تهران، میدان ولیعصر، جنب سفارت عراق، ساختمان مینو
مشهد، میدان شریعتی، نرسیده به احمد آباد ۱، طبقه بالای بانک دی

Karatu a Jami'ar Allameh Tabataba'i

Karatu a Jami’ar Allameh Tabataba’i

Loading

Jami’ar Allameh Tabataba’i ɗaya ce daga cikin ingantattun jami’o’in gwamnati na Iran a garin Tehran. Jami’ar na daga cikin manyan jami’o’i ƙwararru a fannonin Human Science, Social Science, Economic Law, da Management ta yadda da yawan fuskokin ilimi da na siyasa da kuma jigogin ilimi daban-daban da na al’umma sun yi karatu ne a wannan jami’a. Ku kasance tare da mu domin samun bayanai a kan yanayin karatu a wannan jami’a ta Allameh Tabataba’i.

Gabatarwa

Jami’ar Allameh Tabataba’i jami’a ce da juyin musulunci ya samar dukda cewa ginshiƙinta na da tsufan shekaru 60. Bayan juyin musulunci, duba da buƙatuwar da ake da ita ga samar da jami’a ta musamman wadda za ta bada ƙarfi a fannonin Human Science da Social Sciences, an yi amfani da cibiyoyin koyarwa masu zaman kansu, kwalejoji, cibiyoyin bincike, makarantun gaba da sakandare, mu’assasoshi, da ƙungiyoyi waɗanda aka assasa bayan shekarar 1958 aka samar da rukuni biyu na jami’o’i da sunan; Rukunin karatu na Literature and Human Sciences, da kuma Rukunin karatu na Administrative and business Sciences.

Kowane daga cikin waɗannan rukunan ya ci gaba da aiki a ƙashin kansa na tsawon shekara 5, daga bisani ranar 7 ga watan July na shekarar 1984 bisa amincewar majalisar ƙoli ta sauyin al’adu, aka haɗe su aka assasa jami’ar Allameh Tabataba’i.

A halin yanzu jami’ar Allameh Tabataba’i ta taka babban matsayi a ƙasar Iran a fannonin Human Sciences kuma ita ce kan gaba wajen bunƙasa da haɓaka ilimin kimiyyar ɗan’adam da zamantakewa a ƙasar ta hanyar amfani da ƙwarewa da tajarubar malamanta da masu bincike, al’umma na amfana sosai da ayyukan jami’ar. Da yawan sanannun fuskokin ilimi da na siyasa hakazalika jigogin ilimin kimiyyar ɗan’adam na ƙasar Iran a wannan jami’a suka yi karatu.

Yanzu haka jami’ar Allameh Tabataba’i ita ce kaɗai jami’ar musamman ta ilimin kimiyyar ɗan’adam wato Human Sciences da kuma ilimin zamantakewa wato Social Sciences a ƙasar Iran kuma tana da makarantu guda 10 da babbar cibiyar koyarwa guda 1, graduate campus 1, growth center 1, da cibiyoyin bincike guda 9, kuma tana karɓar ɗalibai a kwas 226 a matakin digiri, mastas, da PhD. Akwai membobin tsangayar ilimi guda 530 masu aiki full-time a jami’ar yanzu haka. Tun assasa wannan jami’ar zuwa yanzu ta yaye kimanin ɗalibai 77,000 sannan yawan ɗaliban da ke karatu a cikinta a shekarar 2016/2017 ya kai 18000.

Karatu a jami'ar Allameh Tabataba'i

Martabar Jami’a

A bayanan da tsarin sa ido da tantancewa da martaba jami’o’in ƙasar Iran ya fitar a shekarar 2016, an gabatar da jami’ar Allameh Tabataba’i a matsayin jami’a mai daraja ta ɗaya a Iran. Saboda ƙoƙarin haziƙan membobin tsangayar ilimin wannan jami’a ta Allameh Tabataba’i, haziƙan ɗalibai da ma’aikatanta wurin bin irin salon shugaban makarantar tun shekarar 2013, jami’ar ta samu cigaba mai yawan gaske. Samun taken jami’ar daraja ta ɗaya da kuma matsayin jami’a ta ɗaya a tsakanin manyan jami’o’i 12 na Iran ne shaidar wannan iƙirarin.

An zaɓi Allameh Tabataba’i University a matsayin jami’ar daraja ta ɗaya bisa la’akari da wasu ma’aunai na ayyukan koyarwa da bincike a shekarar da ta gabata tare da Sharif University of Technology, Iran University of Science and Technology, Amirkabir University of Technology da Isfahan University of Technology wanda wannan ma wani abun alfahari ne ga jami’ar.

