa mujalla 2 na musamman tare da maƙala 979 a matakin ƙasa da ƙasa.

 

Makarantu da kwasa-kwasai

 • Faculty of Literature and Humanities
  • Jurisprudence and Principles of Islamic Law
  • Law
  • Arabic Language and Literature
  • Persian Language and Literature
  • Educational Science
  • French Language and Literature
  • English Language Translation
  • Study of Iran
 • Facuty of Agriculture
  • Water Science and Engineering
  • Biosystem Mechanical Engineering (Agriculture)
  • Promotion and Education of Sustainable Agriculture
  • Production Engineering and Plant Genetics
  • Horticultural Science and Engineering
  • Soil Science and Engineering
  • Animal Science
  • Plant Medicine
  • Engineering of Food Industry Machines
 • Faculty of Engineering
  • Electrical Engineering
  • Industrial Engineering
  • Civil Engineering
  • Industrial Engineering
  • Computer Engineering
  • Mechanical Engineering
  • Material Engineering and Metallurgy
 • Faculty of Economic and Social Sciences
  • Political Science
  • Psychology
  • Sociology
  • Acoounting
  • Economic
 • Kwalejin Basic Sciences
  • Statistics
  • Mathematics and Applications
  • Physics
  • Geology
  • Plant Biology
 • School of Arts and Architecture
  • Archaeology
  • Architectural Engineering
  • Video Connection
  • Painting
 • School of Chemistry
  • Applied Chemistry
  • Pure Chemistry
 • School of Paramedicine
  • Veterinary Laboratory Science
  • Associate of Veterinary Medicine
  • Food Health
 • Faculty of Technology and Natural Resources (Reshen Toisarkan)
  • Computer Engineering
  • Science and Engineering of Food Industry
 • Faculty of Technology and Engineering (Reshen Kabudarahang)
  • Industrial Engineering
  • Civil Engineering
  • Urban Engineering
 • Faculty of Management and Accounting (Rozen Branch)
  • Accounting
  • Business Management
  • Government Management
  • Industrial Management
 • Faculty of Food Industry (Reshen Bahar)
  • Science and Engineering of Food Engineering Industries (Agriculture)

 

Kuɗin Makarantar Bu-Ali Sina University

Cibiyoyin Bincike

 • Plant Chemistry Research Center
 • Water Research Institute
 • APA Center of Bu Ali Sina University

Ɗakunan Gwaje-Gwaje (na bincike)

 • Central Laboratory
 • Residual Stress Laboratory
 • Strength of Materials Laboratory
 • Materials Laboratory
 • Archaeological Laboratory
 • Laboratory of Robot Intelligence and Vision

Ababen More Rayuwa

 • Laburare mai ɗauke da dubban litattafai na kowa da kowa da kuma keɓantattu
 • Gidan tarihi na ɗabi’a
 • Swimming Pool
 • Zaurukan wasanni guda 11
 • Hanyoyin kekuna
 • Buɗaɗɗen filin wasa

Wannan jami’a na da wuraren kwana 3 na maza da na mata guda 10.

Wuraren kwanan ɗalibai

 • -Wurin kwana na Ghadir 1, 2, da 3 (Na maza)
 • -Wurin kwana na Farzanegan 1, 2, da 3 (Na mata)
 • -Wurin kwana na Farzanegan 1, 2, da 3 (Na ɗalibai mata)
 • -Wurin kwana na Kowsar (Na mata)
 • Wurin kwana na Shahedane Bahadorbigi (na maza)
 • Wurin kwana na Shahedane Mohaghegh (na maza)
 • Wurin kwana na Hazrat Zainab (AS) (Ana kiransa da Wurin Kwana na Yas) – na mata
 • Wurin kwana na Ma’asomieh (na mata)
 • Wurin kwana na Farhang (na maza)

Yanayin Wuri

Adireshi: Hamedan, Chahar Rahe Bagh Shahid Mostafa Ahmadi Roshan, Bu Ali Sina University

Shafin jami’a: https://basu.ac.ir


Tambayoyin da ake yawan yi game da jami’ar Bu-Ali Sina

 1. Minene alfanun karatu a wannan jami’a?
  Wannan jami’a kasantuwar tana da matsayi mai kyau a ƙasa da duniya baki ɗaya, ɗaya ce daga cikin jami’o’in gwamnati mafi kyau a garin Hamedan, a rubutunmu mun ambaci duka matsayin ta na ilimi.
 2. Wasu irin kayan aiki wannan jami’a take da?
  kayan aikinta sun haɗa da ɗakunan gwaje-gwajenta waɗanda ke ɗauke da kayan aiki na zamani, laburare, cibiyar kiwon lafiya, da sauransu. Shi ma duk mun ambata a cikin wannan rubutun.
 3. Jami’ar Bu-Ali Sina makarantu nawa take da, kuma a wasu kwasa-kwasai take karɓar ɗalibai?
  Wannan jami’a tana da makarantu 13, kuma a kowace shekara tana karɓar ɗalibai a kwas 319, mun ambaci kwasa-kwasanta a cikin rubutu.
Related Posts
Leave a Reply