Jami’ar fasaha ta Shiraz jami’a ce ta gwamnati a lardin Fars (lardi na huɗu mai yawan jama’a a Iran ), a garin Shiraz. Abubuwan da ke cikin wannan rubutu za su taimaka muku wajen yanke shawara mai kyau game da karatu a Shiraz University of Technology.
Gabatarwa
Ita ce jami’ar gwamnati ta biyu a gabacin garin na Shiraz wadda tarihinta yana komawa zuwa ga zamanin daular Pahlavi. Hakazalika a lokacin assasata ta fara aiki ne a matsayin kwalejin Electronics Industry har zuwa shekarar 2003 , sannan aka canja sunanta zuwa Shiraz University of Technology. Sabuwar harabar wannan jami’a na cikin sabon gari na arewa maso yammacin Shiraz.
Yanzu haka wannan jami’a na da ɗalibai 1810, malamai 120. An wallafa maƙalar ilimi 2337 a wannan jami’a, an kuma gudanar da taruka 3 a cikinta. Har ila yau, membobin tsangayar ilimi 98 sun fito ne daga wannan jami’ar. Jami’ar fasaha ta Shiraz ta ƙunshi wuraren bincike guda 2 tare da cibiyar nazari 1.
Ɗakunan gwaje-gwaje (laboratories) na wannan jami’a sun kasu kashi biyu, na koyarwa da kuma na ayyukan bincike. Daga cikin ɗakunan gwaje-gwaje na wannan jami’a akwai electronic laboratory, logic circuits laboratory, computer architecture laboratory, da sauransu.
Haɗin gwiwa tsakanin Shiraz University of Technology da research laboratory na GRAMFC na jami’ar Picardy Jules Verne (université de Picardie Jules Verne) ta ƙasar Faransa, ya soma ne a shekarar 2018.
Martabar Shiraz University of Technology a tsarin Shanghai
Bisa dogaro da tsarin ranking na Shanghai a fannin Electrical Engineering, Shiraz University of Technology ta samu matsayi na 401-500 tare da jami’o’in; Shiraz University, Tarbiat Modares University, University of Kashan, Isfahan University of Technology, Iran University of Science and Technology, da Ferdowsi University a tsakanin jami’o’in duniya, ta kuma samu matsayi na 6 a tsakanin jami’o’in Iran. Ta kuma samu matsayi na 501 – 600 a tsarin ranking na TIMES.
Makarantu
_ Faculty of Electrical and Electronics Engineering
_ Faculty of Mechanical and Aerospace Engineering
_ Faculty of Computer Engineering and Information Technology
_ Faculty of Chemical, Oil and Gas Engineering
_Engineering and Material Science
_Faculty of Mathematics
_Faculty of Physics
_Faculty of Chemistry
_ Faculty of Industrial Engineering
_ Civil and Environmental Engineering
Kuɗin karatu a Shiraz University of Technology
Kwasa-Kwasai
_ Electrical Engineering
_ Mechanical Engineering
_Applied Mathematics
_Physics
_Chemistry
_ Civil Engineering
_Materials Engineering
_Aerospace Engineering
_Electrical Engineering and Telecommunications
_Electrical and Power Engineering
_Electrical and Electronic Engineering
_ Chemical Engineering
_ Pure Mathematics
_Da sauransu…
Domin samun cikakken list na kwasa-kwasan wannan jami’ar, ku sauke wannan fayil na ƙasa.
Kwasa-Kwasan Shiraz University of Technology
Abubuwan Alfahari
_ Shiraz University of Technology ta samu shiga tsarin ranking na Times shekara huɗu a jere (daga 2019 zuwa 2022) inda ta samu matsayi na (tsakanin 601 zuwa 800)
_ Samun thesis mafi kyawu na Masters a fannin Mechanics wanda ƙungiyar Mechanics Association of Iran ta tabbatar a shekarar 2016
_ Thesis mafi kyawu na PhD a fannin Mechanics wanda shi ma ƙungiyar Mechanics Association of Iran ce ta basu
_ Cibiyar bincike mafi inganci ta ƙasa a shekarar 2015
_ Kambun bincike na IEEE a shekarar 2014
_ Lashe kyautar ‘Usern’ tsakanin matasan masana kimiyya da masu bincike na duniya wanda ɗaya daga cikin membobin tsangayar ilimi na jami’ar ya yi
_ Zaɓar fitaccen mai bincike na ƙasa a fannin Engineering daga cikin membobin tsangayar ilimi ta wannan jami’a, a shekarar 2015 da 2019
_Da sauransu…
Ababen More Rayuwa
Wurin kwana: Wannan jami’ar na da rukunin hostel guda biyu (na maza da na mata) waɗanda duka suna cikin harabar jami’ar.
Wurin kwanan maza (mai ɗaukar mutum 430): Yana da block 4 kamar haka; Modares, Razi, Ibn Sina, da Chamran. Abubuwan cikin wannan hostel sun haɗa da ɗakin karatu, ɗakin kallo, ɗakin computer, koren fili, wurin cin abinci, da kayan wasanni.
Wurin kwanan mata (mai ɗaukar mutum 190): Yana da block biyu kamar haka; Yas da Nergis. Daga cikin abubuwan da ke cikin hostel ɗin ɗalibai mata akwai ɗakin karatu, wurin cin abinci, koren fili, filin wasan volleyball da basketball, ɗakin kallo, da kayan wasanni.
Laburare: Babban laburaren jami’ar fasaha ta Shiraz wanda aka kafa da hadafin tattarawa, tsarawa, da adana abubuwan karatu na na’ura da waɗanda aka wallafa, don a amfana a harkokin karatu da na bincike, haka kuma domin taimakawa masu bincike wurin samun bayanan da suke buƙata, ta hanyar aiki tare da sauran cibiyoyin bincike a sassa daban-daban. Laburaren na da kwafin litattafai 34000 a harshen farsi da latin, ɗauke da batutuwa dabn-daban na kimiyya, gama-gari, da sauransu waɗanda aka tsara ta hanyar amfani da tsarin Dewy Decimal.
Maziyarta za su iya amfani da kayan aikin da aka tanada, haka kuma daga nesa za su iya amfani da tsarin portal na laburaren domin yi rizab, tsawaita wa’adin lamuni, neman littafi, sauke littafin na’ura, tambayar mawallafa, da sauransu. (Zaurukan karatu za su iya ɗauke kimanin maziyarta mata mutum 70, da kuma maza mutum 100 a ɗakuna biyu daban-daban. Ana buɗe ɗakunan karatu a koyaushe (dare da rana) a cikin kwanakin jarabawa.)
Yanayin Wuri
Jami’ar tana unguwar Shahrak Parvaz ta garin Shiraz, a titin Modarres. Idan aka duba yanayin muhalli kuma jami’ar na kusa da zauren motsa jiki na jami’ar, laburaren jami’ar, zauren cin abinci na jami’ar, masallacin jami’ar, da kuma wurin ajiye ababen hawan ma’aikata da malamai na jami’ar.
Adireshin Shiraz University of Technology
Adireshi: Lardin Fars, Shiraz, titin Modarres, Shiraz University of Technology
Adireshin ofishinsu na Tehran: Titin Inƙilab, Yankin arewa na tashar metro ta Darvaze Dolat, layin Karimi, block 10
Tambayoyin da ake yi
- Wasu irin takardu a ke buƙata domin yin rijista a Shiraz University of Technology?
Passport, hoto, transcript, certificate, resume, motivation letter, recommendation letter.
[neshan-map id=”26″]