A sabon sakamakon da tsarin ranking na TIMES ya fitar, Jami’ar Allameh Tabataba’i ta samu shiga sahun manyan jami’o’in duniya a matsayin jami’ar da ta keɓanta da ilimin kimiyyar ɗan’adam da zamantakewa wato Human Sciences da Social Sciences a karon farko, inda jami’ar ta samu matsayi na 1206 bayan ta kara da jami’o’i 2673 na duniya.

Kuɗin Makarantar Jami’ar Allameh Tabataba’i

DegreesDurationAnnual Tuition ( in Dollars )
Bacholar4 years1400-2000
Masters2 years1500-3500
PhD4 years3000-4000

Makarantu

 • Faculty of Economics (located on Shahid Beheshti Street)
 • School of Persian Literature and Foreign Languages (kan babban titin Shahid Chamran , Pol Modiriyat)
 • School of Theology and Islamic Studies (kan babban titin Shahid Hemet Gharb, Dehkade Olympic)
 • School of Physical Education and Sports Sciences (a ƙarshen titin Hakim Gharb)
 • Faculty of Mathematical and Computer Sciences (a titin Shahid Beheshti., titin Vezara)
 • Faculty of Psychology and Educational Sciences (Yammacin itin Hemat, Meidane Dehkade Olympic)
 • School of Social Sciences (A junction ɗin Hemat da Shariati, titin Dawood Gol Nabi)
 • School of Management (a ƙarshen titin Hemet na yamma, Meidane Dehkade Olympic)
 • School of Communication (a ƙarshen titin Hemat na yamma, Meidane Dehkade Olympic)
 • School of Law and Political Sciences (a ƙarshen titin Hemet ta yamma, Meidane Dehkade Olympic)
 • Autonomous Postgraduate Education Campus (a Dehkade Olympic, Meidane Dehkedeh)
 • Eco Insurance Institute of Higher Education (a titin Valiasr)

Karatu a Jami'ar Allameh Tabataba'i

Kwasa-Kwasai

 • Persian Language and Literature (daga matakin digiri har zuwa PhD)
 • Arabic Language Translator
 • Arabic Language and Literature (BSc, Masters, da PhD)
 • Istanbul Turkish Language
 • Spanish Language
 • English Language and Literature (BSc, Masters )
 • Chinese Language
 • Russian Language
 • French Language (translation)
 • English Language Translation
 • Business Economics
 • Agricultural Economics
 • Theoretical Economics
 • Industrial Economy
 • Philosophy (PhD)
 • Theology and Islamic Studies (Ph.D.)
 • Insurance Management (Eco)
 • Law
 • Political Science
 • Educational Sciences (preschool and primary school trends, educational management and planning, educational technology, mentally retarded children)
 • Social Planning and cooperation
 • Social Work
 • Communication Studies and Information Technology
 • Journalism
 • Public Relations
 • Statistics and Applications (Statistics)
 • Acoounting
 • Administration (Customs Administration)
 • Business Management
 • Insurance Management
 • Industrial Management
 • Tourism Management
 • Hotel Management
 • Government Management
 • German Language and Literature
 • Spanish Language and Literature
 • General Linguistics (Masters da Ph.D.)
 • Ancient Languages of Iran (subset of Persian language and literature, master’s degree)
 • French Language Translator (master’s degree)
 • Economics (trends in energy economics, economics and e-commerce, economic sciences, economic development and planning (duka a matakin masters))
 • Economics (Ph.D. major in financial economics)
 • Islamic Theology and Education (Master’s Degree)
 • Philosophy of Art (Masters da Ph.D.)
 • Philosophy (Master’s logic major)
 • Philosophy of Religion (Master’s Degree)
 • Comparative Philosophy (Ph.D.)
 • Computing Sciences and Insurance Planning (Master’s Degree)
 • Sports Pathology and Corrective Movements (Master’s degree)
 • Physical Education and Sports Sciences (Master’s Degree)
 • Motor Behavior (learning tendency and motor control (Master’s Degree))
 • Sports Psychology (Master’s Degree)
 • Sports Management (Strategic management in sports organizations. Master’s Degree)
 • Criminal Law and Criminology (Master’s degree, Ph.D.)
 • Economic Law (Master’s degree)
 • International Trade Law (Master’s Degree)
 • Criminal Law of Children and Adolescents (Master’s Degree)
 • Communication Law (Master’s Degree)
 • Private Law (Master’s Degree, PhD)
 • Intellectual Property Rights (Master’s degree)
 • Human Rights (Master’s Degree)
 • Public Law (Master’s Degree, PhD)
 • Public International Law (Ph.D.)
 • International Relations (Master’s Degree, PhD)
 • Islamic Thought in Islam (Master’s Degree)
 • Political Science (Master’s Degree)
 • Educational Sciences (trends of preschool education and education, comparative education and education, elementary education and education (master’s degree))
 • Psychology (Ph.D.)
 • Clinical Psychology (Master’s Degree)
 • General Psychology (Master’s Degree)
 • Educational Psychology (Master’s Degree, PhD)
 • History and Philosophy of Education (Islamic Education (Master’s Degree))
 • Educational Management (Master’s Degree)
 • Counseling (rehabilitation counseling trends, family counseling, career counseling, school counseling (Master’s degree, PhD))
 • Urban Planning (Master’s Degree)
 • Social Welfare Planning (Master’s Degree)
 • Social Sciences (Trends of Sociology, Demography (Master’s Degree))
 • Social Work (Master’s degree, PhD)
 • Statistics (Master’s degree – Ph.D.)
 • Mathematical Statistics
 • Computer Science
 • Mathematics (mathematics of finance (Master’s Degree))
 • Accounting (Master’s degree, PhD)
 • Management Accounting (Master’s Degree)
 • Auditing (Master’s Degree)
 • Financial Management (Master’s Degree)
 • Executive Management (Master’s Degree)
 • Business Management (marketing trends, international business, entrepreneurship (master’s degree, PhD))
 • Urban Affairs Management (Master’s Degree)
 • Media Management (Master’s Degree)
 • Industrial Management (Production Orientation (Master’s Course))
 • Information Technology Management (Master’s Degree, PhD)
 • Training and Improvement of Human Resources (Master’s degree)
 • Educational Technology (Ph.D.)
 • Industrial Management (research trends in operations, production and operations, finance (master’s degree))
 • Persian Language and Literature (mystical literature trend, PhD)

