[gtranslate]
مشهد، میدان شریعتی، نرسیده به احمد آباد ۱، طبقه بالای بانک دی

Karatu a Urmia University of Technology

Karatu a Urmia University of Technology

Loading

Urmia University of Technology (Jami’ar Fasaha ta Urmia), jami’ar gwamnati ce a garin Urmia wadda aka assasa a shekarar 2005. Bayan wannan jami’ar akwai Urmia University of Medical Sciences, da Urmia University duk a garin na Urmia. A cigaban wannan rubutu mun kawo muku bayanai game da yanayin karatu a wannan jami’a ta fasaha ta garin Urmia.

Gabatarwa

Jami’ar ta fara aiki ne a shekarar 2005 a matsayin jami’ar fasaha ta farko a lardin Urmia. Yanzu haka akwai makarantu ko kwaleji 4 a ƙarƙashinta. Jami’ar Fasaha ta Urmia jami’ar gwamnati ce a garin Urmia, lardin Azarbaijan ta yamma.

A halin yanzu akwai ɗalibai 4895 da malamai 105 a jami’ar. Bincike ya nuna cewa jami’ar fasaha ta Urmia ta wallafa maƙalar kimiyya guda 1582 zuwa yanzu a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida, tare da maƙala 108 a matakin ƙasa da ƙasa. A shekarar 2023, masu bincike na jami’ar fasaha ta Urmia sun wallafa akasarin maƙalolinsu da kalmomin “Adsorption” da “Electrohydraulic shock” a matsayin muhimman kalmomi.

Karatu a Urmia University of Technology

Martabar Jami’a

A sabon sakamakon da tsarin tantance jami’o’i na Scimago ya gabatar, jami’o’i 154 ne daga ƙasar Iran suka samu shiga jerin jami’o’in da aka tantance, daga ciki akwai jami’ar fasaha ta Urmia (Urmia University of Technology) wadda ta samu matsayi na 742 a tsakanin jami’o’in duniya, kuma ta zo a cikin fitattun jami’o’in fasaha 13 na Iran.
Ƙungiyar ta Scimago wadda ke ƙasar Spain ta yi fice a wurin tantance jami’o’in duniya sannan ta fara aikin ne a shekarar 2009 tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Elsevier wurin tantancewa da martaba jami’o’i bisa la’akari da ma’aunai guda 3 kamar haka; Ayyukan bincike maki 50, ƙirƙire-ƙirƙire maki 30, da mu’amala maki 20.

Sakamakon tsarin ranking na Webometrics kuma ya bayyana jami’ar fasaha ta Urmia a matsayin jami’a ta 3348 tsakanin jami’o’i 31000 na duniya, da kuma matsayi na 12 a tsakanin jami’o’in fasaha na ƙasar Iran a shekarar 2021.

Kuɗin makarantar Jami’ar Fasaha ta Urmia

DegreeTuition FeeFarsi courseAccommodation Per semester
Bachelor$800$200$200
Master$1,000$200$200
Ph. D$1,200$250$200

Makarantu

  • Faculty of Renewable Energy
  • Faculty of Industrial Technologies
  • Environment College
  • Khoi Technical and Engineering Faculty

Karatu a Urmia University of Technology

Kwasa-Kwasai

  • Engineering Technology for Manufacturing and Production of Machine tools
  • Manufacturing and Production Technology Engineering – molding trend
  • Information Technology
  • Mechanical Engineering of Solids
  • Mechanical Engineering – heat and fluid
  • Industrial Engineering – industrial production
  • Chemical Engineering – petrochemical industries
  • Chemical Engineering – food industry
  • Mining Engineering – exploration
  • Electrical engineering – electronics
  • Computer Engineering – software
  • Industrial Engineering – industries
  • Mechanical Engineering – energy conversion
  • Civil Engineering – structural
  • Information Technology Engineering

Bunƙasar gine-ginen jami’ar

A ranar 25 ga watan February na shekarar 2007, jami’ar fasaha ta Urmia ta fara aiki a wani wuri mai girman hekta 2, kilomita biyu da rabi daga farkon hanyar Band-Ziveh. Gininta na yanzu mai girman kimanin murabba’in mita 2000, a da can ma’aikatar ruwa ta lardin ce ke amfani da shi da sunan “Cibiyar nazari da bincike a kan ruwa da ƙanƙara”. Ƙaruwar yawan ɗalibai da kuma buƙatuwa da wurin karatu mai yalwa ya sanya mas’ulan jami’ar fara yunƙurin samar da kwaleji ta farko a watan August na shekarar 2007.

Kwalejin farko na Petrochemical Engineering ya fara aiki a watan September na shekarar 2008 a wani fili mai girman murabba’in mita 900 a gine-gine masu girman murabba’in mita 2500 a jimlace. Buƙatuwa da ɗakin karatu da ɗakin kwamfuta ya saka a lokaci guda tare da gina sashe na farko na kwalejin Petrochemical Engineering, mai girma gwamna ne ya aza tubalin gine-ginen sashen administration a watan May 2008, wanda ƙwararrun ƴan kwangila suka gina shi da kyakkyawar siffa kuma girmansa zai kai murabba’in mita 850. Hauhawar yawan ɗaliban da ake ɗauka ya sanya aka fara aikin gina sashe na biyu na kwalejin Petrochemical Engineering a watan March na shekarar 2009. Baya ga jona shi da hedikwata da sashe na farko na kwalejin Petrochemical Engineering, wannan aikin ya samar da rukunin gine-gine masu ɗauke da keɓantattun abubuwa na musamman.

Ofishin Sadarwar Masana’antun Jami’a

An assasa wannan ofishin da nufin haɓaka ƙarfin kimiyya da tafiyarwa na ɗalibai a kwasa-kwasan fasahar Engineering da kuma biyan buƙatun masana’antu a ilmance, da samar da tsararriyar mu’amala tsakanin ma’aikatan masana’antu da na jami’o’i.

Yanzu haka wannan ofishin yana aiki tuƙuru wajen bunƙasa ilimi da masana’antun ƙasar Iran ta hanyar shirya daurorin koyon aiki ga ɗalibai da kuma shige musu gaba wurin shirya ziyarorin ƙarin ilimi a sassa daban-daban na masana’antu a fagen ayyukan bincike. Har ila yau, wannan ofishin baya ga ƙulla yarjejeniyar haɗin gwiwa da ƙungiyar bunƙasawa da sabunta masana’antu, ya taka muhimmiyar rawa wurin aiwatar da mu’amalar masana’antu da jami’o’i, sannan yana da shirin aiwatar da ayyuka a matakin ƙasa da na yanki tare da wannan ƙungiyar.

Karatu a Urmia University of Technology

Ababen More Rayuwa

Wannan jami’a na da hostel guda biyu na ɗalibai maza, da biyu na ɗalibai mata. Hostel ɗin maza: 1- Khalili: matakin digiri 2- Ithar: matakin masters. Hostel ɗin mata: 1- Beheshti: digiri 2- Sadr: masters. Akwai motar makaranta kyauta mai jigilar ɗalibai zuwa junction ɗin jami’a.

Yanayin Wuri

Jami’ar fasaha ta Urmia na nan a unguwar Janveslu ta garin Urmia, titin Shahid Beheshti, babbar hanyar Band-Ziveh. Jami’ar na kusa da wurare kamar wurin juye na Ghadiri, da ginin Shahrak Electronics Technology Services a garin Urmia.

Adireshi: Garin Urmia, Janveslu, titin Shahid Beheshti, hanyar Band-Ziveh

Shafin jami’a: https://uut.ac.ir

Related Posts
Leave a Reply