Ababen More Rayuwa

 • Babbar ƙungiyar koyarwa
 • Cibiyar haɓaka binciken kimiyya
 • Cibiyar Wallafa (ɗakin editing da kula da al’amuran da suka shafi fasaha, ɗakin hoto, assembly, binding, printing )
 • Cibiyar ayyukan computer (ɗauke da na’urori da manhajoji na zamani)
 • Dandalin al’adu na ɗalibai
 • Wallafe-Wallafen ɗalibai (Samar da ƙungiyoyin ɗalibai da samar musu da yiwuwar wallafa abubuwansu)

Karatu a Jami'ar Allameh Tabataba'i

Hostel

Jami’ar Allameh Tabataba’i wadda ke cikin garin Tehran ta yi tanadin masauki mai ɗauke da kayayyaki domin baƙin ɗalibanta maza da mata, da ma ɗalibanta masu iyali. An rarraba wuraren kwanan ne bisa la’akari da kwas da sashen karatun ɗalibai, haka kuma dukansu suna ɗauke da abubuwan more rayuwa. Jerin sunayen hostel ɗin maza da na mata na jami’ar Allameh Tabataba’i:

 • Hostel ɗin maza na Shahid Hemat (titin Jalal Ali Ahmad)
 • Rukunin hostel na Shahid Salamat (na mata, titin Sa’adat Abad)
 • Hostel ɗin ɗalibai mata na Hazrat Valiasr (titin Hazrat Valiasr)
 • Hostel ɗin maza na Shahid Ashtiyani (titin Khaled Islamboli)
 • Hostel ɗin ɗalibai maza na Shahid Moeniyan (titin Shahid Beheshti)
 • Hostel ɗin mata na Shahid Azodi (titin Karimkhan Zand)
 • Hostel ɗin mata na Shahid Rahimi (titin Keshavarzi)

Laburaren Jami’ar Allameh Tabataba’i

Shafin yanargizo na babban laburaren jami’ar Allameh Tabataba’i yana ba ma ɗalibai damar yin rizab na littafan karatu da sauran littafai na kowane fanni. Ɗalibai za su iya amfani da shafin laburaren wurin karanta thesis na kwasa-kwasai daban-daban na matakin masters ko PhD.

Yanayin Wuri

Jami’ar Allameh Tabataba’i na cikin garin Tehran a babbar hanyar Shahid Kharazi, Mahdavi kani. Jami’ar na kusa da muhimman wurare kamar gidan tarihin jami’ar, wurin wasan yara, cibiyar saye da sayarwa ta Golestan, makarantar maza ta Omid Islam, makarantar Law and Political Science, Philly Cafe, Emdad Khodro duk a cikin garin Tehran. Haka kuma za a iya cewa wannan jami’ar ɗaya ce daga cikin jami’o’i masu kyau na wannan yankin bisa la’akari da ra’ayoyin mutane a manhajar Neshan.

Adireshi:

 • Lardin Tehran, Tehran, babbar hanyar Shahid Kharazi, Mahdavi Kani

Shafin: https://atu.ac.ir

Related Posts
Leave a Reply